← Book details Kawar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 31

Sashe 14

Kawar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

na zo da kaina. Saboda Zayyan na musamman ne a wuri na saboda biyayyar da yake yi mun, kuma shikenan mini Da namiji”. Malam yaji dadi kwarai da gaske, ya kuma yaba da saukin kan Baba, don ko da ganinsa ka san ba karamin mutum bane. Hira suka barke da ita daga bisani, da hira tayi hira tsakaninsu har tarihin iyaye ya shigo ciki, nan Malam ya gane ainahin iyayen Arch. Bello ya sansu, don sunyi makwabtaka da kakansa a Rafindadi tun farkon kafuwarta. Malam Usman da Arch. Bello basu rabu a ranar ba, sai da suka kulla kyakkyawar alaqa da abota a tsakaninsu. Kuma daga satin daya biyo baya ya fara zuwa zance gun Safiyyah Usman Dandume, da yardar iyayensu duka bangarorin, komai na soyayyarsu bisa tsarin da Malam ya kafa mai tsauri da wuyar bi Zayyan ke bi, yana kokarin kiyayewa, don akwai shi da biyayya ga na gaba da gudun zuciyar babba, bai taba karya dokar Malam ba, misali baya tsare Safiyyah da zance a makaranta kuma baya zuwa sai sati-satin da malam yayi izni kadai, har gidan Antinta a Zaria baya zuwa a renakun da aka masa iyaka da ita. Baba Bello kuma bai bata lokaci ba, watanni uku a tsakani da fara neman sa da Safiyyah bai ko yi shawara da Mama Fatu ba yasa aka kai kudin aure mai tsoka Dandume. Daga Zayyan har Safiyyah kallon komai suke kamar a mafarki ko kuwa almara sanda aka kai kudin aurensu, saboda basu taba zaton al’amarin zai zo musu da wuri kuma da sauki haka ba. Duka-duka haduwarsu da kankamar maganar auren ba’a fi watanni tara ba. Safiyyah da mai binta Sabah, Rayyah da autarsu Rayhah, dukkasu har ita Hafizan Alqur’ani ne, tun tana shekaru goma sha hudu tayi hadda da sauka. Kannenta wadanda kwanikar haihuwarsu Ammi Hafsatu tayi, shiyasa zaka dauka ko ‘yan uku ne, suka biyo bayanta akan wannan tsarin na gidansu. Ba’a kaiwa shekaru sha biyar a duniya yaran gidan basu yi sauka da haddar Alqur’ani ba. Gidansu Safiyyah gidane da aka yiwa tubalin tarbiyyar Islam, da riko da Alqur’ani da hadisin Manzo, babba da yaro kowa mahaddaci ne kuma masanin hadisi. Duk hujjar da ‘yammatan Ammi zasu baka cikin maganarsu zasu hada maka da Aya ko Hadisin da ya dace da ita. Malam Usman a kasar Mali yayi karatun addinin musulunci mai matukar zurfi wanda al’ummar Dandume da wajenta suke amfana dashi a halin yanzu. Akwai manyan dalibansa da a yanzu ake damawa dasu a gwamnatin Katsina da kuma wadanda manyan ‘yan siyasa ne, don haka kullum baka raba gidansu Safiyyah da bakin motoci na manyan mutane masu zuwa ganin Mallam, ko neman taimako akan wani al’amari da ya shafi addini ko fatawar ilmi daga gareshi. Bayan masu zuwa daukar karatu, kullum kuma zaka tadda gidansu cikin kabakin alheri na kayayyakin abinci da sutturah da dabbobin yankawa ayi sadaqa daga almajiran Malam. Don haka gidansu Safiyya kullum cikin kyakkyawar cima yake. Mahaifiyarsu Haj. Hafsatu da suke kira “Ammi” haifaffiyar garin Dandume ce itama kuma auren zumunci ne irin na hadin iyaye da kakanni tsakaninta da Malam Usman. Ammi da Malam, tamkar Lailah da Majnun suke tun daga kuruciya har girma, Malam bai ko kara attempting na kara aure ba, don yakan ce “bai iya adalci