← Book details Gurbin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 113

Sashe 105

Gurbin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abinda bai sani ba tuni hawayen ya diga saman fuskartata,yana shirin miqewa ta bude idanuwan nata wadanda suka qara kyau da kuma haske,ta dubeshi cikin yanayi na masu barci,bakinta ya motsa kadan alamun magana zatayi,sai ta dawo gefanta ya zauna fuskarsa na fidda murmushi,ya taimaka mata ta zauna sosai ya jingina mata bayanta da filo

"Congratulations angel moon" binsa tayi da kallo kawai ba tare dafa fuskanci komai ba,a tausashe ya rungumeta cikin jikinsa yana jin yadda take sake mamaye rayuwarsa da duniyarsa gaba daya,hannunsa ya dora a hankali yana shafar cikinta

"Kina dauke da juna biyun ja'afar marwan khalid akko,zaki haifawa anni d'a,zaki haifawa amma jika,zaki kuma kuma haifawa amneee 'yan uwa" mamamki ya kamata ta kasa cewa komai,jin shuru saiya daga kansa yana duban qwayoyin idanunta dake nuna tsoro,tsoron nan dake burgeshi

"Are you happy?" Qwalla ce ta subuce mata hade da murmushi,saita kifa kanta a kafadarsa tana jin kunyarsa,wai ciki?,ciki ita din?,yanzu kowa zai san abinda suke aikatawa ita dashi a boye kenan?,tunda ga ciki ya fito?.

Sosai ya dinga tsokanarta,tare da.lasafta mata burikansa akan cikin,burikan nasa masu yawa ne,har ta gaji da tayashi lissafawa,sun jima a jikin juna suna wata irin hira dake haifar da sabuwar soyayya da kuma shaquwa ta musamman,idan tayi magana sai yace dumin babynsa yakeji,babyn da ko gama sanin lokacin shigarsa da kuma adadin zamansa ba'ayi ba.

Sanda ya dauki waya yana niyyar kiran anni cewa tayi

"Don Allah hubby......kada ka gaya musu" dubanta yayi yana murmushi

"Why?"

"Kunya nakeji Allah"

"Kunyar me?" Cikin sakalcin dan fari da da wautar auta ta daga kai

"Kowa sai yasan me mukayi na samu ciki kenan fa?,Allah bazan iya sake kallon kowa ba" dariya irin wadda takan jima bataga yayi irinta ba ya saki,ya zame wayar gefe ya riqeta da kyau,ita kuma ta tura baki gaba kamar zata saki kuka,don kukan kamar baya mata wuya

"Ni baba tabawa zan kira a aiko,saboda banason ki sake komai,amma kuma kinsan halin anni,indai ta tsokaneni saina rama" kamar wasa sai ta sake masa kuka,yana tsokanarta ya dauka wasa ne sai yaga kukan take da gaske,sanyata yayi cikin jikinsa sosai,ya fara gaya mata wasu sanyayan kalamai,a hankali tayi shuru tana sauke ajiyar zuciya,zuciyarta tana yin sanyi,shima ajiyar zuciyar ya sauke, yaushe ta koyi rigima irin haka?.

Bugu biyu anni ta dauki wayar,abu na farko data fara fada shine

"Kai nake shirin kira yanzu,kai kaje ka sace musu yarinya cikin dare?" Sam sam ya mance daukota yayi ma daga gidan,ba wanda ya sani sai guard guda daya

"Sata ce wannan anni?,matata na dauko na gaji da kawaici,ko tausayina na lura anni bakiyi gaba daya"

"Kai ja'afaru ka fita idanuna......kayi ta kanka wallahi"

"Zanyi ta kaina......amma kafin sannan,ki turo baaba tabawa please ta kula da ita,bata da lafiya" wani farinciki ya kama zuciyar anni, ja'afar dinsu daya daina amsa kowa ya daina hurda da maida amsar magana yau shine ake kai ruwa rana dashi akan matarsa,tun baice komai ba jikinta ya bata mawuyacine a wannan karon idan ba abinda taketa addu'a bane ya samu

"Ahaf,wato daga daukota harka hadata da jinya ko?"

"Ba jinyar kikeso tayi ba?,ko bansha jinki kina roqa mata ita ba?" Idanu ta fiddo

"Kai ja'afaru,ni zaka yiwa sharri?....." Sai kuma tayi shuru data tuna randa tayi addu'ar,a take farincikinta ya ninka,ta kashe wayar da kanta tun bai kashe ba,ta kuma tashi da kanta ta shiga kitchen kiran baba tabawa,wadda tana ganin annin tasan kiran mai muhimmanci ne,don ba shiga kitchen din take ba.

