Sashe 3
Kaifi Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"duk lafiya lau" ta fada cikin jin kunya sannan ta koma gefe ɗaya ta zauna tana kallon Afeef din wanda ya sake suna ta hira da Ammi domin dama ko a waya ne suna kwashe lokaci mai tsawo suna hira bare kuma da gashi gata yanzu,
"kai matsalar ka baka son maganin gargajiya ne Afeef amma irin wannan lalurar taku dole sai ana hadawa da na Hausa...... Zan karbo maka indai zaka sha"
"to Ammi.... Insha Allah zan sha"
"kamar gaske..." Irfan ya fada cikin tsokana.
Sun jima zaune a part din Ammi har zuwa la'asar lokacinne suka fita, bayan sun yi salla suka shiga part din umma, itama kamar Ammi haka take da kirki da haba haba da mutane anan yanmatan gidan suka kewaye su a nata hira bama ya Janan da take ta jan Afeef da hira a takaice dai basu suka samu kansu ba sai magriba lokacinne suka zauna suna hira shida Irfan, cikin damuwa ya kalli Irfan yace,
"ni damuwata Allah yasa wannan matsalar ta anty mimi da yaya Aliyu bata taɓa zumuncin iyayenmu ba...."
"babu abinda ya taɓa zumunci kawai dai ka san dole kowa zaiji babu dadi, gashi nan dai kawai lamarin sai dai mu rakashi da addu'a..." Irfan ya bashi amsa yana kai kallon sa gate dan ganin wanda zai shigo saboda an bude gate din nan yaga Abbansu ne sai kuma Abban su Yaya Aliyu shima yana biye dashi cikin tasa motar a bayansu kuma Daddy ne wato mahaifin su Afeef, yanayin yanda zumuncin iyayensu yake dole ya burge kowa bama iya kadai su da suke matsayin ƴayansu ba,
Tashi suka yi suka nufi wurin iyayen nasu, nan kowanne ya fito fuskarshi dauke da fara'a da kuma farin ciki, kusan kullum dama a al'adarsu nan suke haduwa wurin hajiya suyi hira zuwa bayan sallar ishah kuma kowa sai ya nufi gidansa, idan akwai wata magana da zasu tattauna duk a wannan lokacin suke tattauna ta,
"soja marmari daga nesa....." Abba fari ya fada cikin tsokana yana kamo hannun Afeef dake kokarin tsugunnawa domin ya gaida shi,
"Mazan fama ba.... Soja mazan fama" shima Abbansu yaya Aliyu ya fada yana dafa kafadar Afeef din wanda daidai lokacin Daddynsu ya karaso tare da Irfan yana rike da hannun Irfan din, tare gaba daya suka rankaya suka shiga part din hajiya wanda dama tuni ta saka masu aiki sun yi shimfidu irin na alfarma kamar yadda aka saba yi musu kullum sannan ga kunun shinkafa nan da aka yi yasha madarar ruwa wadatacciya sai fruits da farfesu, kullum ta Allah wannan hidimar haka ake yinta,
Can gefe suka samu suka zauna shida Irfan wanda gaba daya yafi mayar da hankalinsa kan wayar shi dake hannunshi yana ta faman murmushi shi kadai,
"wai wannan murmushin da kake ta faman yi me yake faruwa ne? Kai da waye?"
Dariya Irfan yayi kafin yace "kayi min alkawari idan na fada maka ba zaka titsiye min budurwa ba kasa ta a gaba da tambayoyi.. “
" I promise... "
" ni da Manal ne..... Tana yimin wata hira ne "
Tsaki Afeef yayi yace," kuna gulmata dai... "
Shigowarsu yaya Aliyu da yaya faruk yasa gaba daya kowa ya maida hankali kansu, cikin girmamawa Irfan da Afeef suka gaida su saboda sune manyan yayu kuma suma age mate ne,fuska a sake yaya faruk da yaya Aliyu duk suka amsa, wurin da suke zaune kafin shigowar su yaya faruk din suka koma suka cigaba da hirar su har zuwa lokacin da su ka fita sallar ishah bayan sun idar Irfan ya maida shi gida, bai shiga ciki ba daga waje suka yi sallama ya wuce shi kuma ya shiga gida, mommy na zaune a falo ita da Manal ya shiga ya zauna kusa da mommy yana kallonta,
"mommy bakya nemana ne....." yace da ita yana turo baki,
"to ba ka tafi can danginku ba mu ka manta damu...."
Dariya yayi ya kwantar da kanshi jikin kujera yace,
"kai mommy nida tunda na zo ma ban fita ko ina ba sai yau....."
"to ai shikenan....."
Kafin ya kara magana wayar shi ta fara kara, duk tunanin shi zai ga Irfan lokacin da ya ciro wayar daga aljihunsa amma sai yaga yaya Aliyu ne, dauka yayi cikin nutsuwa yace,
"hello yaya haidar....."
"hello.... Afeef ya kake?"
"alhamdulillah yaya..."
"gobe dan Allah ina nemanka.... Zan kiraka da safe insha Allah sai in fada maka inda zaka same ni"
"ok to shikenan yaya, Allah ya kaimu"
Katse wayar yayi yana kallon Manal dake kallonsa ta zuba masa ido kamar yau ne ta fara ganin sa,
"what?" yace da ita shima yana kallonta,
"yaya..... Bani aron wayarka"
Mika mata yayi yana kokarin tashi, dan kallonta yayi yace "kina gama abinda zaki yi ki dawo min da wayata bacci zanyi"
"abincin fa? Ko kaci wurin kakar ku?" mommy ta tambaya idanuwan ta a kanshi,
"ehh wallahi na koshi mommy.... Kunu muka sha nida Irfan"
Daga haka ya tashi ya nufi part dinsa yana shiga wanka yayi kawai ya kwanta lokacin da ya kwanta kuma sai ya fara tambayar kansa to me kuma ya faru da yaya Aliyu ke son ganin sa? Bayan dazun nan suka rabu a gidan hajiya ai da idan akwai wani abu tun lokacin zai yi masa magana, da wannan tunanin bacci ya dauke shi baima san lokacin da Manal ta gama amfani da wayar shi ba ta kawo masa.
