← Book details Gurbin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 113

Sashe 6

Gurbin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yuuma.....yuuma.....warnano wakka haala kawela(zo kiji wani mummunan labari)" ta fara qwalawa yuuma dake xaune qofar dakinta kiran,abinda ya sanya himu zubawa innar idanu cike da mamakin meye ya gigita innar tasa haka?,har take irin wannan kiran?.

"Ku tashi ku fita" innar ta fada tana waiwayawa gasu safiya dake zaune tun dazu suna kallon kallon a tsakaninsu,tsam suka miqe suna masu ficewa kowacce bakinga fal da magana,dai dai sanda yuuma ta shigo dakin a rude

"Lafiya kuwa?" Ta tambayi inna tana laluben wajen zama hankalinta a tashe,sai da inna taja wani dogon numfashi mai nauyi ta furzar da iska sannan tace

"Yaron nan ne yakeson dauko mana jaraba rana tsaka" sake tashi hankalin yuuma yayi tana duba inna tace

"Subhanallahi,jaraba wacce iri?" Kai inna ta gyada cike da jin xafi tace

"Wai yarinyar nan maimunatu ya gani yakeso?"

"Maimunatu?....maimunatu?" Yuuma ta maimaita sunan tana son tuna aka wace ake magana

"Diyam ta gidansu laulo" take yuuma ta fahimta,sunan kuma ya fado mata a rai,saboda ita daya keda sunan kaf rugar,hakanan kuma mahaifiyarta kadai ke kiranta da sunan,sai ta sauke ajiyar zuciya,alamun tashin hakalin da ya taso tun daga zuciya zuwa fuskarta ya fara zagwanyewa

"Hankalina ya tashi sosai innar sadam,na dauka wani abun tashin hankalinne"

"Yo akwai tashin hankalin da yafi wannan yuuma?""ai abinda yasa nace haka innar laulo.....kaf fadin rugarnan anyi ittifaqi babu yarinyar dake da nutsuwa da kuma kamun kai da tarbiyya irin maimunatu....."

"Amma kinfi kowa sanin ainihin wacece ita ko?"

"Wannan duk camfi ne ko ince hasashe....duk cikin masu hasashen babu wanda yake da tabbas kan abinda yake fada koda kuwa a gaban Allah ne,dukka abinda al'umar rugar nan keyi ba komai bane illa jahilci zalla da kima gurguwar fahimta gami da mummunan zato,koda ba zato bane hakanne,babu wanda ya taba kama maimunatu da wani mummunan aibu da za'a qita,a karan kanta maimunatu bata da wata matsala ko illa....." Idanu inna ta zubawa yuuma,a hankali a kuma sanyaye tace

"Yuuma...kodai don bake kika haifi himu ba kike qoqarin wanke maimunatu gami da kore kowanne aibu daga gareta?" Ba yuuma kawai ba,hatta da ibrahim sai da maganar ta tabashi,qas yayi da kanshi yana jin babu dadi a ransa,yayin da yuuma ta rintse idanu,maganar tana sauka saman zuciyarta da wani irin dafi mai zafi,dai dai maganar take da saukar mashi saman zuciyar tata,duk yadda take zaman kawaici da innar laulon....bata taba gwaba mata magana me zafi akan yaranta ba irin wannan

"Kaico!....kaico!" Yuuma ta fada tana girgiza kanta

"Inama ace Allah ya bani d'a na cikina wanda yakai shekarun ibrahim....kai koda ace bai qarasashi ba,matuqar ya isa a daura aurensa,da ba shakka na tabbatar miki da cewa magana nake Miki da zuciya daya.....Allah ya kyauta,kiyi haquri bisa shishshigin da nayi miki" yuuma ta fada bayan ta yunqura ta miqe,zuciyarta na wani irin tafasa,wanda tana fita qofar dakin hawaye ya silalo mata.

