Sashe 18
Kawar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wasu muharraman juna ko yaya? Da zaki ce ina miki rashin kunya, ko ba kya son lectures din da nake miki hakkina ne in miki”. Ko tace cikin jimami “Allah Sarki diyata Safifi, duk wannna hirar soyayyar da ake sha a waya (is different) fa da irin abinda nake gaya miki, duk da na fahimci kamar Zayyan din baya da rawar kai irin na angwayen zamani, amma zaki ce na gaya miki irin shi sun fi kowa fitina da an shiga gidajensu.”. Hakan kullum kara ruda Safiyyah yake yi duk duk tabi ta tsorace, ta kidima kanta da auren bakidaya, don Anti Dije ta sakata a kwana, ta jefata a tsoron masoyinta yanzu, ya zama last person data ke son jin sallamarsa gidansu. Da tunanin Zayyan zai canza daga yadda ta sanshi zuwa marar ta ido, da zarar ta saka kafarta a gidan shi kullum take kwana take tashi. Safiyyah dai irin ‘yammatannan ne kifin rijiya, ko kawaye bata dasu, watakila shiyasa ko kwalliya bata iya ba, gata dai a jami’a, amma bata deviating daga abinda ya kaita, kamar bata san wasu ‘yammata na existing a jami’ar ba. Kannenta su Sabah ne manyan kawayenta, sai ko Anti Dije da ta maye mata gurbin uwar daki kuma karamar Goggonta, 'yan ajinsu tsakaninta dasu gaisuwar mutunci ba wata hira makamanciyar wannan irin ta sa’o’In juna, ita Anti Dije a wurinta abin kirki take yi, bata san ta saka mata shakku da wani bahagon tunani na daban ba, a kan cewa Zayyan zai canza daga nunkufurcin sa na ustazi zuwa devilish duk ranar data tare. Sai ta cewa kanta ashe auren ana yinsa ne don wata manufa, tarewarta kuma na nufin a zubar mata da kunyarta ta diya mace, to bazata je ba. Har ila yau Anti Dije ta nuna mata kamar taci wani bashi ne nasa a kanta, da zata biya koda tsiya koda arziki da zarar ta tare din. Bawan Allah Zayyan yana can ABU yana fama da akalami bai san da aika-aikar da Anti Dije ta gama yi masa ba, bai san ta gama jika masa garinsa ba, ta hanyar yiwa amaryarsa famfon ilmi da wankin kai ba. Ya kammala project ya mika. Duk da haka bai koma Katsina ba yana Zarian yanata shirye-shiryensa na tarewar Sahibah Sophie, bai fasa ba, sayo wannan yau sayo wancan gobe yana kara kawata dan gidan nasu, duk don tanadin zuwan Safiyyah. Mama da kanta take tambayar Zayyan ya taji shiru, sai yaushe ne Safiyyar tasa “fi-sauran mata” zata tare ne??? Rasa mai zai gayawa Mama yayi, sabida ya biyewa son ran Safiyyah da yawa, shi kansa ya rasa inda Safiyya tasa gaba akan batun tarewarta. Yau tace ciwo, gobe tace jarrabawa. Kuma duk tayi su ta gama. Don haka a karshen wannan makon da yazo Dandume, aka yi masa masauki a inda suka saba zama wato dakin bakin Malam na soron gidansu Safiyyah. Safiyya ta fito ta sha Jilbab dinta kamar ba amarya ba, kai shi hijab dinnan fa ya fara daina burgeshi yanzu, ta tsugunna da murmushi a gabanshi tana zuba masa ruwan randar Ammi mai sanyi data debo a jug a tambulan mai garai-garai. Tace "wai fa daga Zaria kazo ko? Sannu kaji! Ka sha hanya". Ya dubeta da kasan idanu rabin jikinsa kwance cikin kujera one seater guda daya dake dakin, sonta da kaunarta kullum karuwa suke yi