← Book details Gurbin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 113

Sashe 59

Gurbin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Iska me zafi ya furzar daga bakinsa yana cire guda daga cikin suit dinsa ta saman,ya kuma saqaleta a suit hanger dake cikin office din,sannan yayi taku biyu ya isa rukunin kujeru masu taushi dake gefe guda a cikin office dinsa,wanda aka tsara wajen tamkar ba cikin office din yake ba.

Opposite jabir dake binsa da kallo ya zauna ba tare da ya daga kai ya dubeshi ba,duk da kuwa yasan shi yake kallo sarai,ya daga qafanshi ya zame qawataccen takalmin dake qafarsa yayi wurgi gefe dashi,ya rage sai socks kawai a qafar tashi

"Wai anya kuwa kasan me dame ka fada wajen meeting din nan?,abinda ka dinga fadi baiyi making sense ba......lafiyarka qalau kuwa yau?" Ya masa tambayar sanda ja'afar din ke tuttulawa cikinsa ruwan sanyi,cike da fatan abinda yakeji ya tsirga masa.

Bai amsa masa ba sai daya qarar da ruwan dake cikin gorar tas yayi wurgi da ita itama,sannan ya sauke idanunsa cikin na jabir,abinda ya sanya jabir din karantarsa,ya kuma sauke boyayyen murmushi

"I know......" Ya amsa masa kai tsaye

"I don't think so" shima ya maida masa da amsa,janye idanunsa yayi daga kan jabir din yana lumshesu sannan ya budesu,kamar zaice wani abu sai ya fasa,ya miqe a hankali yana roller hannun rigarsa zuwa sama don ya samu daman yin alwala,ya taka sannu a hankali zuwa qofar toilet din nasa,ya turata ya shige.

Madaidaicin toilet ne amma ya tsaru matuqa,hakan ya bashi damar lashe kudade masu yawa saboda toiletries da aka zuba masa masu tsada da kyau sannan kuma sabbin design,babban mudubi ne daga wani side daban da zai baka daman ganin kanka sosai,a gabansa ya tsaya yana kallon kansa yana kuma murza sumarsa da hannunsa,ta qasan zuciyarsa yake magana da kansa da kansa,he really made a mistake,ya manta wayeshi.....me ya kaishi kusanta kansa sa wata mace?,to wai hakan ma yana nufin akwai improvement kenan daga depression din da zuciya da ruhinsa ya fada?,tunda har gashi zuciyarsa da gangar jikinsa sun fara neman wani abu daban wanda a baya ko tunaninsa babu a ransa?,hannayensa ya tara a qasan famfo ya cikasu da ruwa ya watsawa fuskarsa,ya sauke ajiyar zuciya yana gaining courage daga can zuciyarsa,yana jin zuwa anjima kadan zai manta komai,komai zai wuce,da wannan ya samu ya daura alwalarsa ya fito,ya samu jabir tsaye dab da rigarsa yana duba takardun da suka gabatarma da juna wajen taron,kai ya daga ya dubeshi

"dude........ina ka samo wannan turaren ne?,but......scent din nasa kamar na mata...,kamar my tee ta taba ban cigiyarsa na kasa samunsa" rasa amsar da zai bashi yayi,yace masa a jikin qaramar yarinya maimunatu ya sameshi?, Ko yace masa rungumeta yayi qamshin ya tabashi

"Ka shiga kayi alwalar muyi salla,lokaci yana wucewa" tuni ya sanya masa ayar tambaya,sai ya gimtse murmushinsa,ya wuce toilet din yana addu'a cikin ransa

"Ya rabb,ya rabb.....ka sanya lokacin nan ya zamo na sauyawarsa".

Duk da miskilancinsa amma shurunsa yayi yawa,haka suke tafe a hanyarsu ta komawa dakin taron,taro yaci gaba kamar yadda yayo announcing business partners din da suka halarci zaman,saidai jabir yana biye dashi,gaba daya kamar ba ja'afar ba yau,ja'afar very energetic person,amma yau din yanata abu kaman mara lafiya.

