← Book details Kaifi Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 21

Sashe 9

Kaifi Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"to zo muje ciki..." binsa yayi zuwa ciki bayan sun gaisa da yaya faruk wanda yake kallon Aliyu cike da mamaki saboda a iya sanin sa Aliyu yana da masifar zafin kishi da kuma riƙo musamman akan Mimi shiyasa duk wanda yayi yunkurin zuwa wurinta da sunan yana son ta to fa masifa ce take tashi daga wurin Aliyu amma yau gashi abin mamaki Afeef ya aure ta baiyi musu wannan haukan ba, gaskiya bai taba kawowa zai ganshi haka ba ko cikin mafarki,

"Aliyu wai ni abinda yake bani mamaki sai naga kamar baka damu da auren mimi da Afeef ba, anya kuwa Haidar din da na sani ne mai zafin kishi......."

Dariya Aliyu yayi ya mikawa Faruk hannu yace,

"to ya zanyi faruk, Afeef ai kanina ne dole banida yadda na iya dashi, da dai wani ne bashi ba sai in tada bore....."

"gaskiya ka kyauta, kuma naji dadi da ka gane hakan har ka sassautawa zuciyarka ka cirewa kanka damuwa, life goes on..... Just move on....."

"yes I moved insha Allah faruk...." runfa suka nufa wacce ke dauke da kujeru a cikinta suka zauna suna cigaba da tattaunawa kamar yadda suka saba.

Anty Mimi tun bayan da ta shiga cikin bedroom dinta jiya bata sake fitowa ba Hajiya tayi mitar tayi mitar har ta gaji ta ja bakin ta tayi shuru,ko breakfast da lunch ma sai cikin dakin aka kai mata, lokacin da Afeef suka shiga part din hajiyan samu suka yi tana tambayar Hajjo daya daga cikin yan aikinta,

"ita wannan gimbiyar ko sarauniya zan kira ta dashi ne ban sani ba ta ci abincin da ake kai mata??"

"wallahi hajiya ban sani ba sai dai ko idan zuwa za ayi a duba...."

"rabu da ita tayi ta kare ƙalau...."

Bayan Hajjo ta fita Irfan ya kalli hajiya yace "wacece?"

"Amarya mana, ban sani ba ko amarcin ta fara tun jiya dai da ta shiga ciki bata sake fitowa ba..."

"kuma lafiya lau take?" Afeef ya bukata yana kallon hajiya,

"to ni ina zan sani ne, ni da ban ganta ba"

"ina zuwa..." ya fada kafin ya mike ya fita zuwa bedroom dinta dan jiki da jini sannan yau da gobe sai Allah, a bakin kofa ya tsaya yayi knocking tana zaune kan gadonta da laptop a gabanta tana wani research.........

Wai shin yaya zata kaya?? Drop your comments...... Next chapter loading...... ✍🏻

KAIFI ƊAYA... ✨

*When the world called her “useless”… he called her “mine.”*💘

_KAIFI ƊAYA_ is not just a love story. It’s the story of Mimi - a doctor whose name was dragged through scandal, whose body was broken by fate… 💔
And Afeef - the man who chose to stay when everyone told him to leave. 😥

They won the fight against the world.
But can they win the fight for each other, when silence is louder than lies, and love is tested by things neither of them chose? 🥺

*One blade. One choice. One love that refuses to break.*❤️
_Kaifi Daya_ - because true love doesn’t walk away when you can’t walk anymore..😥

It's available now 07044644433

Your heart will not be the same after the last page🥰✍🏻✍🏻

#Kaifi ɗaya
#lovetriangle
#EmotionalRomance
#DrMimiAndAfeef

*_Ummi Shatu_*👌🏻
[7/18, 8:56 AM] Oum Jasrah: https://www.arewapen.com/book?id=6a50f2f571e75baab6622006

_A story of scandal, sacrifice and a love that refused to break, a love that says am still here._

KAIFI ƊAYA.....

