← Book details Kaifi Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 21

Sashe 20

Kaifi Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inda ya mayar mazauninsa wato gefenta nan yaje ya zauna yanzu dinma ya kama hannunta yana wasa da yan yatsunta, bai san dalili ba haka kuma bai san me yasa ba kawai ya samu kanshi da kissing hannun nata sannan goshinta, ita dai bata san me yake yiba dan wani mugun bacci mai nauyin gaske take yi, sallar isha ce ta sake tayar dashi bayan sun fito ya zauna suka yi dinner da su hajiya da sauran iyayensu maza kamar yadda suka saba, shi dai kam yau baya jin zai bar part din hajiya shiyasa bayan kowa ya baje an watse ya shige bedroom din anty Mimi harda saka key ya rufe ƙofa, kan gadon ya hau ya kwanta kusa da ita yaja duvet ya rufe musu rabin jikinsu ya zaro wayar shi a aljihun wandon jeans din da yake jikinsa, ɗan short video yayi mata ita kadai sannan yayi musu tare tana ta bacci bata san abinda yake yi ba, text massage ya turawa mommy cewar zai kwana a family house wurin Irfan, ya san ba zata ce komai ba dan dama ya saba kwana tun suna yara wani lokacin sai yafi 1 month idan ta raya masa, latse latsen shi yake ta yi a waya har kusan 12 lokacin ne ya ajiye wayar kan bedside drawer dinta ya kwanta bayan ya shige jikinta sosai. Bayan asubah ya farka nan ya ganta har lokacin bata farka ba, shifa baccin nan nata fa kuma ya fara bashi tsoro, bacci tun jiya da safe wuni guda, awa nawa tana bacci, Allah Allah ya rinka yi a idar da salla ya koma ya tashe ta, Irfan na ta son ya zauna a masallacin saboda akwai ƴar takaitacciyar nasiha da ake yi kullum amma yaƙi yace zai rinka jiyowa daga dakin anty Mimi,

Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya shiga cikin bedroom din sakamakon ganinta da yayi a zaune kan gadon fuskar ta duk ta kumbura da idanuwanta duk tana jinsu sunyi mata nauyi, da kallo ta bishi har ya karasa shiga cikin dakin ya zuba gwiwowinsa a ƙasa ya dafa gadon yana kallonta,

"sannu..... Ya jikin?"

"Bani ruwa insha..... Mai sanyi" yaji ta fada ba tare da ta amsa sannun nashi ba, tashi yayi ya fita downstairs ya dauko mata bottle water mai sanyi ya koma, bude mata yayi ya mika mata ta karɓa yana kallonta bata ajiye robar ba sai bayan da ta shanye ruwan tas, komawa tayi ta kwanta ta juya masa baya mintuna kadan wani baccin ya sake kwasheta, zama yayi gefenta ya zuba mata ido a hankali ya kai hannunshi goshinta ya ɗora idanuwansa na kanta ko ƙiftawa baya yi,

Tun bayan da ya dawo daga masallaci bai matsa ko nan da can ba har 10 ta ɗan gota a lokacinne yan dubiya suka fara shigowa suna duba ta kuma hayaniyarsu ce ma ta tashe ta daga baccin da take yi, da kanta ta cire cannula din dake hannunta dan ta dameta sannan ta takura mata, breakfast suhana ta kawo musu amma tace a bari sai ta fara yin wanka sannan zata ci, jin hakan da ta faɗa ya sanya kowa dake cikin bedroom din fita, shima Afeef bin Irfan yayi suka fita zuwa part din Irfan, wanka yayi ya saka farar jallabiya sannan ya koma dan yasan yanzu kam ta gama shiryawa, knocking yayi sau ɗaya kuma bai zauna zaman jiran a bashi izni ba ya tura kansa cikin dakin, tana zaune gefen gado daure da towel da cup a hannunta tana shan tea,

"ya jikin naki?" ya tambaya yana kallonta kamar yau ne ya fara ganin ta,shuru yaji babu amsa nan ta cigaba da shan tea dinta har ta sha rabin cup din sannan ta ajiye ta tashi a hankali ta wuce gaban closet ta ɗauki doguwar riga ta shan iska ta saka bayan ta feshe jikinta da turare, komawa kan gadon tayi ta zauna fuskar ta duk a cunkushe, tea din da yaga ta rage ya dauka ya fara sha yana ta faman aikin kallonta, kwanciya yaga ta sake yi ta dan lulluba da duvet duk da ba bacci zata yi ba,

Zaman kurame suka cigaba da yi har Ammi ta zo, kallon Afeef Ammi tayi bayan sun gaisa tace,

"Afeef ai ya kamata kaje gida ka huta kaima, ka samu kayi bacci...."

"A'a Ammi babu komai.... Bana jin bacci, I don't want to leave her side...."

"duk da haka ko baka jin bacci kana bukatar hutu, tun jiya kake zaune anan kuma daga ganin idanuwan nan naka baka samu isasshen bacci ba da daddare, kaje gida ka huta......"

"to Ammi bari naje zuwa azahar sai na dawo...."

"A'a azahar ai baka wani huta ba, kaje zuwa dare sai ka dawo, zan turo suhana ta zauna tare da ita kafin ka dawo..... Kana bukatar hutu kaima kaji...."