"Matar manya ce babu lafiya,zaki je ki zauna da ita......don Allah tabawa kiwa Allah kiwa ma'aiki ki kula da yarinyar nan da kyau,kada kice zaki yiwa manya kaara,basu da kunya ko kadan yaran wannan qarnin,ki kula da ita da kyau,kada wata matsalar ta afku a rasa cikin nan" guda baba tabawa ta saki,wadda ta jawo hankalinsu laila safina da salma dake falon annin suna hada wata game

"Alhamdulillahi, alhamdulillahi,Allah mun gode maka,ai zama bai kamani ba,Allah dai ya raba lafiya" take tahau shirin tafiya anni tasa aka yiwa driver magana.

Cikin lokaci qanqani labarin cikin ya karade gidan,wani irin murna da farinciki suka tsinci kawunansu,amma na falon abbi tana gyara masa laila ta sameta a can tana labarta mata,saita saki duster din da take goge kayan kallon falon,ta sulale ta zauna tana ambatar

"Allah na gode maka,Allah na gode maka" sai kuma hawaye ya biyo baya,ta debe tsammanin samuwar ja'afar din a nan kusa,sai kuma gashi bayan daidaituwar al'amuransa harda tagomashi na samun qaruwa.

Abbi dake daura links din hannunsa ne ya fito,yaji dukka abinda.laila tace,gaidashi laila tayi ta juya ta fice,shi kuma ya isa wajen amman,ya zauna a hannun kujerar da take zaune a kai,cikin kulawa ya fara mata magana

"Ci gaba zamuyi da godewa Allah da yawaita sadaqa,ubangiji ya sake tabbatar da dukka alkhairinsa a tarayyarsu" yayi maganar shi kansa farinciki yana ratsa zuciyarsa,kai ta jinjina tana share hawayenta

"Babu abinda zamuce da anni saidai Allah yasa ta gama da duniya lafiya,kaf rayuwarmu da alkhairi take binta,ko yaushe tunaninta yadda zata inganta rayuwar family dinta" kai ya jinjina yana jin dadin yadda ko yaushe tana gaba gaba wajen fadin alkhairin mahaifiyarsa gami da yi mata addu'a

"Ameen ameen" ya amsata sannan ya miqe,cikin salon tsokana kuma yace

"Ashe dai aishatu anason samun sabbin jikoki,wannan kuka haka?, ja'afar din dai shine na gaban goshin dai,ya kamata anni taji wannan labarin" kunya ce ta kamata sosai,saitayi qasa da kanta tana goge hawayen da batasan sun zubo ba

"Ayi haquri yallabai,kada na kasa hada ido da anni" ta fada tana miqewa don yi masa rakiya.

Tun ranar da baaba tabawa ta tafi gidan ta koma 'yar kallo,hakanan ta dinga kame kanta waje daya,saboda gaba daya ja'afar din ya kunce mata tunani,ashe haka yake?,ashe lumbu lumbu ne?,wata irin wutar soyayya ke tashi cikin gidan,saidai cikin salo da ban sha'awa da kuma qayatarwa,ya dauki kulawar maimunatu gaba daya ya aza a wuyansa,abinda baaba tabawa kawai keyi kula da gidan da kuma girki.

Ta fannin maimunatu kuwa sai yanzu tasan meye ainihin ma'anar gata,gata mai sunan gata,tako ina lelenta akeyi,umma sa'adah nayi,su fareeda cousins dinta sunayi,anni nayi ammi da amma nayi,tsohuwa hajja nayi,umma sa'adah nayi,abbanta nayi,ga kuma afrah dinta data qeqashe taqi komawa makaranta,sai day abbuu ya maidata,wanda a yanzun itama ta koma ce masa abbuu,ya samu cikakkiyar lafiya ya kuma koma kan ayyukansa kamar daa,ya murmure fes dashi kamar babu wata jarrabawa data taba samunsa,a yanzun abu daya ya ragewa hajja shine ya qara aure,shi kuwa gani yake bazai samu mace kamar hauwa'u da shatunsa ba.