NA
UMMI A'ISHA

7

***Shuru kamar ba zata amsa ba saboda haushin kowa take ji, shi kuma bai fasa ƙwankwasa kofar ba, a hankali tamkar bata so ta tashi ta sauka daga kan gadon nata ta nufi bakin kofar tana tsaki cikin ranta,

"Wai hajjo me kike bukata ne...... Bana fada miki kar ku sake kawo min komai ba....." tana budewa taga Afeef tsaye hannayenshi cikin aljihun wandon shi, kallon juna suka yi tsawon mintunan da baza su wuce ɗaya zuwa biyu ba kafin ta dauke idonta ta kalli gefe,

"Anty Mimi fatan komai lafiya?"

"Lafiya lau......."

"Ok, dama na zo in duba ki ne ko ba ƙalau ba saboda naji Hajiya tace tun jiya bata ga kin fito ba...."

"lafiya....."

"shikenan tunda lafiya...... Amma kin ci abincin?"

"naci" ta fada a takaice kamar bata son cigaba da maganar "

" to shikenan, sai anjima" ba tare da ta amsa ba kawai yaga ta mayar da kofar ta rufe tayi komawarta ciki, shima juyawa yayi ya koma inda ya fito inda ya tarar da hajiya da Irfan suna cigaba da maganar anty Mimi dan yanzu kamar haushin kowa take ji, wuri ya samu ya zauna kusa da hajiya cikin ransa shima yana fatan lokaci yayi yayi ya zo ko ya huta da wannan tsaka mai wuyan da ya jefa kansa.

Har dare yana family house amma babu ko alamar motsin anty Mimi kai tamkar ma bata cikin gidan bayan kuma tana nan a cikin daki sai tufka take yi da warwara ita kaɗai, shi kam yana son ya koma gida amma yana tunanin halin da zai sake zuwa ya tarar da mommy dan yanzu babu fuska ko kadan daga gareta shiyasa yaji gaba daya baya son komawa gidan sai dai kuma idan har bai koma dinba nanma wata sabuwar matsalar ce dan haka ya lallaba ya nufi gida kuma tunda ya shiga part dinsa ya rufe bai sake fitowa ba har zuwa lokacin da yayi bacci. Washe gari bayan ya tashi a fusace ya hango mommy ta fito daga cikin part dinta ta wuce wurin motar ta sai faɗa take yi, yasan ita da daddy ne kuma ba zai wuce akan wannan maganar kwaya daya ba ta aurenshi da anty Mimi, sakin labulen da yake hannunshi yayi ya shiga cikin toilet, ji yake a ransa ma kawai gara ya shirya yayi tafiyar sa calabar dama a yanda ya tsara zuwa upper week zai koma amma yanzu tunda zaman nashi baida wani amfani ko alfanu ai gara ya koma bakin aikinsa saboda baya jin dadin wannan rashin jituwar da yake ganin yana faruwa kullum tsakanin mommy da daddy kuma duk a ta silarshi da sanadiyyarsa, ko breakfast bai yi ba kawai yayi wanka ya fita family house acan ya yi breakfast dan yana shiga gidan Ammi ya tarar suhana da Irfan suna kokarin karyawa suhana ta soya musu dankali tare da sos din kwai ita kuma Ammi din bata nan ta tafi raka hajiya gaisuwa,

Zama yayi yana kallon Suhana da tun bayan shigowarshi take kallon sa tana kunshe dariyarta,

"Yaya Afeef sannu da zuwa ina kwana?"

"Lafiya lau, ya aka yi ne? Dariyar me kike yi?"

"dariyar yanzu ka zama in law dina mana...."

Murmushi yayi ya zauna ya dan kalli Irfan kadan kafin ya mayar da kallonsa gareta,

"Bana son ki rinka yimin kallon in law, am your blood brother....."

"na sani ai yaya..."

