← Book details Gurbin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 113

Sashe 113

Gurbin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

"Banson wata kunya malama,johannesburg tana da kima da babban tarihi a rayuwarta,ki shirya bayan amnee ta gama exams dinta,za'a dauran auren gaaje da himu,na gama magana dashi tun ina can ya kuma amince,zamu wuce umra gaba daya da yara,harda baaba tabawa,daga can zasu dawo gida,mu kuma zamu sauka johannesburg,inason na sake dasa wasu 'yan biyun a can" juyowa tayi tana qanqame shi,dadi yana cikata kamar yaune zuwanta umara na farko,saidai shi din wajene da dukka musulmi,gefe guda farincikin yadda burinta ya cika,himu ya yarda zai auri gaaje,ta tabbatar har yanzu gaaje nason himu,saidai tana ganin kamar ya mata nisa,sai gashi cikin haquri dattako da kyawun hali nasa ya amince zai auretan duk da abubuwan da suka biyo baya.

Hannuwansa dukka biyun ta riqe,tana sake jin duk duniya babu macen data kaita sa'ar miji,addu'o'i ta dinga jero masa,wanda ta kasa yankesu har sai da ya hade bakinsu waje daya,bada gangan yayi ba amma sai gashi sun sake rikita juna saida suka koma ruwa,sannan suka dawo suka sake sabon shiri,ita ta shirya shi tsaf da kayan da suka kasance zabinta kamar tadda ta saba masa,ta zauna a gefansa ta ci dashi ya qoshi,sannan suka fito.

Wani irin perfect match couples wanda duk wanda ya kallesu sai ya sake waiwayowa ya kallesu,saboda zallar dacewa da juna da kulawa da kuma soyayya dake fita daga idanun kowa zuwa ga dan uwansa,wani lokaci ba tare da sunsan suna aikata hakan bama,haka suka dauki yaran nasu,sunata hirarraki a tsakaninsu,hira dake nuna fahimtar juna da qaunar juna a tsakaninsu,asim nata murna zaije ya tsokani anni,ya boye dan qaramin qadangaren wasaya radawa asad a kunnensa

"Yau anni zatayi ta kanta,saina tsoratata,ladan tallemin qeya data yi rannan" karaf a kunnen maimunatu,ta waiwayo ta watsa masa daquwa

"Akul dinka da tabamin uwa,ranka zai baci,zakayi ta kanka ne indai naji labarin hakan ya faru" dariya suka sanya gaba daya,dukkansu suna qaunar tsohuwar,har yanzu rigimar nan tata tana nan,saidai kuma tana tsananin son jikokin nata,musamman ace an hadu gaba daya,yaran hisham salma laila safina da fa'iza,ranar bata da katabus sai nasu.

A motar kuma hirar sai ta koma ta anty amna,asad da as'ad nata hirar graduation party da suka shiryama amnan ba tare da amnan ta sani ba,ko maimunatu ma sai lokacin takeji, murmushi kawai ta saka tana jin dadin yadda Allah ya hade kawunansu,babu wanda zaice ba ita ta haifi amna ba,captain ja'afar kuwa hannunta ya lalubo kawai ya sanya cikin nashi,yasan ko mene yaran suka zama qoqari da jajircewarta ce,soyayyar data gwadama amanan tsahon shekarun da suke tare ko mahaifiyarta sai haka,yana alfahari da maimunatu matuqa a rayuwarsa,tayi masa komai,ta kuma zame masa dukkan abinda yakeson matarsa ta zama,tana kan zama din ma.

*Tammat bi hamdillah*

*A nan na kawo qarshen labarina mai suna GURBIN IDO,ina fata Allah yasa al'umma sun amfana,kura kuran ciki Allah ya yafe mana,ya bamu ladan ciki,abinda muka manta kuma bamu rufe dashi ba sai ayi mana afuwa,ajizanci ne*

*Masoya masu siyan litattafan mu a koda yaushe,bawai don baku da inda zaku samu ba,mun gode qwarai da gaske,ubangiji ya yalwata arziqinku,ya bar zumunci a tsakaninmu,muna matuqar godiya a gareku,haqurin da kuke damu Allah ya saka muku da alkhairinsa,Allah ya sadamu da alkhairin sa*

*ZAFAFA BIYAR NA MATUQAR GODIYA DA JINJINA A GAREKU*

*Subhanakallahumma wabi hamdika,ash hadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa'atubu ilaika*
Chapter 113 · 0% Book details