← Book details Gurbin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 113

Sashe 93

Gurbin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cak numfashinta ya dauke na wucin gadi, kafin ta samu nasarar fusgoshi kuma hannunsa ya fara yin sama,har ya samu nasarar isa muhallin da taketa bawa kariyar,sai ji tayi ta ratsa hannuwan nasa a tsakaninsu da wani salo da ya sanyata dauke wuta.

Qugunta ya riqo da kyau sanda qafafunta suka soma rawa,ya matso da ita jikinsa sosai yana sanya hannunsa ya zare hannuwanta dake riqe da gaban rigar,sannan a hankali ya hada tafin hannunsa da ainihin fatarta mai santsi da laushi ya fara zame rigar gaba daya daga jikinta.

Qanqameshi tayi da kyau don hana faruwar hakan,ta tabbatar idan ya samu nasarar rabata da rigar komai zai iya faruwa,don babu wani abu daya rage a jikinta sai ita,cikin rarrabewar numfashi da yadda laushin fatarta ke shirin zautar dashi ya dora bakinsa saman kunnenta

"Don't scare,baccin gajiya kawai nazo muyi" sake qanqameshi tayi tsigar jikinta na tashi,bakinta na rawa tace

"Ammm.....bar.....bari na saka riga" dago fuskarta yayi da kyau yana duban tsakiyar idanuwanta da idanunsa da suka soma kaduwa,kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace

"Waye ya gaya miki saka riga ya halatta a irin wannan lokacin?,this is unfair....kamar ha'inci ne fa?,ya zaki lullubemin abun rufar da babu kamarsa a duniya da wata suturar da bata kama qafarsa daraja ba?" Ya fada cikin wani irin shauqi da baisan gana bayyana ba,ya kuma juye mata dukka nauyin maganganun hade da nauyin qwayar idanuwansa,gaba daya jikinta sai ya saki,ta runtse idanuwanta,tana sauraren yadda yake rabata da rigar gaba daya,sannan ya dauketa kai tsaye zuwa kan gadon bayan ya sauke dukka labulen dakin ya kuma rage hasken qwayayen dake ciki,sai dakin ya bada wani ni'imtaccen yanayi.

Sosai ya manne fatar jikinsu waje daya,ya boyeta cikin faffadan qirjinsa,kusan tare suka saki ajiyar zuciya,ya sanya hannunsa saman kanta a hankali yana shafar sumarta,idanunsa a rufe yana jin bugun zuciyarta,kana daga bisani kuma yaji ya sauya,alamun dake nuna bacci ya dauketa,hannunsa ya dauke daga saman kan nata,ya jata jikinsa sosai yana jin kamar ya bude qirjinsa ya sakata a ciki,babu jimawa shima wani daddadan bacci yayi awon gaba dashi.

*Arewabooks:Huguma*

#gurbin ido

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR CONTINUES PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 74

Sun jima a hakan kafin ya bude idanunsa a hankali,sannan ya miqe ya zauna yana kallon cotton din yadinsa fari qal daya ya mutse,ya fara maida button na rigarsa,sannan ya duqa qasan motar a hankali ya lalubo hijabinta ya matsa a tausashe ya miqa mata,bata iya hada ido dashi ba,ta miqa hannu ta amsa ta zura,sai daya tabbatar ta saka sannan ya dage coloured glass din da ya sauke din,ya sanya hannu ba tare da yace komai ba ya buda murfin motar,ya zagaya ya bude mata,ta zura qafafunta a hankali ta fito.

A gaba ya sanyata yana biye da ita kamar wani bodyguard dinta har zuwa office din da ake shigar da dawowar dalibi a register,ya cike komai ya kuma ce kada a sake barin kowa yazo daukanta,sai yazo da kansa ko kuma ya bada umarnin a dauketan,cikin ma'aikatan su suka daukar mata jakankunanta,cike taf da kaya fiye da yadda ta saba zuwa dasu,kamar zata bude qaramin provision.