"good...."

Shi dai Irfan yana jin su bai yi magana ba hankalinsa na kan breakfast dinshi da wayar shi dake hannun sa, janye flate din Afeef yayi ya kai gabanshi ya fara ci yana hararshi, girgiza kai Irfan yayi ya saki murmushi ya kalleshi yace,

"Good morning in law....."

Wata sabuwar hararar Afeef ya sake aika masa yace "bana son neman magana fa"

Dariya suhana tayi dake zaune tana jinsu sannan cikin ranta tana jin dadin yanda zumuncin ahalin nasu ke tafiya ta yadda har sun zamo tsintsiya, haka kuma kowa na kaffa kaffa da dan uwansa babu bambanci bare waraki, sallamar janan ta katse mata tunaninta kuma ta dawo cikin hayyacinta, atare duka suka amsa sallamar nan ta shiga cikin falon inda suke yin breakfast din,

"yaya Irfan ina kwana, Yaya Afeef ina kwana...." janan ta fada tana ajiyewa suhana dan karamin food flask din da ta kawo mata wainar fulawa,

"lafiya lau...." Afeef yace kadai yayin da shi kuma Irfan yaci gaba da tsokanar janan bayan ya amsa gaisuwar ta, cike da kunya kunya take amsawa Irfan kafin taja hannun suhana suka fice gaba daya daga cikin falon. Bayan fitar janan da suhana Afeef ya kalli Irfan wanda idonsa ke kan screen din wayarsa yana kallo yace,

"Irfan ina jin zuwa gobe zan koma calabar....." ajiye wayar Irfan yayi ya kalle shi yace,

"saboda me? Ba da naji kace sai zuwa upper week ba?"

Ɗan murmushin takaici Afeef yayi wanda ke kunshe da damuwa sannan ya kalli Irfan ya bashi amsa da,

"ehh but i change my mind..... Inada ayyuka da yawa.... I have alot of works soo kaga is better na koma instead of nayi ta zama a nan gida ina hutun jaki kaya aka...."

Ajiyar zuciya Irfan ya sauke yace "hakane but ya maganar ku da anty Mimi? Ko ba yanzu zaku tare ba?"

"Anty Mimi zata cigaba da zama a nan har zuwa lokacin da komai zai zama settled kamar hakan zai fi...."

"ok to hakanma yayi, in dai har kun riga da kun gama tsara komai kun fahimci juna ai shikenan ni ina ganin babu problem...."

"Yeah..." shine kawai abinda Afeef yace ɗan shuru ya ratsa falon kafin Irfan ya katse shurun da cewa,

"itama kamar bata nan taje hospital tun da sassafe.... May be an kirata emergency ne..."

"Allah ya dawo da ita lafiya" ya fada a hankali kuma daga haka bai sake cewa komai ba har suka kammala breakfast din, nan suka cigaba da zama suna kallon ball ahaka Ammi ta shigo ta same su sun dawo tare da hajiya daga ta'aziyyar da suka je,

Sauka daga kan Kujerar da yake zaune yayi ya durkusa ya gaida Ammi ta amsa cikin sakin fuska da kulawa sannan ta wuce ciki,

"wai ko har an fara yar surukuntar ne?" Irfan ya fada cike da tsokana saboda yaga har lokacin kan Afeef din na ƙasa bai ɗago ba sannan bai tashi daga tsugunnon da yayi ba,

"you are not serious..... Ammi ai uwata ce ba suruka ba"

"to ai naga kana ta faman sussunne kai ne...."

"to yanzu dai ka tashi mu tafi wurin hajiya...."

"muje... Fada ne zamu sha shi marar dalili tunda idan tsufanta ya motsa haka take yi"

Dariya Afeef yayi yace "dambun nama nake son a sammin tunda gobe zan tafi"

"zata baka ai.... Kuna shiri ai sosai"
Chapter 9 · 0% Book details