Sashe 30
Kawar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
damuwar nan da kuma tunanin nan take ganinsa ciki, tun dawowarsa daga Katsina, ta kuma fahimci (family issue) dinsu ne, shiyasa bata tsananta masa da tambayar abinda ke damunsa ba, kuma bata saka baki ba, tunda shima bai sakata a cikin sha’anin ba. Ko a daren ranar ma tana ji yana waya da Yaya Zubaina akan wata bukata da Mama ta saka shi da bazai iya ba, taji Zubaina tana kara tabbatar masa sun riga sun gama shawara shi zai ja ragamar dukiyar Baba, bata son wata magana daga gareshi bayan wannan, kada ya zama raggo mana? Zubaina ta kare da cewa “Ita ba haka tasan Zayyan dinta ba, rashin Baba duk ya salube jarumtakarsa”. To sati biyu bayan nan, da ya dan samu nutsuwa don Mama da ‘ya’yanta duka sun dage akan bakansu, ya gayawa Safiyyah zai je Lagos gun aminin Baba, kuma zai kwana uku don bazai yiwu ya dawo a washegarin ranar ba tafiyar motar haya ce. Tunaninsa a lokacin shine yaje wurin Babansu Alh. Murtala, ya kai karar Mama dasu Zubaidah, kan suna son dora masa nauyin da bai shirya dauka ba, ya kuma nemi shawararsa kan batun. Kasancewar ya san Baba Murtala a matsayin mutum mai amana da rikonta, mai son cigaban Baba Bello da zuriyarsa da zuciya daya ko ba’a fada ba, duk shawarar daya bashi zata zama mai amfani ce a gare shi fiye da tasu Zubaina. Safiyyah ta kwana yi masa shirin tafiya Lagos, a washegari sukayi sallama ya tafi kamar bazasu rabu ba, soyayyar Safiyyah da Zayyan kullum kamar a ranar suka fara ta, basa taba gundura da juna da nuna ma juna so da kulawa, sai ka zauna kusa dasu zaka gane tamkar ‘tube’ da ‘tyre’ suke rayuwa. Koda Zayyan ya isa Lagos cikin motar haya ta luxurious, unguwar Ikoyi ya nufa wato inda gidan Baba Murtala Masari yake, kyakkyawar tarba Baba Murtala yasa aka shirya masa da masaukin da zai sauka tun kafin isowarsa. Sauka irin ta Dan da ka haifa a cikinka, ka kuma dade baka ganshi ba, ita Baba Murtala ya shirya masa. Aka kaishi dakin baki ya ci abinci ya kintsa, tare da Baban suka yi sallahr maghriba da isha’i a jam’I, sannan suka zauna a falon Baba Murtala don tattaunawa, ya fara gaya masa abinda ke tafe dashi, wato rigimar Mama data ‘yan uwanshi, na sai ya kwafe musu Baba, ya koma sana’ar da Baba ya bari da dukiyarsu. Ya gayawa Baba Murtala shi bai taba sha’awar wata sana’a bayan koyarwar da yake yi ba. Kuma bashida ra’ayin tara dukiya a rayuwarsa, don a ra’ayinsa ma nashi kason da aka bashi ya yanke shawarar Mama zai hadawa ta hada da tumunin takabarta ta kara jarin kasuwancinta. Yace. “A komai yana so ya gaji Babansa, amma banda a harkar irin neman kudinsa na rashin hutu da tara dukiya, baya kuma son yayi disappointing Mama da ‘yan uwansa in bai zame musu abinda suke hange a juya dukiyarsu ba”. Baba Murtala sai yayi murmushi, ya sake murmusawa, don ya lura rashin mahaifinsa ya karya lagon jarumtar Zayyan da yawa, ta wani fannin kamar mara sauran ‘hope’, a rayuwa, wato ya maida kansa (hopless) wanda bazai iya tabuka komai ba, tunda ya rasa source of inspiration dinsa Baba Bello. Daga ranar Alhaji Murtala ya sha alwashin zamewa dan amininsa Zayyan UBA mahaifi. Uban da zai karfafa shi a rayuwa har zuwa nasa karewar numfashin, sannan