Biron hannunsa ya aje saman table din bayan yayi singing wata takarda,zai tura file din jabir ya karba yana duba singing din,sai ya zubewa ja'afar idanunsa

"Me yake damunka yau?,kaga abinda kayi jikin takardar nan kuwa?" Ya fada masa da harshen hausa qasa qasa,duk da cewa dukka mahalarta taron babu bahaushe ko daya bare ya fahimci abinda yake fada masa

"it's better to let everyone go.....ka sanya wani time and date din a qarasa abinda bamu gama ba" bai jaa da cewar jabir ba,don a jikinsa yaji yana buqatar hutu,cikin mutuntawa girmamawa da sanin ya kamata jabir ya juya yayi musu bayani gwargwadon yadda zasu fahimta ba tare da jin damuwa ba.

Ko kafij jabir din ya gama sallamarsu tuni ya yima drivernsa magana,don haka ko ta office dinsa bai koma ba ya wuce parking lot driver ya tashi motar sukayo gida,yau ko ta eatery din bai biya ba bare ya samawa kansa abinda zaici.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 43

Sai da suka tsaya masallaci sukayi sallar azahar sannan hisham ya sake daukansu wuce asibitin,gab da zasu qarasa ya soma slow da motan,jaafar dake duba wani abu a tab dinsa ya daga kai ya dubeshi

"Uhmmm,ya dai?"

"Naga masu fruit ne,akwai paw paw a ciki,zan siya ma maimunatu" sai ya maida kansa ga abinda yakeyi baice dashi komai ba,har ya buda motar ya fita yaje ya siyo,ya dawo ya tashi motar suka wuce.

Dakin babu kowa,don duka sun yoye sun tafi,daga ita sai amnan sai baba talatu data shiga bandaki zata dauro alwala,tana zaune a saman gadon amna ta zame mata dankwalinta ala dole wai sai ta yi mata kitso,tana ta jagwalgwala mata sassalkan gashinta ta kasa kitsawa saboda sulbi da santsinsa,jikinta akwai sauran zazzabi,an yima likitan bayani yace zai shigo ya dubata,tana biyewa amna dinne kawai don kada yarinyar taji babu dadi.

Batayi zato ba bare tsammani sassanyar muryarsa ta furta sautin sallama hadi da turo qofar dakin gaba daya,tashin farko kuma idanunsa suka sauka a kanta lokacin data rude ta kuma tsorata tana neman dankwalinta,wanda bata sani ba amna ta jefa mata shi qasan gadon,shi yasa ta kasa ganinsa,idanunsa ya dauke ya waiwaya baya inda hisham ke biye dashi

"Wait for a while"

"Okay" hisham ya amsa masa ya kuma ja baya ya tsaya ba tare da yasan dalilin ja'afar na fadin hakan ba.

Koda ya shigo din gaba daya ya maida hankalinsa ga amna wadda ta diro a gadon fa kuma rugo da gudu zuwa gareshi tana kiran sunanshi,haka kawai yaji baya son ganinta haka,ya budewa yarinyar hannayensa bayan ya durqusa yana jiran qarasowarta,zuciyarsa kuma na tuna masa da lokuta irin haka a baya,lokuta mafiya farinciki a rayuwarsa,lokutan da ita da twin sister dinta amra ke rige rigen isowa gareshi,mamansi shahida na tsaye tana kallonsu tana kuma murmushi,sai gashi a yau yarinyar ita daya ta rage masa a cikin guraben farinciki guda uku da yake dasu,tana qarsowa kuwa yayi sama da itama ya cillata kan ya rungumeta cikin jikinsa.

Kafij su gama ganin murnar ganin juna ta lalubo dankwalin da qyar ta yane kanta gaba daya zuwa saman qirjinta,duk da hankalinsa na kan amna amma yana ankare da ita,baisan me yasa take tsoronsa haka take kuma rudewa duk sanda yazo wajen ba,tun ranar daya tsorata tan randa suka baro gembu zuwa gombe,sauke amna yayi a hankali

"Kice da uncle ya shigo yana waje" da dan gudunta ta fice,sai a sannan ya sake maida dubansa kanta,ta nutsu guri guda,wanzuwarsa a wajen tana sata jin kamar wani zazzabin zai sake qaruwar mata,kwata kwata batason ganinsa a waje idan tana nan

"Ina wuni?" Ta fada da muryar nan tata dake da tsananin zaqi da sanyi,shi kansa ya yadda da hakan,idan tayi magana wani sauti take bayarwa na musamman

"Ya jikin?" Ya tambayeta ba tare da ya amsa gaisuwarta ba,yana bin ledar qarin ruwa da aka cire mata da kallo

"Da sauqi" ta bashi amsa dai dai da fitowar baaba tabawa daga bandaki.

