← Book details Gurbin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 113

Sashe 28

Gurbin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baki gani ta kusa kamoki a qiba?,amna bakisan yanzun kin girma ba,saura kadan ki cika 4years fa" kafada ta noqe tana buya bayan maimunatu sanda yake shirin karbarta,a dole ya haqura da amsar nata,maimunatu ta wuce da ita bayan ta gaidashi,ya amsa yana binta da kallo har sanda ta bacewa ganinsa.

Cikin jikinta takejin wani iri a duk sanda haisam yake mata irin wannan kallon,batasan ma:anarsa ba,ba kuma tasan dalilinsa ba,ya mata shige da kallon da himunta yake mata,amma dai tana jin nauyi da kunya sosai.

A dining area suka tadda khadim,shi ya karba amna daga wajenta,ta bashi ba don ta gaji ba,sai don khadim din shima mutumin amna ne na gaske,saidai tun bata isa dakin anni ba sai ga amnan ta sake biyota,ta kama hannuwanta tana dariyar meya hadota da khadim din taga ta bata rai,bata amsa mata ba suka wuce.

A hankali anni ta ajjiye wayar gefanta tana fidda ajiyar zuciya,dai dai lokacin maimunatu ta shigo dakin,goye da amna a bayanta,kusan wannan al'adarta ce,mtuqar zasu tattaka zuwa wane waje kamar haka sai ta dauketa ta aza a bayanta,dukkaninsu fuskokinsu dauke suke da dariya,da alama wani labarin suke baiwa junansu.

Idanun anni a kansu,wani abu ya darsu a ranta,kusan tafi kowa jin dadin qulluwar wannan kyakkyawar mu'amalar tsakanin amna da maimunatu,taci gaba da kallonsu a fakaice,farinciki ne shimfide saman fuskarsu,wanda abune da ba kasafai ake ganinsa akan fuskar amna ba,tun daga sanda ta rasa mahaifiyar da 'yar uwarta da suka kwanta ciki daya.

Kwarin gwiwa gami da yaqini taji yana shigarta,zuciyarta na bata shawarar tunkarar maimunatu,gwara tun yanzun tasan da maganar,tana ganin kamar hakan zaifi dacewa,akan ta samu zanca lokaci daya,amma kuma idan ta aikata hakan maimunatu zata ci gaba da walwalarta da sakewa dasu yadda take a da?,babu gamsashen tabbaci akan hakan,abinda yasa hankalinta yafi karkata da barin maganar a cikinta,har zuwa sanda zata gama magana da ja'afar kan ainihin lokacin da zai dawo cikin ahalinsa.

Ta baya jabir ke kallon ja'afar kadan kadan,cikin ransa yana juya maganar da suka fara yi da anni a kansa.

Yana tsaye ne yana shirya kansa cikin wasu lafiyayyun suit saqar qasar Italy kamfanin kiton k-50 wine color masu dan haske kadan,agogon hannunsa gold color ne na companyn lange and sohne mai asalin tsada da kyau.

Bayan ya feshe jikinsa da mayen tattausan turaren bad boy,ya zauna baya a hankali yana saka socks dinsa,sai a sannan jabir yayi magana,ganin cewa tunda ya shigo shi din bai ce masa komai ba

"Ina zaka ne haka a wannan lokacin?" Sai daya daga kai ya dubeshi sannan ya sauke yana ci gaba da sanya safar

"Ka manta yau wacce rana ce?" Dan tunani kadan jabir yayi sannan ya amsashi

"Oh,yeah,amma kamata yayi ka jirani mu fita tare"

"I finished bazan iya jiranka ba,saidai ka sameni a mint garden"

"Alright,ba case" ya fada yana miqewa ya nufi toilet,shi daya ne keda wannan alfarmar a wajen ja'afar din,banda shi din yasan bazai tsaya jiransa ba.

Kamar yadda yace din kuwa,ya cimmashi a mint garden cafe and bistro,saman table din shi daya ne,yana kurbar coffee din me zafi a hankali yana duban wani sashe na daban, joining dinsa jabir yin yayi,idanunsa kan fuskar ja'afar din kafin ya sauke cup din yana dubansa.