Shuru ne ya ratsa dakin na wucin gadi,cikin ranta innar laulo tana jin kamar bata kyauta ba,wata zuciyar kuma na gaya mata daidai ne abinda tayin,zallar mugunta ce kawai tasa yuuman bada wannan shawarar a gaban himun,bayan tasan kowa gudu da qyamar yarinyar yakeyi,ko ita bata sake ganinta tana hulda da yarinyar ba

"Amma inna abinda kika yiwa....."
"Kaga dakatamin" inna ta tsaida ibrahim dake Shirin nuna mata rashin dacewar abinda tayin

"Kada kace min komai,maganar maimunatu kada na sake jinta a bakinka,domin kuwa ba kai ba,koda wanda na isa na gaya masa yaji ne bazan bari ya aureta ba,bare kai dan cikina,bama maimunatu ba,banason ka sake kawomin maganar kowacce yarinya,na riga na zabar maka matar aure tun shekarun baya.....kaje gidansu maimunatun ka nemi gaje ku dai daita".

Tsaf kwanyarsa fa birkice,ta yaya zaizo da maganar maimunatu inna ta umarceshi da auren gaje?,gaje dai da ya sani?,ya akayi suka zama 'yan gida daya ita da maimunatun?,babu kama ta siffa ko dabi'a ko qanqani a tsakaninsu,wanne aibu ne ma wai da innar ke magana a kai da har zai zama hujjar raba sabuwar tarayyar da yanzu aka fara kiwonta tsakaninsa da maimunatu?.

*FREE PAGES ZASU KARE NE ZUWA GOBE IN SHA ALLAH,ZAKI IYA BIYAN KUDINKI TA WADAN NAN HANYOYIN*

Hafsat umar kabir
2270637070
Zenith bank

*Saiki tura shaidar biya ta nan*
07040727902

*Idan katin mtn ne kuma zaki tura ta nan tare sa shaidar biya*

09134848107

*Thanks for choosing zafafa biyar*

*_GURBIN IDO_*
*LAST FREE PAGE 05*

*AREWA BOOKS::HUGUMA*

Cikin kwanakin da suka biyo baya gaba daya kusan rabi da rabi na dawowar maimuntu daga kiwon ibrahim ne,wasu lokutan yakanyi gaba wani lokaci kuma tana biye dashi a baya,har sukai gida,ya tayata daure na daurewa ko sharar wajen idan bata samu tayi ba,sudan taba hira sannan ya wuce zuwa gida. Duk da cewa fiye da rabin hirar shi kadai yake abarsa,na maimunatun baya wuce eh ko a'ah. Haka kawai fa tsinci kanta da jin dadin tarayyarsu ita dashi,sai takejin wani canji na zuwa ma zuciya da rayuwarta,gaba daya wannan kadaicin babu shi,tana jin kamar ta samu wani bango da zata raba ko ta jingina dashi ko yaya yake,sabanin daa da bata da wanda zai magana da ita,magana da ake kirame dadi,idan taji magana daga bakin wani to fada ne,idan taji hira akanta to ta tsangwama ce,wani lokaci takan jima kwance duk sanda taje bacci,tana tuno irin hirarrkinsu da ibrahim,wani abun takan saki murmushi ne ta kuma juya ta gyara kwanciyarta.

Ta bangaren ibrahim din wani matsayi na musamman yakeji maimunatu na sake damu cikin ruhi da zuciyarsa,a dan zamansu ya fahimci abubuwa masu tarin yawa tattare da ita,ta banbanta qwarai da duka yaran rugar tasu,tana da wata irin nutsuwa da fasahar magana wadda ya jima baiga irinta jikin wata 'ya mace ba,komai nata na hankali ne da sanin ya kamata,yakan zauna yana kallon yadd take iya controlling dabbobinta da baki kawai ta hanyar basu umarni,lokaci dai daiku ne takanyi amfani da sandarta wanda xaiyi wuya ma kaga hakan.

Yadda take tausayin dabbobin kamar 'yan adam,bayan dukka alamu sun nuna sun fita samun gata da kulawa,duk da har yanzu bata taba bude baki tayi masa wata magana data shafi gidansu ba,yadda take communicating dasu kawai abun burgewa ne,duk da shima cikakken bafullace ne amma ba kasafai yake ganin hakan ba,lokuta da dama idan ya tsokanetan saidai tayi murmushi kawai,wanda kusan wannan din dabi'arta ne.

Ko sau daya himu baiyi nufin zuwa ga gaje ba kamar yadda daada ta buqata,wani lokaci ma sai ya rako maimunatu yake tunawa da batun,saidai yana ganin ba abu bane mai yiwuwa,yana da tabbacin komai zai daidaita da zarar bappansa ya dawo,wanda ya qara kwanaki kan wadanda yace zai dawo,saboda jiran haduwar kudadensa dake hannun mutane.