a ransa, musamman saboda yawan kunyarta dinnan da har gobe taki barinta, da kalamanta na hankali cikin in’ina, sannan da hankalinta irinna tarbiyyar tsoffi, daga Malam har Ammi sun manyanta sosai kuma tarbiyyar manya suke yiwa ‘ya’yansu, shiyasa kullum ya ganta gabansa tana masa magana cikin in’inarta da taushin murya sonta da kaunarta karuwa suke a ransa su ninka na baya. Komai Safiyyah tayi na manyancennan nata burgeshi take yi, amma yau jilbab da hijabs din sun fara gimsarshi. Fisabililllahi ace wai har bayan daurin aure matarsa ba zai ganta cikin kwalliya ba??? Yau sai ya hade giran sama dana kasa ya fito mata a Mr. Zayyan dinsa sak, namiji irin kowanne, yace cikin dakewa da shanye shakkarta, wanda kwarjininta ke sabbaba masa a kullum har yaji ba kowanne irin zance zai iya dosarta dashi ba. Amma yanzu fa? Ya hadiye miyau yana kallon pinky lips dinta da kullum suke bashi sha’awa. Yace. “Sophie, yau daya dai a ajiye Hijab dinnan a gabana mana, in ga “Hijabie” dita a zahiri babu Hijabin?” Ta yi maza ta kalle shi da mamaki, sai ya lumshe mata ido yace cikin kwantar da murya. “ina nufin don ki sha iska. Dubi fa yadda yake faman saka ki zufa har a goshi, to ina ga cikin jikinki? Duk da fankar nan dake faman filfilwa Safiyyah gumi kikeyi? Shi Hijabin na dauka na fita ne kawai amma banda a cikin gida a gaban miji?". Taji kunya da murmushi sun kamata a lokaci guda. Ranar farko kenan da ya taba cewa yanaso ya ganta babu hijabi, ya kuma hada da kiranta da suna ‘Sophie’ duk don ya tausasawa yardarta, sai taji sunan yayi mata dadi yau fiyeda sanda ya fara fade, saboda ba wanda ya taba kiranta da ‘Sophie’ din ta wannan sigar ta lallashi da Zayyan ya furta yau, very loving and so romantic daga zuciya har bakinsa, hakan yasa Safiyyah jin kanta yayi girma, irin na macen da miji ke lallashi kan tayi masa abu, taji kamar sunannan da Zayyan ya lanqaya mata yanzu, yafi na kowacce mace dadin furtawa (Sophie). Duk da haka Safiyyah sai ta turo baki gaba, sannan a shagwabe ta dubeshi cikin marairaicewa “ai ni sam ban saba cirewa ba, sai in a dakina nake kona Ammi. Saboda inna cire hijab ko a gaban mata 'yan uwana nake, sai in jini kamar tsirara”. Zayyan yace a ransa “tabdijam! Akwai aiki ja, a gabana ashe”, kafin ya samu abin cewa Safiyyah ta kara da cewa cikin irin zancen zucinnan da ya fito fili “kwatakwata ni in ba a cikin gidanmu bane, a dakina kona Ammi, bana iya cirewa. To balle kuma a gaban katon namiji kamarka". Abin ya bashi dariya sosai amma ya gintse ya shanyeta yayi fuska, ya dan zamo daga cikin kujerar da yake kwance, ya riko hannunta dake zuba ruwa a tambulan bata san sanda ta saki kofin ba ruwan ya bare, jikinta ya hau rawa, Zayyan bai damu da reaction dinta ba ya kura mata ido, so inviting... tuni Safiyyah ta hau barin jiki, bai damu ba ya ce a tausashe. “Sophie, nine katon namijin??? Ni ko???” Ya fada yana nuna kansa da dan alinsa. Idanunsa na neman nata. Ta ji wata irin kunya ta kamata, ta rufe ido da hannu dayan da bai kama ba tana cewa “to da menene? Ai kayi biyuna a girma da tsayi, you are a giant!". Zayyan ya murmusa