Ko yaya maimunatu ta motsa sai a kawo mata caffa,tako.ina gata da kulawa take samu,hatta su laila kaman zaayi musu haihuwar jikan fari,kusan ranaku d'ai d'aikune basa zuwan mata a yini ana hira,haka afrah itama fashin kwana daya ko biyu take,ba abinda maimunatu keyi saidai taci abinda ranta keso tasha abinda ranta keso,duk da cikin yazo mata da laulayi sosai,amma tana samun sauqi saboda akwai masu debe mata kewa.

Saidai fa duk yadda gidan yakai ga mutane,da zarar oga captain ja'afar ya dawo zai dauke abarsa ya wuce sassansa da ita,hidimarta kuma ta koma wuyansa,ita kanta maimunatu qorafi take masa ya dinga hutawa yaji da aikin office kawai amma yakance

"Da da hali zan ajjiye komai ne,nayita rainon cikin nan har sai randa kika haihu zan sake fita na barki" idan kun sake ganin maimunatu yana cikin gidan saidai idan wata muhimmiyar fita ce ta kamashi.

Tako ta ina babu abinda zata cewa rayuwa sai godiyar Allah,cikin dare daya Allah Almusawwiru ya canza mata rayuwarta gaba daya,bata da wani sauran qunci ko kuma damuwa kwata kwata,saidai lokaci lokaci takanyi tunanin inna furera,ko yaya take ciki?,me takeyi a halin yanzu,da gaske bata sonta don bata taba waiwayar inda take ba.

Abinda bata sani ba shine,inna fureran ta hadu da ibtila'i,bata da lafiya ta fita wani private asibiti da aka bude jikin rugarsu,bayan ta gama fadi tashin neman adreshin maimunatu har gembu amma kowa ya hanata,daga bisani kuma ta samu adress din,saidai har garin gombe ta shigo amma ta bace,tayita yawon neman gidan bata samu ba,qarshe ta hadu da 'yan damfara suka karbe sauran 'yan kudadenta,sai bara tayi ta hado kudin motar dawowa gida.bayan taje asibitin an gama dubata likitan yace

"Akwai wani aiki da mukeson bawa.mutane,aiki ne da yanzu yanzu zaki zama.shahararriyar attajira idan kinso" a yanzu ba abinda inna furera keso kamar wannan kalmar ta zata zama me kudi, kowacce hanyace tana jin zata iya binta,don haka tace

"Ko meye likita zanyi,zanyi wlh"

"Ba wani abu bane mai wahala,jini zamu diba leda biyu,zamu biyaki naira miliyan talatin" jin yawan kudin ya sanyata zamowa qasa,sai gata dabas zaune a qasa tana raba idanu,fillo yaji kudi sama ta ka ba tare daya siyar da kasanarsa ba😝😝😜

"Shin da gaske kake likkita?"

"Hajiya ba wasa a maganar nan,jinin muna kaiwa ana taimakawa marasa qarfi a cikin gari,saboda ku fulani kun fisu lafiya da yawan jini saboda yanayin abincinku da nasu ba daya bane"

"Aradu likkita ko yanzu ina iya kwanciya ka diba" ta fada jikinta na mazari,don har ta gama hango kudaden da abinda zatayi dasu idan sun samu,lallai magauta da maqiya ganin bayanta ba yanzu ba,ita din me sa'a ce,tayi musu shalll.....
[11/25, 12:59 PM] Safiyyatulkiram: 85

"Angel ya kika yimin haka?,kinajin naquda kika bari na tafi na barki?,bayan alqawari ne muka yiwa juna,dadi ko wuya zamu rabasu tare?" Kyakkyawan murmushi ta sauke masa duk da har yanzu da qwalla a idanuwanta

"Banason raba maka hankali ne ko na tashi hankalinka,kayimin dukka wani abu daya dace kayi din"

"Duk da haka angel,ki yafeni" ya fada yana sanyata cikin jikinsa yana kuma shafa bayanta a hankali.

Yadda taji zuciyarsa na bugawa ya alamta mata zuciyarsa ta motsu da soyayyarta,hanya mafi sauqi kenan da take gane hakan

"Ka cancanci dukka yabo da kuma jinjina" ta fada masa murya can qasa,sai kuma ta zare jikinta a hankali,da kallo ya bita

"Banyi wanka bafa,jikina duka warin asibiti yakeyi"

"Yafimin qamshin dukka turaren dake duniya" ya amsa mata yana narkar da idanunsa cikin nata,yana sake jin ta zama mallakinsa.
Chapter 105 · 0% Book details