Tana takawa a hankali zuwa dakunan kwanansu amma tana jin idanunsa cikin jikinta,ta tabbatar yana tsaye yana kallonta,saidai bata waiwaya ba har ta qule.

Nannuyar ajiyar zuciya ya sauke,yana jin kamar an cire zuciyarsa an wurgata can nesa dashi,sai ya waiwaya jiki a mace ya buda motar tasa ya tadata yabar cikin makarantar yana jin duk wani farinciki da yayi saura a zuciyarsa yana raguwa.

Numfashi ta sauke tana duban dakin nasu,tayi missing nasa,saidai yadda ta dauka zatayi farinciki da da dawowa cikinsa sai ta lalubi hakan cikin zuciyarta ta rasa,hasalima wani mutuwar jiki takeji da kasala,sai ta zauna bakin gadon ayman,ta zare socks din qafarta da takalminta ta wuce toilet ta daura alwala.

Sallar la'asar tayi,tana son binsu masallaci amma kuma batason garin murnar nan tasu suyi mata tarere,don haka sai ta bude jakankunanta,ta fara fidda kayanta tana shiryawa.

Kafin wani lokaci ta gama shirya komai yadda ya dace,ta sake kintsa musu dakin,wanka take som yi amma ta kasa,sai ta koma ta kwanta gadon afrah tana jin wata lafiyayyar gajiya tana bin jiki da gabobinta,haka kawai takejin zuciyarta duka babu dadi,walwala da dokin dawowa makarantar duka sun kau,ta lumshe idanuwanta,abun mamaki sai tunaninsa ya soma mamayarta,ta fara hangen fuskarsa a mabanbantan lokutan da suka kasance tare dashi.

Ganin lokaci na tafiya kuma ta gaza hasala komai sai ta yunqura ta miqe tana duban dan qaramin agogonsu dake jikin bango,wanda afra ce ta maqala musu,tace hajjanta wato kakarta ce ta bata shi,yau kamar sun dan gota lokacin dawowarsu,ta miqe ta shiga dube duben dakin babu abinci,kuma yunwa take dan ji,duk da taci abinci kafin su fito,don takeaway ya mata na musamman da abinda taji ranta yana so.

Babu sauran abinci a cikin dakin,da alama ma basu dafa komai ba,a kitchen suka karba abinci,sai ta zari hijabinta har qas ta zura ta sanya slippers ta fito,tana tuna maganar da ja'afar ya gaya mata sanda suna kan hanya,hannunsa na cikin nata

"Please ki kularmin da kanki,ki adanamin kanki da kyau,don babu yadda zanyi ne da anni,kamar uwa take a wajena,banda ita abbi da amma babu wanda ya isa yayimin wannan hukuncin na yarda dashi,zan iya mutuwa wallahi angel......ina da kishi sosai.... please take care of yourself".

Ajiyar zuciya ta saki ta qarasa shiga kitchen din,mama's dinsu dake musu girki dukka ta samesu suna nan,kowacce cikin fara'a ta soma mata maraba,ita kuma tana gaidasu cikin matuqar girmamawa,suna son maimunatun sosai saboda yadda take martabasu,ba kamar wasu daliban da suke ganin sun fito daga gidan gata ba,ana.biya musu school fees almost one million naira so babu me takurasu

"Munata jajjabin rashin dawowarki,sai afra tace ai kunyi tafiya ne keda 'yan gidanku"

"Eh wallahi mama"

"To madalla,an dawo lpy ko?"

"Lafiya lau mama,zan samu abinci kuwa?"

"Eh akwai na rana da akayi,bari na duba miki" ta fada tana buda babbar tukunyar,ta deba mata cikin plate maimunatun ta karba tayi mata godiya kamar yadda ta saba tana cewa

"Idan kun tashi aiki mama kiyimin magana,sai ku karbi tsarabarku" kusan hada baki sukayi wajen mata godiya,indai kyauta ne maimunatun ba daga nan ba,ta juya ta fice da abincin a hannunta.