"to Ammi..... Bari naje, Allah ya bata lafiya"

"amin, Allah yayi maka albarka"

Tashi yayi ya fita, duk abinda yake faruwa anty Mimi tana jin su, bayan ya fita Ammi ta zauna tana kallonta,

"wannan yaron yana ta faman kokari a kanki..... Tunda kika kwanta yake dawainiya dake baci ba sha..... Ubangiji Allah ya saka masa da alheri, hakika wani hanin ga Allah baiwa ne" tana jin Ammi har tayi ta gama dai bata tanka ba, so take ta tambayi jikin yaya Aliyu amma ta rasa wa zata tambaya, so take taji har yanzu bai samu lafiya bane ko yaji sauki? Ta san bata isa ta tambayi Ammi ba ko hajiya shiyasa ta ja bakin ta tayi shuru amma kuma tana son sanin halin da yake ciki. Koda Afeef ya koma gida kamar yadda Ammi ta saka shi every 30 minutes yake kiran Irfan yaji ya jikin anty Mimi, bayan sallar la'asar video call ya kirashi yace yaje bedroom dinta yana son ya ganta, tashi Irfan yayi daga kusa da hajiya ya nufi upstairs wurin anty Mimi, kai gaskiya Afeef fa kamar ya shiga da yawa dan abubuwan da yake yi sun zarta hankali, tana kwance tana baccin dai kamar jiya yau ma din ta wuni tana bacci ne, kallonta yake yi ta cikin wayar tashi,

"hankalinka ya kwanta yanzu?" Irfan ya fada cikin tsokana,

"ba sosai ba, me yasa zaku barta ita daya?"

"ba ita daya bace wallahi ita da suhana ne na jiyo motsin ta acikin toilet...."

"ok tom sai na zo, anjima nima zan shigo, bana son in saɓa umarnin Ammi ne"

Magriba nayi ya tafi shida Manal, yanzun ma jallabiya ce a jikinsa amma baƙa ta ciki yasa wando jeans, niyyar shi yau ma ya kwana wurinta amma tunda ya shiga dakin shida Msnal yaga tana ta faman ɓaɓɓata rai iya Manal kadai ta amsawa shi kuma tayi banza dashi, fita yayi zuwa masallaci saboda lokacin salla ya yi, bai koma wurinta ba sai bayan sallar isha bayan su abba sun gama zaman majalissun su, tare da daddy Manal suka tafi shi kuma ya zauna kuma a lokacinne ma yake jin labarin yaya Aliyu yaji sauki dan yanzu daga wurinsa yaya faruk ya dawo. Daren yau kam bata jin bacci ko kadan, lokacin da Afeef yaje bedroom din jinsa yayi ta garkame kayan ta da key nan yayita knocking amma taki budewa,

"sauki ya samu kenan...." ya fada cikin ransa tare da juyawa ya koma wurin Irfan, kallonsa Irfan yayi amma sai bai ce komai ba saboda yanzu wasu abubuwan da suka shafi anty Mimi da shi babu bukatar ya rinka tsoma bakin sa sai dai ya zuba ido kawai dan sun fi kusa............✍🏻

KAIFI ƊAYA... ✨

*When the world called her “useless”… he called her “mine.”*💘

_KAIFI ƊAYA_ is not just a love story. It’s the story of Mimi - a doctor whose name was dragged through scandal, whose body was broken by fate… 💔
And Afeef - the man who chose to stay when everyone told him to leave. 😥

They won the fight against the world.
But can they win the fight for each other, when silence is louder than lies, and love is tested by things neither of them chose? 🥺

*One blade. One choice. One love that refuses to break.*❤️
_Kaifi Daya_ - because true love doesn’t walk away when you can’t walk anymore..😥

It's available now 07044644433

Your heart will not be the same after the last page🥰✍🏻✍🏻

#Kaifiɗaya
#emotionalromance
#lovetriangle
#AliyuHaidar
#DrMimiAndAfeef

*_Ummi Shatu_*👌🏻
[7/18, 9:02 AM] Oum Jasrah: https://www.arewapen.com/book?id=6a50f2f571e75baab6622006

KAIFI ƊAYA....!

NA
UMMI A'ISHA

16

***Kamar zai yi kuka saboda bata barshi ya kasance acikin dakin ba, haka kuma baccinshi sama sama yayi domin kowanne bugun zuciyarshi tunaninta ne gaba daya ya kasa gane wanne irin yanayine wannan ya samu kansa and it's not just pity anymore its turning into something deeper, ita kam anty Mimi tana can cike da tunani kala kala hakika wannan sharadin da Abba ya saka mata tsakaninta da Aliyu yayi mata tsauri da yawa tunda ko babu komai ɗan uwanta ne bai kamata a raba su har haka ba, tashi tayi ta lallaba ta fita zuwa wurin hajiya wacce har ta kwanta amma dai ba bacci take yiba,

"hajiya wurinki na zo.... Dan Allah wata alfarma nake nema, ki taimaka min ki rokar min Abba akan ya sassauta min wannan sharadin da ya saka, wallahi yayi tsauri da yawa, ai ko babu komai yaya Aliyu dan uwana ne tayaya za ace ko gaisawa baza muyi ba? Naji na yarda bayan gaisuwa babu abinda zai kara hadani dashi amma a bani dama in duba shi ko ta waya ne dan Allah hajiya "

"Kinga ki kiyaye ni da maganar duba Aliyu dinnan fa, yadda uwarsa take tashen rashin mutunci yanzu wallahi komai zai iya faruwa tom...."

"ni babu ruwana da Umma iya yaya Aliyu nace...."

"shikenan na baki dama kiyi masa ya jiki, zuwa gobe da safe shikuma Alhaji ƙarami zanyi masa bayanin komai..."

"yawwa hajiya nagode...."

Ai sai taji har taji kwarin jikinta, da sauri ta koma bedroom dinta ta zauna ta dauki wayarta ta fara neman layin yaya Aliyu, babu kowa cikin dakin sai shi kadai dan umma ta fita saboda suna sa ran za a basu sallama zuwa gobe,

"Mimi..... Mimi ashe dama zan sake ganin kiranki cikin wayata?"
Chapter 20 · 0% Book details