ya zame masa ubangida na kasuwanci. Ba abinda yake bukata a lokacin irin soyayyar Uba da ya rasa, wanda ita kadai zata karfafeshi a yanzu, ta dawo da jaruntakarsa. Don haka Arch. Murtala Babangida Masari, ya dafa kafadarsa ya ce dashi cikin yin kasa da murya. “Faduwar wani tashin wani ce my son Zayyan, kada ka taba bari faduwar wani naka ta zama faduwarka. Dama wannan ranar nake jira, wato rana irin wannan da zaka tako ka zo gabana da kanka ba tareda Fatuma ta turoka ba, ka nemi zama cikakken ‘Architect’ makwafin mahaifinka a gabana. Hajiya Fatu dasu Zubaina sunyi abinda ya dace. Ka sani Bello ba raggo bane, na kuma tabbata bai haifi raggo ba”. Yayi murmushi ya cigaba “hakannan Bello bai abota da ragwaye a sanina dashi tun muna makaranta, in yaga baka da kokarima baya kusantarka, kada rashinsa ya maida kai ragon maza kaji ko Zayyan, ka mike ka zama mai zafin nema irin Babanka, duniya bata aure da ragwaye yanzu, shi namiji rayuwarsa duka ‘yar gwagwarmayar nema ce, in dai da dama kuma da nasibi. Balle kai gashi kana da damar, a gefe kana da ni, Babanka Murtala. Allah kuma yace tashi in taimakeka, sai ka shiga da kwarin guiwarka ka gani idan akwai nasibi a ciki ko babu. Dama jira nake komai ya lafa ka kuma kara samun nutsuwa, sannan in nemoka ko baka zo ba. Duk da dai inada kyakkyawan fata, na cewa zaka zo din watarana. In ce da kai, ka zo mu cigaba daga inda muka tsaya ni da mahaifinka. Ka mayemin gurbin abokina Arch. Bello. Nima cikin kewar rashinsa nake cigaba da nawa harkokin. Mahaifi ko kwasar kashi yake a matsayin sana’a yana so Dansa ya gaji wannan sana’ar, in dai ta halal ce. Da na Zayyan, ka zo a dama da kai a harkar “Real Estate”, ka kutsa cikin profession dinka da kyau ka yishi practically, ka zama Professional Architect dinda duniya zata san da zamansa, kamar mahaifinka. Wato ka zama cikakken magaji ga Bello Rafindadi, akan komai nasa. Ina kara jaddada maka, “mutum ko kwasar kashi ce sana’arsa, zai so ace dan sa ya gajeshi a kanta”. Ita wannan harkar ta gine-ginen gidaje da zana su da bada hayarsu, wadda ta zame mana silar alkhairi nida mahaifinka, ba kamar aikin koyarwar daka saba da shi bace, harka ce da babu hutu a cikinta kuma wadda ke bukatar tsayuwar daka da cinye lokaci, dole sai ka zage damtse ka kuma jajirce sannan zaka ci ribarta. Amma harkace ta ilmin zamani dake kawo alkhairi sosai ga mamallakanta. In da ka san irin wahalhalun da muka sha ni da Bello, da fadi tashin da muka sha akan harkokin nan kafin mu kawo wannan matakin, zaka fi yarda kada abar sana’ar ta bi ruwa a cinye jarinta a wasu abubuwan daban, tunda Allah yasa akwai namiji a cikinku”. A nan Baba Murtala ya shiga baiwa Zayyan tarihin struggle din Babanshi Bello Rafindadi, wajen gina abinda ya tara da guminsa, yace bai dace ya yarfe wannan gumin ya zubar ba, tun yana malamin jami’a a mataki na farko Bello yake koyarda Zanen gidaje mai ban mamaki ga dalibansa, ya kara da bawa Zayyan nagartattun shawarwari akan yadda ake cimma nasarar harkar REAL ESTATE, ya kuma ce ya zo su tsunduma cikin harkar tare, zai kama hannunsa zai masa jagora. Har zuwa sanda zai gama gane kan harkar “Real Estate Business” bakidayanta sannan ne zai saki hannunsa, ya