Sam bata kula da tahowarsu ba,gab da zata isa dakinsu taji an saki ihu,kafin ta waiwayo taji an rungumeta tsam ta bata,ayman da fatima kuma suka zagayo ta gabanta suna riqe da hannunta gam,wanda saura kadan abincin hannunta ya kife a qasa

"Daga ina?,saukar yaushe?,wai mu zakiwa suprise moon?,kin barmu gaba daya makarantar babu dadi?" Murmushi ta sake musu,ita jikinta gaba daya babu wani cikakken qwari

"To sakeni afreen,afwa,wacce tambaya zan amsa miki a ciki?"

"Duka" ta fada tana sakinta gami da zagayowa gabanta tana murmushi,sai kuma ta fidda idanunta waje gaba daya,ayman tayi caraf tace

"Kinga abinda na gani sis afreen?"

"Ko makaho ai dole ya gani....moon?,me captain yake baki?"

"Banason iskanci afreen,zaki fara ko?" Cikin qyalqyala dariyar farinciki tace

"Wallahi Allah am serious,kinga yadda kika qara fresh?,jikinki kamar jini zai diga?,don Allah bai saka miki dokar sanya niqaf ba?"

"Saidai ki bashi shawara 'yan wulaqanci.....mu qarasa daki don Allah" ta fadi saboda yunwa da gajiya da tsaiwar da tayi.

Cikin dakin suka bude sabuwar hira,gaba daya sun sakata gaba kan irin yadda ta qara kyau da kuma yi fresh da ita

"Wallahi honeymoon tayi kyau,Allah yasa an samo mana dan lagos to johannesburg" afra ta fada tana kwanciya saman gadonta tana dariya,har qasan ranta tana jin dadin canzawar aminiyar tata.

Duka maimunatu ta d'ana mata a bayanta tana cewa

"Mara kunya kawai,ni ba abinda ya shiga tsakanina dashi,ni da sauran kunyata"

"An fada a radio" ta amsa mata tana sake sheqewa sa dariya,dariyar ta baiwa maimunatu,sai kawai ta murmusa itama.

"Allah ko,inda nice ke banga abinda zaisa na dawo makaranta ba,kuma wai boarding tabdi" ayman ta fada tana duban maimunatu,idanu ta fidda

"Yaushe afreen ta bata ku da son aure?"

"Dan sunna yaqi sunna" ayman ta amsa mata tana dariya.

Anan sukayi sallar magariba da isha'i tare,don ko fita cin abinci basuyi ba tsabar hira,fatima ce taje kitchen ta karbo musu, maimunatu ta hada da tsarabar su mama fatiman ta kai musu.

Sai wajen goma na dare kowa yayi shirin kwanciya,saboda gobe suna da shiga lab qarfe takwas,malamin kuma yace duk wadda ya rigata shiga ba zata shiga ba,tasu tsarabar ta ware,dogayen riguna ne masu kyau irin daya,sosai sukayi murna kamar basu taba sawa ba,duk da kowacce a cikinsu tafi qarfin abin,amma hausawa sukace alkhairi dadi gareshi,koda kafi qarfin abun.

Ba'a rufa awa daya ba dakin ya dauki shuru,da alama bacci ya daukesu,sama ko qasa maimunatu ta nemi bacci a idanunta ta rasa,ta dinga juyi tana canza position da wajen kwanciya,saidai still dai kwanciyar babu dadi,ta dinga jan qananun tsaki,gadon ne babu dadi ko kuma katifar?,ko sauyin wajen kwana?,sai ta rasa amsar tambayar,can wani sashe na zuciyarta kuma yanata qoqarin danne abinda ke taso mata,tana ta qoqarin karyata zuciyar tata,yaushe ta sanshi?,yaushe sukayi sabon da zata ji babu dadi don babu shi a kusa?,kwata kwata sai kwanciyar taqi mata dadi,ta runtse idanunta da kyau tana qanqame filo a qirjinta,tana son tilastawa kanta yin baccin ala dole.
Chapter 93 · 0% Book details