Tunda anty Mimi ta tashi yau haka ta tashi jikinta a sanyaye haka kuma ranta gaba daya a ɓace zuciyarta nata faman harbawa da kuma jin kunci, cikin wannan yanayin tayi wanka ta shirya ta fita aiki batare da tayi ko breakfast ba, tana fitowa hajiya na zaune falo tana shan tea saboda lokacin wurin karfe 11 na safe,
"Hajjaju ina kwana?"
Kallonta hajiya kaka tayi kafin ta gyara zaman gilashin idonta tace,
"takwara ya naga kamar har fita zaki yi baki karya ba?"
"ehh wallahi hajiya inada patients da yawa ne nasani suna can suna jirana...."
"to ai ko suna jiran ki dole ke kici abinci tunda aiki bazai yuyu ba sai an koshi..... Baza ki rinka nemawa wasu lafiya ke kuma kina janyowa kanki wata rashin lafiyar ba Mimi.... Ulcer fa gaskiya ce kin fini sanin haka.... Tsaya ki tafi da abinci kuma lallai lallai idan kinje asibiti ki ci karki zauna da yunwa "
Ba dan zata ci dinba kawai ta amsa da to aka yi mata packaging ta tafi dashi tana driving hankalinta duk a rabe sai tunani take yi, wannan shawarar da Yaya Aliyu yazo da ita wallahi gaba daya bata kwanta mata arai ba kawai dai dan babu yanda zata yi ne, da tunane tunane fal ranta ta shiga asibiti tayi parking motarta kai tsaye ta nufi office dinta kuma tana zama taji knocking,
"come in...." kawai ta fada ba tare da ta daga kanta ba dan ta janyo wani file ta fara rubutu a jiki, Aliyu ne ya shiga ciki yana sanye da farar shadda kar mai tsadar gaske kansa babu hula,
"good morning my love...." ya fada idanuwansa narai narai kamar zai fashe da kuka, sai lokacin ta dago da kanta tana kallonsa take taji ta kasa cigaba da rubutun da take yi kawai ta zuba masa ido tana kallonsa shima yana kallonta har tsawon mintunan da basu san adadinsu ba dan ahaka Afeef ya shigo ya samesu,
Cikin wani irin yanayi da ba zata iya fassara shi ba ta janye idanuwan ta daga kallon da take yiwa Aliyu ta mayar dashi kan file din da yake gabanta, tana tsananin son Aliyu irin son da bata san shi ba sai yanzu da saki har uku ya shiga tsakanin su ya zama katangar da ta raba tsakaninsu,
"Afeef ka karaso..... Bismillah"
"ehh wallahi yaya, ina kwana... Anty mimi ina kwana?"
Afeef ya fada yana sanye da kananan kaya jeans baƙi da t shirt coffee, fari ne sosai siriri dogo mai kyakkyawar sura, a haife bazai wuce 27 years ba saboda sa'an Irfan ne amma Irfan dinma ya girme masa da wurin watanni shida zuwa bakwai, ba tare da ta ɗago kanta ta kalleshi ba ta amsa ciki ciki,
"lafiya lau..."
Zama yayi kan kujerar dake gaban teburinta tana fuskantar yaya Aliyu, cikin damuwa da nutsuwa yaji yaya Aliyu yana yi masa magana kamar haka,
"Afeef.... Kasan kai matsayin ƙani kake gare mu nida Mimi, duk duniya yanzu banda wani wanda na yarda dashi sai kai haka itama Mimi, wallahi Afeef muna cikin wata masifa da jarrabawa, muna bukatar taimakonka.... Kai kaninmu ne na jini tushenmu ɗaya haka kuma mu ahali ɗaya ne sannan duk daga cikin tsatso ɗaya muke.... Tunda na saki Mimi rayuwata ta hargitse ta shiga garari itama kuma haka, dan Allah muna son kayi mana wani taimako ka auri Mimi na tsawon watanni biyu zuwa uku saboda bama son su Abba su gane ko su hajiya su fahimta.... Ba sai ta tare ba zaka saketa dan ina so ne zan mayar da ita..... Mun san idan wani muka samu na waje ba lallai ya cika alkawari ba sai azo ana samun problem ana kai ruwa rana watakila idan ba ayi sa'a ba har asarinmu ya tonu...... "
Cikin razani da tashin hankali Afeef ke kallon yaya Aliyu cikin ransa yana tambayar kansa anya yaya haidar bai haukace ba kuwa? Anya yasan abinda yake fada? Anty Mimi fa? To shi yanzu ta ina zai ma fara auren anty Mimi idan har lissafinsa bai rushe ba yana tafe daidai she's 32 or 33 yanzu dan wurin 4 years ta bashi,
"Afeef kana jina? Ka samu su hajiya ka fada musu kana son Mimi su aura maka ita na san ba zasu musa maka ba kuma baza su hanaka auren ta ba tunda duk gida ne...."
"yaya wai ka san abinda kake fada kuwa? Anya yaya lafiyarka ƙalau? Are sure you are okey"