"lokaci yayi fa,daya kamata ace ka sake ajjiye wasu family din da zasu zame maka makwafin wadanda ka rasa" tsaf ja'afar ya daga kai ya kalli jabir,tsahon wasu sakanni kamar bazai amsa ba kafin yace

"Kai ka taba ganin inda GURBIN IDO ya zama idanu?" Tambayar data sanya jabir zuba masa idanu,yana hasashen irin dagar da za'a diba nan gaba kadan,shi da kansa ya qarashe amsar tambayar bayan ya miqe tsaye ya zuba hannayensa a aljihun wandonsa

"Banajin har kawo yau an haifi macen da zata mayemin gurbin shaheeda,ita kadai ce,kuma ta tafi da dukkan abinda zai burgeni daga diya mace" daga haka ya fara takawa sannu a hankali.

Tabbas jabir ya sani,ba abune mai sauqi ja'afar yaso wata diya mace ba,koda a nesa ne balle nan kusa,ko kafin shigowar shaheeda rayuwarsa,shi din ba irin mutanen nan ne da ake samun soyayyarsu da sauqi ba,bare kuma wannan babban al'amari yazo ya yiwa rayuwarsa karan tsaye.

A wajen jiran jirgin qasa me tafiya da lantarki ya sameshi,tsaye yana kallon gefensa guda,hannunsa cikin aljihun wandon nasa,duk da yaji takunsa amma bai waiwayo ba,matsawa gaba kadan yayi ya daidaita tsahonsa da nashi,kusan kansu daya,amma ja'afar din ya darashi

"Dole dole ja'afar ka dai daita rayuwarka zuwa yadda take a baya,koda komai bai dawo ba,shekaru uku ba wasa bane,kana tunanin shaheeda zataji dadin wannan halin da ka sanya kanka?,wanda ya mutu ya riga da ya mutu,bazai taba dawowa ba,indai bakayi qoqarin saita kanka ba tabbas nan da lokaci qalilan zaka ji sanarwa daura maka aure,confirm" wani kallo ya juyo ya watsawa jabir,daidai lokacin da jirgin ya tsaya,sai ya taka zuwa gaba sannan yace

"Mafaashi" qaramin murmushi jabir din yayi,sannan yabi bayansa a hankali shima yana amsa masa

"Zaka gani kuwa"

[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 20

Sannu a hankali rayuwa ke juyawa,cikin wani yanayi me dadi ga maimunatu,dukkan wani ci gaba a hankali yake samunta,ta zama cikakkiyar diya ga Dr marwan,bai taba bari an banbantata cikin duka hidimar da zaiwa iyalinsa ba,bata da matsala da kowa kasancewarta yarinya me haquri kawaici da kuma sanyin hali,zallar biyayya da kuma girmama kowa koda na qasanta ne,wannan ya siya mata soyayya sosai daga wajen iyalin gidan dr marwan,saidai a rayuwa ba kowane zai soka ba,hakanan bazaiyiwu ace kowa gudunka yake ba,cikin surukai da kuna sauran jikokin anni ba za'a rasa wadanda suke mata wani kallo na daban ba,duk da babu wanda yasan daga ina fa fito,ko kuma ita din wacece.

Babu abinda yafi mata dadi irin ilimin da take samu,batasan cewa a baya rayuwar da take rayuwa ce dake cike da zallar duhu ba sai yanzu,batasan haka ilimi yake da dadi ba sai yanzu,duk cikin abinda anni tayi mata babu abinda take jin ya mata dadi fiye da kima irin karatun da take,qoqarinta kan karatun ya ninka adadin karatun da ake mata,wannan ya sanya ake qara mata karatun da yawa,yake kuma mugun gudu,hakanan ta fannin boko,shi kansa malamin yakanyi mamaki idan yaga wasu guraren da yawa ta iyasu kafin suxo wajen,dole hakan kuma ta kasance,don kuwa duk sanda ta koma gida bita take sosai,tare da duba duk wani karatun da ya shafi wanda aka qara matan,koda yaushe baka rabata da dan qaramin dakin karatu dake gidan,wanda dr ya qirqireshi saboda yaran,su din kuma ba wani damuwa sukayi dashi ba,ba kasafai suke shiga,zuwan maimunatu da yawan shigarta wajen sai wajen ya soma rayuwa,a kullum zata tsaftaceshi,ta kuma bata lokaci a can tana nazari,daga fannin bokon har na addini.

