← Book details Gurbin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 113

Sashe 58

Gurbin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai sannan ya buda wayoyin yana duba lokaci,zai isa ya samu sallar azahar a gaba cikin jam'i,yana shirin sake kashewa kiran hisham ya shigo masa

"Barka da rana yaaya"
"Yauwa,kana lafiya?"
"Lafiya lau,akwai kayan da aka maka order ne ka saka phone number dita?" Shuru ya danyi

"I don't think so,but ka kira mr farid,na bashi wani aiki last month,ban san ko shi ya saka number dinka ba"

"Okay yaaya"

"Kaman kana hanya ko?"

"Eh,ina ta wajen unguwarku,naje na duba patient din da na yiwa surgery jiya,sai na biyo wani suya spot"

"Bakaji ko?,kai ne can gobe kaine nan,ka samu standard waje daya ka tsayar dashi duk sanda kwadayinka ya tashi,kaman ba likita ba?" Dan shafa kansa hisham yayi,ja'afar din badai aqida ba,shi kam duk inda yaji taste dinsu ya masa ko yaga abinda yakeso indai ya gamsu da tsaftar wajen zaije yaci

"Am sorry" yace masa a taqaice,don yasan bazai tsaya sauraron dogon jawabinsa ba

"Sorry for your self,ka biyo ta gida ka daukeni"

"Okay" ya amsa shi yana murmushi sannan ya aje wayar,yayan masa is very different and unique,komai nashi ya bambanta dana kowa,shi yake sarawa jabir da suke zaune lumi baka jin kansu.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 45

Sosai ta tsorata kamar yadda ta saba,comb din hannunta ya sulale a qass,bugun zuciyarta kuma ya sauya,zuciyarta ta fara tantama shine ko muryarsa ke mata gizo?,don gusar da tantama sai ta waiwayo cike da fatan ya zaman bashi bane.

Ido hudu sukayi dashi sanda yake kurbe kununsa,wannan tsoron dake haifar da wani kyau cikin qwayar idanunta ya bayyana muraran,hakanan yadda gashin kanta ya sauko ya qawata fuskarta ya kuma yi mata ado sosai,ba tare data qara tunanin komai ba ta laluba hanyar toilet,ta manta da cewa qofar toilet din yafi kusa dashi akan inda take tsaye.

A nutse ya dire cup din a saman side drower din dake gefansa idanunsa a kanta yana jiran isowarta,goye hannayensa yayi a qirji yana kallonta har xuwa sanda ta qaraso dab dashi da niyyar wucewa a rude,babu zato kuma babu tsammani taji an ruqo dukka hannayenta gaba daya,sannan kuma ya jata zuwa cikin jikinsa,ya rungumeta ta baya,hannuwansa riqe da dukka hannayenta biyu,rungumar data sanyashi cikin nadama bayan ta samu kyakkyawan masauki cikin jikinsa,gashin kanta ya musu rumfa gaba daya shi da ita,sahihin qamshin hair mist din da yake ji daga nesa bayan ya shigo dakin a yanzun yaji ainihinsa,lallausar fatarta data gama mulketa da wani body lotion mai wani irin sulbi da qamshin rose ta gogi jikinsa,saura kadan yayi missing numfashinsa na gaba,dukka gabbansa suka saki,wani irin yanayi da bai taba zata ko kawowa zaijisa daga kowacce mace ba macen ma irin maimunatu da yakejin zai iya haifar kamarta lokaci daya ya saukar ma kowanne lungu da sawo na sassan jikinsa.

A jikinta ta dinga jin kamar jinin jikinta ke daskarewa saboda tsoro.

Tun daga tafin qafarta zuwa hannayenta dake cikin nasa sunyi wani irin sanyi saboda tsoro da mamaki,kasantuwarta a jikinsa sai takejin kamar cikin wani mafarki take,ire iren mafarkan da suka takura mata kwanakin baya,har ta dinga tsammanin tana da wata lalura data shafi jinnu,amma kuma bayan sun karanta a fiqhu cikin alamun balagar mace da suke nuna kaiwarta munzali irin wannan mafarkin sai hankalinta ya kwanta ta kuma fuskanci abinda ke faruwa da ita.

Tsigar jikinta ce tayi wani mugun zubawa,kanta kuma ya sara sanda hannunsa ya shafi wuyanta a qoqarinsa na tattare gashin nata gefe guda,bata warware ba daga wannan taji ya juyota gaba daya tana fuskartarsa cikin hanzari,tashin hankali!!....ta fada qasan ranta,ta fiddo idanunta dukka waje tana jin yadda towel dinta ya kunce daga daurin data masa,ya kuma fara warwarewa a hankali a hankali,ta kuma yi imanin nan da wasu sakanni zata iya kasancewa tsirara kenan?.

Ta bangarenshi baisan me yake faruwa ba,yadda ta zare idanun nata ya sake haifar masa d wani abu ya kuma gasgata masa tsananin tsoronsa da takeyi

"Why all this fear?Am I a monster?" Yayi maganar yana kafeta da ido,da mugun hanzari ta girgiza kanta,tun kafin ma yakai aya,cikin shagwabarta data zame mata jiki,shagwabar da a baya idan inna furera ta daketa ta fara bata haquri sai tace da ita ba tare da duba da cewa haka yanayinta yake ba tun usuli

"Shegiya karuwa,wannan,irinku ne idan kuka kama mazan jam'a a bariki ba matarsa ba,haar uwarsa saidai ta sallama muku shi"

"Kayi haquri don Allah" maganar ta fito da wata siririyar qwalla daga idanunta,saboda yadda taji towel din naci gaba da ware kansa.

