← Book details Gurbin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 113

Sashe 74

Gurbin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Jeki cema maama ta goge miki baki da tissue,am coming"

"Zan bika dad?" Ba tare da ya gama tantance me ta fada ba ya daga mata kai,sai ta cilla tayi gida cikin tsananin murna.

Tazarar dake tsakaninsu ya sake ragewa,abinda ya sabbaba musu fara musayar numfashi,ya kafeta da dukka idanunsa yana kallon matsoraciyar fuskarta,wadda har ta runtse idanunta,zuciyarta na wani irin bugawa fiye da kima,a hankali kuma tsigar jikinta ta fara tashi,jikinta ya fara saukar mata da wani feeling saboda dumin numfashinsa dake gauraye da lallausan qamshinsa wanda ke sauka saman fuskarta,yar yar jikinta ya fara yi tako ina,wani baqon yanayi da tunda take bata taba jinsa a tattare da ita ba.

"Me yasa kika zauna haka?,kin manta ke matar aure ce?" Maganar da sam ba ita yaso yi ba ta subuce ta fita daga bakinsa da husky voice dinsa wadda ta cika kunnuwan maimunatu.

Jikinta ne gaba daya ya dauki rawa,wayar hannunta ta sulale a take ta fadi a qasa,qarar faduwar tata ya sanya idanuwansu shida ita kaiwa kan wayar,suka kuma dauke a tare suna kallon juna,sai ya tsaya kawai yana kallon kyawawan idanuwanta da suka sakeyin kyau kamar kullum a lokaci irinn wannan,idanuwan da suka dan sauya launi,suka kuma cika da qwalla,ya sanya hankalinsa sosai ga qwayar idanun nata yanason karantarta

A hankali ya zame idanuwansa daga cikin nata,ya maida qwayar idanun nasa ga jikinta yana kallonta har zuwa saman tafin qafarta,sai yaja baya ganin yadda jikinta ke dan rawa,mamaki na darsuwa a ransa,baiga wata magana da yayi da zata sanyata shiga wannan mood din ba,amma sai ya sassauta kafin fushinsa wanda baisan me yake sake hasalashi ba

"Ki dauko mayafinki ki sakemi a mota" yayi maganar yana bata hanya,tuni ta tsallake,ko takan wayar tata bata bi ba ta wuce da sauri sauri,ya bita da kallo,sai data bace ya maido dubansa ga wayar,sai ya duqa a hankali ya daukota,ya dannan gurin power ta kawo haske.

Face dinta dake cike da cuteness ce ta cuka screen na wayar,cikin uniform dinta na makaranta,lafiyayyen murmushi ne kwance akan fuskar tata daya qara mata wani kyau na musamman,duk da screen din wayar ya fashe amma hakan bai hana bayyanuwar kyan hoton ba,samun kanshi yayi da kallon hoton na wasu sakanni,sannan ya kashe hasken wayar,ya sanyata a aljihunsa yana miqewa,a kasalance yabi ta qofar baya ba tare da ya koma ta cikin gidan ba ya fice parking lot na gidan.

Toilet ta fara shigewa ta maida qofan ta rufe,numfashi take ajewa gami da cure hannayenta waje daya,tanason ta gama tantance abinda ke damunta tukunna,tsahon minti biyu kafin bugun zuciyarta ya dai daita,hawayenta kuma suka tsaya,saidai abinda takeji cikin jikinta bai sauya ba,famfo ta kunna,ta tara hannayenta ta wanke fuskarta da kyau ta gyarata sannan ta fito,tana takawa a hankali cikin sake daidaita nutsuwarta don kada yanayinta ya nuna wani abu.

Ranta fal haushinsa,me tayi haka da zai sanyata a kwana yana mata irin wannan tambayar?,ya kuma rutsata da idanuwansan nan data tsani ya kalleta dasu,tana cewa dukkansu a haka suke zaune kamar ita?,meye tayi wanda ba dai dai ba?,ko wani tafi a cikinsu?,don kawai tana da aurensa?.

Laila fa'iza rahama da sahla 'yar anty maama ne sukayo mata rakiya,sai amna dake riqe da hannun maimunatu wadda ta kafe kai da fata yau fa a wajen anty moon zata kwana.

