← Book details Kawar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 31

Sashe 31

Kawar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

ya saka a cikin capital dinsa ta ginin da zasu yi, su yi Estate din amma wannan karon a matsayin nasa shikadai. Saboda shekaru uku bayan kama harkar ‘real estate’ da yayi dukiyarsu Zubaida ta rubanya a hannunsa, kusan kashi hudun yadda ya karbeta daga hannunsu, kowaccensu ta mallaki Estate nata na kanta yanzu a Katsina, haka shima yanada Estate sun kai hudu a Katsina, hakika Allah ya sanya masa hannu da nasibi a harkar ‘real estate’, da kuma taimakon Baban kwarai Baban marayu, Alhaji Murtala Babangida Masari. Bayan ya tsayar da idea din yin nasa Estate din na kansa, bisa shawara da gudummuwar Safiyyah, sai yaje ya samu Mama Fatu akan yana son gina Estate nasa na kashin kansa a Abuja. Mama Fatu bata hanashi ba, ta dai ce in dai zai cigaba da rikewa ‘yanuwansa mata nasu Estates din, ita bazata hana shi yin yadda yake so ba. In kuma Safiyyah ce ta zugo shi akan ya ware dukiyarsa daga Katsina ya mayar Abuja don tana bakin cikin yana kulawa ‘yan uwansa da Estates dinsu a Katsina, tana so ta janyeshi gabadaya ya maida hakalinsa a Abuja, to tayi a banza, tunda dukiyarsa dai zata taba zama tata ba, tunda gata nan har yau sai cika masai da kashi ta iya, ko gudan jini bata taba ajiye masa a kasa da sunan dansa ba. Maganar ta dade tana masa yawo a kai, amma bai ce komai ba. har yaushe akayi auren da za’a soma cewa Sophie bata haihu ba? Bisa shaidun da suka kamata wato Lauyan Baba Barr. Abba Gana Shettima da Baba Murtala da Mama, Zayyan ya zame komai nasa daga cikin na ‘yan uwansa su Zubaidah, amma zai cigaba da kula musu da komai nasu. Mafari kenan na fara samuwar assasa tubalin ginin SUNSET ESTATE a unguwar Guzape. Bisa zane da tsari irinna zamani, wanda yayi amanna bai taba yiwa kowa irinsa ba. Kuma anyi ittifaqin bai dauko samfurinsa daga ko’ina ba. A’ah, zallar idea dinsu ce shi da Safiyyah. Domin sun kure duk wata fasaharsu ta Zane a kansa shida Sophie. Shi da Safiyyah suka samar da SUNSET ESTATE. Bayan shekaru biyun da suka dauka suna raba dare akan zanensa, tareda tsara proposal din ginin, komai na shirye-shiryen ginin ya kammala a shekara ta shidda da aurensu, sai aka fara gina ‘Sunset Estate’. **** **** ****

Mu karasa a littafi na biyu.
Tare suke.
Sumayyah Abdulqadir
07030137870
(whtspp only).
PAID BOOK

Assalamu alaykum TAKORITES.
Kafin mu fara ina farin cikin tallata muku Hajiya Aisha Umar Dauda mai A&A Incense & Collections.
Dealers ne nadukkan kayan Oriflame Products & GHT Products. Sanan suna da Room Freshener, Toilet Cleaner, Tiles Cleaner, Glass Cleaner, Dish Wash, Hand Wash, Shoes & Bags, Hand Made Shoes, Atamfa, Shadda, Materials, Kid's Wears, Electronics, Perfumes and many more.
Domin sayen daya ko sari ana iya tuntubarsu a;
No.1 Beside Lolo Dakare's Filling Station Hajj Camp, Katsina State.
Suna aikawa ko'ina. Ko a tuntubesu kai tsaye a wannan lambar waya don saka order.

08067303736
08054647489
Chapter 31 · 0% Book details