**************Yammacine lis,wanda yake busa wata ni'imtacciyar iska me dadi,yanayi ne da ya yiwa halittu da dama dadi,bawai ga dan adam kawai ba,hatta da sauran tsirrai da kuma dabbobin daketa kai kawo suna kiwo a farfajiyar wajen da ya zame musu wajen yini.

Daga can qasan bishiyar idan kakai kallonka wajen,bafullatana maimunatu ce cikin baqin saqinta,zaune saman koren hiramin da himu ya shimfida mata,shi kuma yana zaune daga gefanta saman wani dan mulmulallen dutse da bai cika girma ba.

Murmushine ke fita daga saman fuskarta,murmushin da kana kallonsa kasan kunyace cike dashi,ko a iya zamanta idan ka.kalla da kyau kasan a takure take,hannayenta sarqafe cikin juna tana kallonsu,yayin da shi kuma ibrahim ya zuba mata dukka idanunsa yana jiran amsar tambayar daya jefa mata.

Wani irin nauyi ibrahim din ke aza mata duk lokacin da ya zaunar da ita irin haka yana karanta mata kalaman soyayya......daga qarshe kuma a yau din ya tirketa kan lallai sai ta furta masa da bakinta tana sonshi,saboda bai taba jin hakan daga bakinta ba.

Wani abune kuma ita din da bata jin zata iya gaya masan,kalma ce data ji ta girmi kanta matuqa,koda baya kallonta ba zata iya fada ba,bare yadda yake zaune yana kallonta.

,sirara kuma jajayen labbanta ta motsa a hankali

"midelli...yamma tayi" dauke idanunsa yayi daga kanta yana murmushi,duk da yasan yau din sun gota lokacin komawarsun,amma tayi hakanne don ta kaucewa tambayarsa,yana mamakin kunya irin tata kawaici da kuma kamewa,sai ya miqe kawai ya dauki sandarta da a yanzun shike amfani da ita idan zasu koma gida.

Kamar ko yaushe ya tayata suka kammala komai,yayi tsaye daga jikin wata rusashiyar bukka dake daura da wajen yana dubanta cikin murmushi

"Shikenan,tunda ba zaki bani amsa ba maimunatu zan tafi,sai jaaango?" A kunyace tayi murmushi tana kauda kanta gefe daya,ya sauke qafarsa da ya harde waje daya ya fara takawa a hankali yana barin wajen

"Ka gaida gida" ta fada cikin siririyar muryarta da ba kasafai ya fiya jinta ba,sai daya waiwayo cikin jin dadi ya kalleta yana jinjina kai sannan yaci gaba da takawa,hakanan taji kunya ta kamata,abinda yasa ta juya da sauri da nufin shigewa zuwa shiyyar da dakunansu suke. Saidai kuma cak ta tsaya,saboda ganin inna tsaye daura da ita,da alama taji komai ta kuma ga komai.

Kallon da innar kawai ta tsareta dashi ya sanyaya mata gwiwa ya kuma sanya mata fargaba me tarin yawa,gabanta ya fara faduwa da wani mugun qarfi,duk da haka ta ari dakiya taci gaba da nufar inda innar ke tsaye tana ci gaba da kallonta

"Immoi'onni?(waye wancan?)"innar ta fada a tsawace cike da tuhuma da kuma zargi,yanayin yadda tayi mata maganar ya jefa tsoro a zuciyar maimunatun,ta qanqame jikinta waje guda,tana jiran jin saukae duka daga wajen innar,don wannan din ba sabon abu bane a wajenta

"Tambayarki nakeyi waye wancan din?"

"Sunansa ibrahim.....ya tayani qaraso da dabbobi gida ne"

"Meye hadinki dashi?" Inna ta sake tsareta da tambaya,saboda zargin da ya shiga ranta,taso taha fuskarsa amma kuma haqarta bata cimma ruwa ba,saidai batajin wanda take tunani dinne,don bata da shakka akan alqawari da yarjejeniyar dake tsakaninsu

"Babu komai" ta amsawa innar kanta a qasa,tana matse hannayenta waje guda,tana jin yadda zuciyarta ke ci gaba da bugawa fat fat
Chapter 6 · 0% Book details