Daga dan baya kadan dukka suka tsaya,saboda kowannensu shakkarsa yake,ta qarasa ta sanya hannu ta bude qofar,tana addu'ar Allah yasa ba'a bayan yake ba,gaba daya batason haduwar sabgarta da tashi sam,saidai yana zaune a owners corner,hannunsa dauke da ragowar ruwan daya dauko a hanyan kitchen kafin ya fito.

Tana shiga amna ta shigo tana fadin

"Daddy.....tare zamu tafiko?" Ta wuce kai tsaye kusa dashi,duban maimunatu yayi,bata yarda sun hada ido ba,sai kuma ya maida kallonsa ga amnan

"Ban miki bayani ba?,ba yau zamu tafi ba,I have prepared something for you soon" kafada ta maqale,idanunta na hada ruwan hawaye

"Nooo daddy....,nafison na bika yanzu" yadda ta narke din sai ta bashi tausayi matuqa,tana yawan son ta bishi,amma kuma sai yake ganin kamar ba zata samu kulawa irin tasu amma ba.

"Let's go"
"Yeeyy..... that's my dad" dolensa tasa murmushi kubce masa,sai yasa hannu ya lakaci kumatunta

"That's my baby" shima ya mayar mata.murmushin da bata shirya ba mai dan sauti ya kubce mata,fitar sautin sa ya sanyashi waiwayowa ya dubeta,sai kuma ta maze,kamar ba ita ba,ta maida idanunta da hankalinta sosai ga titi.

Bata sake tabbatar da surutu da kuma wayon amna ba sai da suka dauki hanya,hakanan ya daure ya dinga biye mata a wasu maganganun nata,itakam farinciki ya cikata,yau zata kwana a wajen daddynta.

Shuru maimunatu tayi tana saurarensu,a hankali taji kewa sosai na cikata,kewa ta mahaifi,tana iya tuna wasu abubuwa da suka faru tsakaninta dashi,gata da soyayyar da yake gwada mata a wancan lokacin,bata manta wasu ba duk da shekaru sun fara nisa,gefe guda kuma tana bin yadda jikinta keta motsawa, mood dinta yana dan canzawa kadan kadan,wanda ita kanta batasan dalili ba,wannan yasa motsinta ya dauke kwata kwata daga cikin motar,har sai da amna tace

"Anty moon,zaki dafamin pepper chicken?" Murmushi ta sauke tana duban fuskarta,har cikin ranta take jin tausayin yarinyar data rasa yar uwarta dama mahaifiyarta tun batasan rayuwa da dadinta ba

"Komai ma kikeso amna....zaki samu" juyi tayi.najin dadi

"Bazan sanwa khadim ba,saboda ya cinyemin wanda amma tasa raliya tayimin jiya,nayita kuka"

"Zan sake miki wani" Allah ya taimaketa hirar ta sake komawa tsakaninta da daddyn nata.

A hankali motarsu ta sanya kai cikin gidan,a lokacin yammaci sosai ya qara yi,qeme me amna taqi takawa da kanta,ta noqe kafada

"Daddy ka daukeni" sai ya sunkuya a hankali ya azata saman kafadarsa,cikin jin dadi kuwa ta saki dariya tana kwantar da kanta saman kafadarsa tana ci gaba da dariya.

Ta rigasu yin gaba,ta buda sashen nata ta shige,kafin ta maida qofar sai gashi sun iso shi da ita,ya duqa a qasa a hankali yana fadin

"Get down" tsalle tayo ta sauka tana dariya ya juya yana fita gami da cewa

"Am tired amnee,let me rest for a while,i will get back to you"

"Okay dad,rest well,am waiting for" qaramin murmushi ya kuma saki na gefan baki,daga tahowarsu tare zuwa yanzu tana ta debe masa kewa tare da rage masa tamper dake ransa,ya yadda ya kuma sake tabbatarwa nisanta da tayi a rayuwarsa bau qareshi da komai ba sai qarin qunci da takura,sai ya samu kansa da tunanin yadda zai dawo da ita kusa dashi kamar haka,ko babu komai he will get some one who will take away his loneliness.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 56

Dakinta suka wuce da amnan,ta ajjie lafayanta jaka da kuma takalminta,sannan ta sauya kayan jikinta zuwa wata doguwar riga

"Me zamu dafa amnee?" Murmushi tana fidda ido

"Kema irin na daddy?" Gira ta dage mata tana murmushi

"Eh yafi dadi ai" sai yarinyar ta saki dariya

"Nima nafi son shi"

"Yeah,me zamu dafa?" Dan daga idanunta tayi kadan

"Ummmm,daddy's favorite" ta fada da sauri bayan ta gama tunaninta

"Me kenan?" Maimunatu ta tambyeta tana dubanta

"Sinasir funkaso or masa" ido ta zaro

"It's late but I'll cook it later,i promise"

"Yayi anty moon,i like it nima"

"Zan miki in sha Allah amnen daddy" ta fada tana jan kumatunta.