"Barka da zuwa,yaushe ka shigo?"

"Yanzu" ya amsata yana waiwaya ga hisham dake shigowa dakin da sallama,kanta ta daga tana amsa sallamar,yadan kalleta ta gefan idanu,akwai dan qaramin murmushi saman lebanta tana dubansu shi da amna,gaisawa shima sukayi da baaba tabawa,ta tayar da sallah,sannan ya matsa inda maimunatu take

"Yanzun don kada a bamu tsarabar boarding shine aka kwanta ciwo?" Shima tana jin nauyinsa sosai,amma ko kwatar na miskilin yayansa me fuskar shanu bai kai ba,akwai dan sabo haka a tsakaninsu,don haka murya can qasa ta yadda take zaton ja'afar bazaiji ba tace

"Kaidai tunda sai yau kk zuwa dubiyan ai shikenan"

"Am sorry.....wallahi ayyuka ne suka yimin yawa kwana biyu,ga teaching hospital da nake zuwa musu sau biyu a sati suma kyauta...."

"Allah ya taimaka" ta fadi duk a darare,ita inda zai fita ya basu waje ma da sai tafijin dadin hakan,ledar gwandar ya tura mata

"Nayi dubiya me kyau,tunda.na kawo miki mutuniyarki ko?" Ya fada yana dubanta yana murmushi,maganar da ta sanya ja'afar karantar fuskarta a fakaice,wanda a zahiri zaka dauka kacokam hankalinsa na ga surutun da amna ke masa,sai yaga fuskarta ta washe sosai,karo na farko da ya taba ganin irin haka tattare da ita

"Na gode sosai,Allah ya saka da alkhairi,ya bada lada" maganar ta tsaya masa a rai,kwatankwacin addu'ar shaheeda kenan duk sanda aka yi mata alkhairi komai qanqantarsa.

Juya gwandar kawai take,tana son sha amma dashi da hisham din duk sun cika mata waje,sanda baba tabawa ta idar da sallar likitan ya shigo,maimunatu ta daga kai a hankali gabanta yana faduwa,ta tuna maganarsa ta jiya,yace indai yazo yau ya samu da sauran zazzabin a jikinta to lallai duk qinta da allura saidai tayi haquri ayi mata ita,a duniya allura itace abu na farko data tsana ta kuma qi jini,daada tafi kowa sanin hakan,don tun kafin rasuwarta akwai sanda bata da lpy,ta takura sai anyi mata takusa shide mata,abinda yasa tun daga ranar bata qara bari anyi mata ba.

"Dr hisham marwan?" Likitan ya fada yana diban hisham,da alama akwai sanayya sosai a tsakaninsu,don shima hisham din yana kallonsa ya kama sunansa,hira suka barke da ita,yana duba file din maimunatu,da treatment din da aka bata daga daren jiya zuwa yau,sai ya daga kai ya dubeta

"Har yanzu da zazzabin?" Kafin ta amsa baba tabawa ta rigata

"Akwai likita,ai har magana aka yo muku dazun"

"Ba damuwa,zai sauka yanzun in sha Allah,qila ma idan akayi wannan allurar basai an sake wata ba" fadin haka kawai sai idanunta ya fara tara hawaye,cikin mamaki a kuma sace ja'afar ke kallonta,bawai tana nufin kiran za'a mata allura ke shirin sanyata kuka ba?,ya hangi zallar tsoro baro baro a idanunta,ta kuma kasa sukuni sanda taga yana hada ruwan allurar waje daya.

Kida wayarsa ta farayi,sassanyar busa me ratsa zuciya,ya cirota ya duba me kiran,sai ya soma takawa a hankali yana ficewa a dakin yana amsa wayar.

Daya daga cikin amintattun ma'aikatansa ne,suke gaya masa motocin da ya siya sun iso,suna lagos,za'a biya kudin clearance da sauransu

"Ayi duk abinda ya dace"
"Okay sir" ya amsa masa a ladabce,ya kashe wayar yana juyowa,dai dai sanda baba tabawa ta iso riqe da hannun amna
Chapter 59 · 0% Book details