cikin kallonta, Mama na yawan cewa shi kato ne amma yau na Safiyyah yasa ya ji mazantaka ta karu masa sosai, a hankali ya sakar mata hannu, a sanyaye yaja baya ya koma cikin kujerarsa sosai, ya soma kokawa da emotions. Sai kawai zancen zucinsa ya fito fili a lokacin. “Baza ki san ni katon bane sai ranar da kika bar gaban Mallam zuwa nawa gidan. Idan na tube a gabanki kika ga girman kwanjina da kaurin ‘muscles’ dina. Daga ranar wannan hijabin na Safiyyah da acan baya yake burgeni ya daina burgeni kenan, sai dai ‘lingerie’ da ‘yan ‘nude nighties’ kawai nake son gani a jikinki Sophie!". Ya kare zancensa da wani irin lumshe idanu kamar mai hasaso ranar kasancewar hakan. Safiyya ta zaro ido tana dubansa a tsorace, sannan ta bude baki, nan ya gane ta ji zancen zucinsa. Sai ya fashe da dariyar basarwa, ya yunkura ya tashi zaune sosai ya dubeta cikin ido yace. “Sophie kenan, to wai ke in tambayeki mana? Me kike nufi damu ne? Nufinki a haka zamu dauwama? Ai hakan ba mai yiyuwa bane a rayuwar zahiri tunda muma ‘yan adam ne. In kuma a haka kike nufin zamu cigaba da rayuwa har zuwa yanzu, rayuwa irinta wa da kanwa, sai ince you are totally mistaken. Maganar gaskiya kawaici na ya fara karewa akan mara tausayin amaryar nan tawa Safiyyah. Nima fa mutum ne, kuma in gaya miki mai cikar lafiya mai bukatar kulawar matarsa kamar kowanne namiji, amma ni sai zabga min kebura ake cikin ruwan sanyi. Kafin muyi aure ne nake saurayinki, wanda bashi da kowanne hakki a kanki, mai iyaka dake a cikin mu’amala, amma yanzu Zayyanu ne mijin Safiyyahtu, Baban yaranta masu zuwa nan gaba kadan in sha Allah, kinji ko Sophie, don haka ki saki jikinki dani haka, Allah ya halatta min in ganki babu Hijabin. In kuma taba duk inda nake so a jikinki don hutu jin dadi na. So yau daya dai, daure ki cire min shi in samu inga halittar matata Safiyyah babu Hijabi, ko in taso yanzunnan in cire miki shi da kaina”. Safiyyah ta sunkuyar da kai cikin jin nauyi da kunya da wani irin abu da ya soma yanyame ruhin jikinta, Zayyan yace “kinsan har suna nasaka miki kuwa a wajen Mama, I used to call you ‘Hijabie’, duk sanda na ce Hijabie Mama ta san ke nake nufi, because these hijabs are your main characters dana fara ankarewa dasu a tare dake, kuma shine babban abinda ya fara fizgata zuwa gareki bayan in’inar. Amma daga yau su koma na fita school don Allah". Kunya sosai ta kama Safiyyah, haka ya ci gaba da kasheta da zance yau mai narka zuciyar mace yasa tayi laushi, har mamaki take wai Zayyan ne, sai murmushi take tana rufe ido in ya fadi wani abun mai nauyi, da ya matsa da son ta cire hijabin sai ta hau buga kafa a kasa cikin tabara tana cewa cikin shagwaba da rigima. “ni dai bazan iya cirewa ba, ka barni da abina, bana so, kana bani kunya Zayyan…”. Zayyan wanda a lokacin duk ta kara rikita shi da wannan salon shagwabar da bai taba gani a tareda Safiyyah ba, har dasu shura kafa irin na rigimammun yara, ba shiri yace ya hakura, domin ta tabo wani irin feeling da bai taba ji ba a kasan ransa, ya daga mata hanauwansa sama cikin saddaqarwa da bada kai, yana dariya yana cewa “nayi