akan Hafsatu”, ya rike ‘yar uwarsa kuma uwargidansa Hafsatu da kyau da amana, suka hada kai da junansu wajen tarbiyyarsu da rufa asirin ‘ya’yansu. Yau da hantsi Ammi da Malam na tattaunawa akan auren Safiyyah da ya gabato musu, Ammi tace. “Malam na fa saka fili na a kasuwa zan maka gudunmuwa, inaso in baka ka hada da abinda ya samu, don ayi kayan dakin Safiyyah, dama saboda auren nan nake ta ajiye da filinnan ban taba shi ba duk da tarin bukatoci na. To amma naga kai baka fara shirin komai ba har yanzu, gashi wata uku kamar yau ne zaka ga sun zo”. Malam ya dubi matarsa Ammi (Hafsatu) yace “ai ko da suka kawo kudin aure na karba, in kin lura ban zura jiki gabadaya ga al’amarin ba, saboda inaso na yi addu’a ta akalla sati biyu tsakaninsa da wanda zuciyata ta kwadaitamin a kanta kafin zuwansa, sannan in yi wasu sati biyun ina istikharar neman zabin Allah, kafin ma na saka musu lokacin daurin aure. Ni bana yin abu da ka, ban gayawa Allah yayimin zabinsa ba, itama Safiyyah kirawomin ita, in bata addu’ar da zata yi, da tata istikharar, duk mu dukufa gayawa Allah nida ita, kafin musa kai a cikin al’amarin gaba-gadi. Ko don yawan maneman Safiyyah dake zuwa wajena da bana ko amsa musu, sai shi wannan Zayyan din kadai da hankalinsa da karamcin mahaifinsa ya ribaci zuciyata ya farauto soyayyata gareshi. To kinga akwai bukatar a tsaya a yi addu’a ta musamman a kai, yadda ya kamata, akan Allah yayi zabin alkhairi ba son zuciyarmu ba”. Ammi tace “gaskiyar ka Malam! Don nidai ban san meyasa ba, har yanzu ko kadan maganar auren Safiyyah da Zayyan dinnan taki kwantamin dari bisa dari a rai, sai nake ganin kamar gidan da ya fito yafi karfin shigar Safiyyah. Koko ince bai yi daidai da tsarin gidajen da ya kamata mu kai ‘ya’yanmu aure ba. Bana son shigar da ‘ya’yana gidan da aka ginu akan rayuwar duniya da akidar boko zallah. Magana ta domin Allah Malam, ban taba kawowa ba Haroun zaka baiwa auren Safiyyah ba (babban hadiminsa kuma babban almajirinsa)”. Malam yayi murmushin manya yace “ko? Ni kuma wallahi na dauka zaki ce ne “Sheikh” Yana nufin Yayanta Ridhwan (Yaya Sheikh) wanda Malam ya kai karatun degree akan Shari’ar musulunci a kasar Misra shekaru biyar da suka wuce, wanda tare suka taso da Safiyyah a gaban Malam da Ammi din. Sai da Ridhwan ya samu tafiya Al-azhar ne ya bar gaban Malam da Ammi. Kuma ko bayan kammalawarsa bai dawo ba ya samu aiki a Doha (Qatar) yayi zamansa. “Yaya Sheikh”. Sunan da Safiyyah ke kiran Yayanta Ridhwan dashi kenan, saboda rikon addininsa da malantarsa kamar Malam ne ya haife shi ba Yayansa marigayi Malam Abubakar Dandume ba. Kafin ya tafi Misra shima yana bada karatu a madadin Malam, musamman idan malam baya gari ko yanada uzuri. Yaya Shaikh dan gaban goshin Malam ne. Ammi tace “ai ni nasan ba soyayya tsakaninta da Ridhwan, amma Malam?! Haroun, shi yafi dacewa ka baiwa auren Safiyyah. Duba da irin yawan hidimar da yake maka da zurfin ilmin addinin sa, sannan tun tana karama yake nuna alamun yana sonta. Mutanen nan na Rafindadi daga zuwansu ban ga ka tsananta bincike a kan gidansu ba, ka aminta ka kuma basu damar kawo kudin aure, kamar wadanda suka ja maka ‘Yaasin’ kafin su iso maka". Dariya Ammi ta baiwa Malam sosai, saida yayi murmushi yace "Amma Hafsatu kinsan Prof. Bello Rafindadi kuwa? To ai shi din baya bukatar dogon bincike saboda sanannen mutum ne a Rafindadi, sannan tsohon shugaban jami’ar Katsina ne, kowa ya san shi, ya kuma shaideshi, duk wani bincike da nayi akansu kyakkyawar shaida ce take fitowa, ta cewa; “Prof. Bello ya isa da gidansa!". Ammi tace "amma dai Malam ka sake tunani da kyau akai, ni a ganina Haroun zaifi rike mana Safiyyah da mutunci da martaba”. Malam ya gyara zama ya fuskanci Ammi sosai, halinta ba bako bane a gareshi bata ko son harka da wanda ya fita kumbar susa a duniya, ta tsaya iya matsayin da Allah ya bata na matar aure a kauye, ita bata wuce gona da iri. To amma shi kansa bai san meyasa ya zabi Zayyan akan Haroun ba, Haroun din da ya sani fiyeda kowanne yaro tun Safiyyah na yarinya sonta yake yi, ita kuma jininta yafi haduwa dana dan uwanta “Yaya Sheikh”, bata ma san me Haroun yake yi ba. Lokacin da Yaya Shaykh ya tafi karatu Misra Safiyyah da yake kira “Safifi” ta sha kuka, kodayake Haroun da bakinsa bai taba zuwa yace masa yana kamun auren Safiyyah ba sai hidima da yake da ita tun tana yarinya kan jiki kan karfi kan aljihunsa. Komai ya samo sai ya kawowa Ammi yace a baiwa Safiyyah. Shikuma Malam, zuciyarsa tafi karkata ga sha’awar watarana Yaya Sheikh ya dawo gida ya auri kanwarsa Safiyyah. Wannan kafin bullowar Zayyan ne. Yace “Hafsatu ki cigaba da yimin shaidar da kinka riga kinka yimin kin ji? Bazan taba yima ‘ya’yana aure don abun duniya ko wani mukami na mutane ba, amma kuma bazan baiwa Safiyya Haroun ba, sabida abinda baki sani ba har gobe bansan asalinsa ba, na bude ido kawai na ganshi cikin almajirai na ne yana gararramba ba iyaye ne suka kawo min shi ba, haka na kama shi na rike gam, saboda naga alamun nagarta da rashin koshin lafiya a tare dashi tun a lokacin. Bama wannan ne muhimmin abinda zai hanani bashi aurenta ba a’ah, halinsa yayi sanyi kwarai, da wuya ya iya tanqwara Safiyyah idan ta butsare wallahi sai jajirtaccen namiji kin san ta dai ba bakuwarki bace, raggon namiji bai iyawa da halin Safiyyah idan tana son abu. To Haroun kam in baki a bude, bayan rashin sanin iyayensa da ban yi ba har gobe, wanda ba shine kadai ya hanani bashi aurenta ba, idan ya auri Safiyya ita zata koma mijin shi ya koma mijin tace, saboda kullum dani zai dinga kallonta, wato ya kalli kanshi a matsayin hadiminta/almajirinta, duk girman da yake bani ita zai koma baiwa. Ina kuwa rayuwar aure zata yiwu da haka?”. Haka malam yayi ta kawowa Ammi hujjojinsa, da misalai na dalilinsa na zabar Zayyan akan Haroun, ya gaya mata ya yaba da hankalin Zayyan, yaga alamun jarunta da mazantakar kwarai a tare dashi. Sannan kuma ya kuma yaba da dattakon mahaifinsa, domin mutum ne na kwarai da kowa ya shaida a jihar Katsina bakidaya, sannan akan ilmi aka sanshi ba wai akan tarin dukiya ba. Ya kuma ce “duk da haka Hafsatu kin sanni sarai, bazan shigar da Safiyyah gidan Rafindadi da ka ba, sai na russuna akan goshina na lankwasa gwuiwoyina a gaban Ubangijin daya halicceni, wato sai na gayawa Allah cikin talatainin dare akan ya zaba min abin duk da fi alkhairi a gareta, kome Allah ya zaba mana dashi zan yi amfani, itama sai in ranta ya kwanta da auren Zayyan din
Chapter 14 · 0% Book details