Tare suka wuce kitchen din da ita,tana aikinta ita kuma tana mata labari,tana ta biye mata,sai taji aikin yayi mata sauri,hakanan ranta fes,babu tunane tunane ko kuma jin kewa.

Soyayyiyar taliya tayi musu data wadata da kayan lambu,duk da haka kuma sai ta hada potato salad,sai kuma farfesun kifi ragon ruwa me kyau,wanda shima yaji kayan qamshi,kamar zata hada lemo taga aikin zai mata yawa,ga magrib an idar bata kuma samu ta sauke farali ba,don haka ta tattara komai takai saman dining,ta kuma gyare kitchen din,amna nata nacin ta bata ko mopping tayi mata amma ta hana,koda ta gama din tare suka wuce daki, maimunatu ta tube ta shiga wanka,bayan ta fito ta shirya cikin wasu white and soft fabric,skirt ne handkerchief style sai shirt off shoulder, design na rigar ya baiwa fararen kafadunta dake qyalli daman fitowa sosai,suka kuma fidda kyansu da kuma sigarsu,hakanan albarkatun qirjinta suka zauna daram daga qasan rigar,saidai ko yaya tayi sunkuyo za'a iya ganinsu saboda yanayin rigar,kayan sun mata kyau sun kuma amsheta,abinda ya bata sha'awa ta sanyasu ganin basu da nauyi ta kuma ji dadinsu a jiki.

Sai data yima anan wanka itama sannan sukayi sallah,suka fito cin abinci,hannun maimunatu ta kama ta riqe sanda take shirin serving nata

"Anty moon,daddy fa?" Kai ta daga a dubeta

"Me ya faru dashi?" Narkewa tayi tana duban qwayar idanunta

"Zaici abincin,yanason kifi" nauyi yadan kamata,to amma kuma jagwal zata ja mata,don ita bata shirya komai dashi ba,bata kuma shirya ganinsa ba bare ga tsareta da wannan kallon nata ya dagula mata lissafi ba

"Kinga baya nan ai,kuma baice yana jin yunwa ba"

"Please anty,zai dawo fa,he promised,kuma daddy na baya saba alqawari,Allah anty na tabbatar zaici,he like it" yadda ta riqe mata hannu ta kuma marairaice mata dole ta ajjiye serving spoo din tana sauke ajiyar zuciya,nan suka zauna jiransa,duk bayan mintuna sai amnan ta duba qofa,maimunatu ta biye mata ne kawai,amma ita ta sani ba shigowa zaiyi ba,tunda ba shigowar yakeyi ba,sai ta kunna musu mbc three daga nan saman dining din da suke ko zata ragewa yarinyar zaman jira.

A tashinta na karo babu adadi sai amnan ta fice ba tare da maimunatu ta lura ba,kanta tsaye ta haye stairs na ja'afar tana sauri sauri,ta wuce balcony ta tura qofar falon da sallama abakinta tana leqe leqe.

Yana tsaye gaban tv yana sauya tasha,bayan ya cika dakin da sanyin ac kaman babu gobe,hannunsa daga dauke da cup na black tea,yana sha yana tunanin abinda zaiyi order wanda zai dace da yanayinsa,yayu matuqar kewar tafiyar da baaba tabawa tayi.

Da mamaki a fuskarsa ya waiwayo yana dubanta,sai yadan sakar mata murmushi,ita kuma ta tsaya daga bakin qofar tana maqale wuya

"Daddy,your dinner is ready" idanu ya fitar alamun mamaki

"Who prepared it for me?"

"Anty moon ce,ka taho daddy please,munata jiranka tun daxun"

"Amneee.....zo kiji" ya fada yana ajiye cup din gami da yafitota,kafada ta maqale
Chapter 74 · 0% Book details