Zuwa lokacin maimunatun ta goge sosai,a hakan ma don ba ita din ba me yawan buri ko son qyale qyale bace,sau tari idan zasu shopping ko wani abu makamancin haka bata binsu,suyita mata tsiya da kazar gida,saidai ta bisu da murmushi,ta gwammace ta zauna da amna suyita labarai,tatsuniya da sauransu,ko ta tsefe kanta ta gyara mata tayi mata kitso ko kalba,ita kanta yarinyar tunda maimunatu ta fara kula mata da kanta ta daina yarda a kaita saloon,har yanzu tana nan a bufulatanarta,bata bari ta jirkita komai nata ba baya ga suturar jiki da kuma tsaftarta data qaru.

************K'arfe uku na azahar anni ta sanyata ta shirya don rakata gidan uncle abbas qani ga dr marwan,zata duba diyarsa da bata da lafiya ita da yaron da amaryarsa ke goyo,magana tayi da maimunatu kan ta shirya tayi mata rakiya ita da tabawa,babu musu ta shirya din,karo na biyu kenan da zata fita tun zuwanta gidan,fitar farko ma hisham ne ya debesu ya kaisu wani eatery sukaci abinci saboda qarin girma da ya samu a asibitinsu,shima tun suna shirin take kallonsu,duk da sun mata tayi amma tace a'ah,zata zauna da anni,kada a barta ita kadai.

Har sun fita suka dawo sukace yaa hisham din yace ta fito suje

"Kuje kawai ku dawo ina jiranku"

"A'ah,tashi ki shirya kuje" anni tace da ita,a dole ta sauya kaya ta bisu.

Kusan daga tafiyar har dawowar a takure take,saboda yadda yace ta zauna gaban mota,suna tafe kuma yana janta da hira da 'yar tsokana,abinda ya aza mata nauyi sosai,yasa ta dinga jin kunya ta kuma gagara sakewa har suka dawo.

Bala'in nauyin hisham din takeji,saboda yadda yake mu'amalantarta ya banbanta da yadda sauran mutan gidan suke mu'amala da ita,yana da kirki sosai,yawan barkwanci musamman idan a cikin gida yake cikin family dinsa.

Tsaf ta shirya cikin doguwar rigar atamfa,sabuwa ce,cikin dinkunan da anni tasa akayi mata,ta yane kanta da madaidaicin mayafi,dankwalin yana riqe a hannuta saboda rashin sabo da daurashi

"Ma sha Allah"anni ta samu kanta da furtawa,saboda wani irin kyau da maimunatun tayi mata,tana ji a ranta ko a yanzu ja'afar ya dawo bai isa ya kushe maimunatu ba,don ta goge qwarai,ta tabbata ko a rugarsu yanzun sai sunyi mamaki idan suka ganta.

Daga ita sai annin sai amna suka tafi,drivern gidan shike tuqa su,jifa jifa suna hira da anni,hankalinta kuma na sama hanya,tana sake ganin ainihin garin na gombe,tafiyar duka duka bata wuce minti talatin ba suka isa unguwar,unguwa ce itama me kyau dake dauke da gidan masu wadata.

Maimunatu na dauke da amna suka fara takawa zuwa cikin gidan,jikokin annin uku suna biye da ita suna ta tsokanarta,saidai taqi kulasu,da alama a qule take dasu,saida sukazo qofar falon daya daga cikinsu tace

"Anni,bari na cire miki takalman"ta fada tana dariya gami da duqawa

"Ke arcan,kiyi ta kanki,ni ba take nake ba,gwandamar banza,wallahi ina tafe cikin gidan nan,duk saina bada sadakarku" ihu yammatan suka saki,namijin na musu dariya harda dafe ciki

"Eh,ba zaku saka min 'ya'ya a gaba kuna cinye tattalin arziqinsu ba,kowa ya kama gabansa mazanku da matanku" tasa kai cikin falon abinta tana sakin sallama,yayin data barsu suna ihu da dariya na tsiyar data lafta musu.

Karbar girma amaryar uncle abbas tayi musu,ta dinga nan nan da annin,da alama yar gaban goshinta ce,saida suka gama shafe wasu mintuna sannan dayar ta shigo,haj munubiya,uwar gidan uncle abbas.

Da kallo anni ta bita kafin ta dauke kai tana amsa sallamarta,ta samu waje cikin jin izza ta soma gaida anni,saidai cikin girmamawa ne,sanin cewa annin bata daukar raini sam,daga nan ta zauna ana taba hira da ita lokaci lokaci.
Chapter 28 · 0% Book details