barshi ya cigaba da tsayawa akan kafarsa. **** **** **** A takaice wannan shine mafari, sila, kuma tushen kafuwarsa, da silar arzikin da yau yayi cikin dan lokaci da fitar sunansa a harkar Real Estate. Arch. Zayyan Bello, ya shiga harkar da kafar dama kamar, koma fiye da mahaifinsa Arch. Bello Rafindadi. Duk wata hikima da baiwa ta mahaifinsa sai ta yi hijira ta dawo cikin kansa kamar yadda dukiyarsa ta dawo hannunsa. Don kuwa a gaba kadan, bayan kamar shekaru biyu da farawarsa, Arch. Zayyan yayi resigning daga aikin koyarwarsa da jami’ar Ahmadu Bello. A lokacin tuni Safiyyah tayi graduating (ta kammala digirinta na farko) itama a fannin nasu na Architecture, har tayi hidimar kasa duka a Zarian. Safiyyah na gama makaranta Zayyan ya bar Zazzau ya koma Abuja, inda acan ne Baba Murtala yake kokarin kafa Zayyan akan harkar zanen Estate da karbar kwangilar gina su da bada hayar su. Kuma acan ne duka harkokinsu suka fi karfi yanzu. Duk da Baba Murtala iyalinsa suna Lagos yana yawan zaman Abuja yin harkokin kwangilar gine-ginensa. Saida ya dan fara kwari a harkar ya soma tunanin dawo da Safiyyah kusa dashi don su bar Zaria gabadaya. Da farko Zayyan ya fara da kama musu shida Safiyyah dan madaidaicin gida flat a wani (block of flats) mai daki uku da falo a Jabi. Estate din da Zayyan ya fara zanawa ya kuma gina na farko mallakinsu ne shida ‘yan uwansa mata, wato hadakar dukiyarsu ce su duka, a jihar Katsina suka samar dashi, a can ya fara gina Estate, don akace kowa ya bar gida gida ya barshi, wanda suka sakawa suna; “BELLO RAFINDADI ESTATE”. Sai suka zuba ‘yan haya duk shekara Mama da ‘yanuwanshi na damkar makudan kudade, shi da Safiyyah ne suka zauna sukayi ta musu, (debate), akan sunan da ya dace a sakawa Estate dinsu na farko, har a karshe suka ambaceta da ‘surname’ dinsu gabadayansu, watau “Bello Rafindadi Estate”. Anan GRA Katsina. Zayyan ya muskuta daga kwancen da yake, yana cigaba da dogon tunanin da yake yi…. wani lokacin har yana matse kwallah, wani lokacin kuma yayi murmushi duk shi kadai. Safiyyah have immensely contributed a lot to his achievements and successes (Safiyyah tayi matukar bada gudunmuwa ga nasarorinsa da abubuwan da ya cimma na nasara a rayuwarsa). Domin a duka wadannan lokutan Safiyyah na tare dashi cikin halin dadi dana babu dadi, against all odds ta tsaya a gefensa, kuma tana kula da rayuwarsa da cikinsa da lafiyarsa da bukatunsa na Da namiji cikin kauna da soyayyah. Ta taya shi raba dare suna ‘sharing idea’ da musayar fasaha, inda zaka gansu sun zauna a falonsu sun baje takardun Zane a gabansu cikin dare, kamar abokan aiki ba mata da miji ba, suna tsara Zanen Estate tare, tareda da shirya time-table na yadda zasu gudanar da kwangilolin ginin gidajen da suka samu su aiwatar dasu bi da bi cikin tsari da sarrafa hikima. **** **** **** Bazai manta ba, shi da ita ne suka raba dare a wani dogon dare mai dumbin tarihi tarihi suka samar da ‘idea’ din kirkirar “SUNSET ESTATE”. Wanda zai zama mallakinsa ne shikadai watau ba tareda dukiyar ‘yan uwansa a ciki ko mahaifiyarsu ba. Cewa suka yi bari su hada duk wata fasaha da suke da ita ta ilmin Architecture a kan Estate din, da duk abinda Zayyan mallaka ya sayar