Idanunsa ya lumshe kadan sannan ya sake budesu,hawaye.....hawaye,he hated it,me yasa kuka baya mata wuya?,shagwaba kamar 'yar fari ko auta?,yayi qiyasin hakan a ransa ba tare da yasan ita din bace

"Nooo,dole ki nunan abinda yake baki tsoro a jikina" kai ta shiga gyadawa

"Babu komai"

"It's a lie kuma ban yarda ba" ya fada yana tsuke fuska tare daci gaba da kallonta

"Allah....wayyo Allah daadata!" Ta fadi kukanta yana qaruwa tana kuma neman durqushewa a wajen saboda jin ya fara salube mata.

Dubansa yakai ga jikinta,sai a sannan shima ya karanci meke faruwa,wani mugun shock yaji sanda idanunsa suka kai kan saman rabin dukiyar fulaninta da suka fara fitowa,ba tare da tunani na biyu ba ya sakar mata hannuwanta da gaggawa ya kuma juya mata baya,sannan a hankali ya nufi inda ya aje cup dinsa ya dauka yana ficewa daga dakin ba tare da ya jira komai ba.

Bai samu baba tabawa a falo ba,sai ya fice kawai daga sassan ya kuma wuce parking lot,inda ya samu drivernsa yana jiransa,bai jirashi ya bude masa qofar ba ya bude ya shiga,sannan ya bashi umarnin tafiya.

Sosai yayi relaxing a bayan motar bayan ya kulle idanuwansa yana sauraren yadda bugun zuciyarsa ya sauya cike da mamakin faruwar hakan a gareshi,fuskarta da gifta duhun idanuwansa sanda take kukan,wanne irin tsoronsa take haka?,idan ta bayyana hakan gaban mutane akwai wanda zai yarda dashi kan ba wani mummunan abu yake aikata mata ba?,bude idanun nasa yayi a nutse yana duban hanya,a hankali qamshin jikinta yake yana tashi ta gaban suit dinsa da hannayensa,sai yaja dan qaramin tsaki,yana ji a ransa he's totally wrong.

Ta jima a duqe a wajen tana sharar qwalla,don batasan ma ya fita a dakin ba sai da taji shurun yayi yawa,a hankali ta daga kanta,ta tabbatar baya dakin,sannan taja jikinta daga wajen,tana riqe da towel din nata gam,kamar wadda aka ce za'a qwacewa shi,saman gadonta ta nufa ta zauna,amma sai zaman ya gagareta,wani irin mutuwan jiki takeji da kasala,gaba daya kamar an samu abu an buge mata gabbanta,gefe daya kuma zuciyarta kwata kwata babu dadi,musamman idan ta tuna a yau din wani namiji ya ganta a rabin tsirara,sai wasu sabbin qwallar su sake zirto mata,saidai ta saka hannu ta shafesu.

Ta kwashe awanni masu yawa a haka,ita ba me lafiya ba ita ba mara lafiya ba,bata tashi ta shirya ba hakanan bata fita a bedroom din nata ba,abu daya ne ya tsaye mata a rai yake ta mata yawo,duk juyin da zatayi sai abinda ya farun ya wulga mata a idanunta,hakanan duk motsawar da zatayi sai mayataccen qamshin da ya bar mata ya kada har qwaqwalwarta,tamkar a yanzun ne yake tsaye cikin dakin,tafukan hannuwanta gaba daya sun rune da qamshin wani dan mitsitsin oily pen perfume da yake amfani dashi,idanunta ta lumshe tana shaqar qamshin har cikin qwaqwalwarta,yana silalewa a hankali zuwa zuciyarta,sai ya tuna mata da handkerchief dinsa dake wajenta,d same qamshin da yake jiki kenan,best scent ever data taba ji me wani irin yanayi,duk da yadda zuciyarta keta qyamatar qamshin amma ta kasa daina shaqarsa,daga qarshe bayan ta gama shafe awanninta,haka ta janyo mataccen jikinta ta sauko daga gadon ta nufi toilet ta sake wanka,waiko zata samu ta raba fatarta da mayen qamshin dake qara mata kasala.

Koda ta fito ma tsaiwa tayi gaban mudubi tana duban yadda fuskarta tayi jaa saboda kukan da tayin,ta sauke idanunta saman qirjinta tana tuna a yadda ya ganta,sai ta dan zame towel din tana iya dai dai yadda ya kufce mata a dazun,dukka idanunta ta qwalalo waje,indai towel din yakai haka sakkowa tabbas yaga fiye da rabin jikinta,wasu qwalla masu zafi suka sauko mata,amma kuma sai tayi hanzarin gogesu sanda taji muryar baba tabawa tana knocking qofar gami da tambayarta lafiya ta jita shuru?,ta fito ta karya kada abincin ya huce

"Gani nan fitowa baba" ta amsa mata,sannan taja lotion dinta da hanzari tana sake sabon shafa.

Cikin doguwan rigan wani material mara nauyi ta shirya,ta gyara sumarta ta hadeta waje daya,sannan ta yafa dankwalin kayan,har tayi gaba ta dawo ta dauki wayarta sannan ta fito.

A zaune a falo ta samu baba tabawa,daga kanta tayi da niyyar cewa wani abu sai suka hada ido da maimunatun,tadan zuba mata idanu kadan saboda yadda fuskarta take nuna tayi kuka,kamar zata ce wani abu sai ta fasa,saboda ta tuna dazun,shima taga fitarsa daga dakin da wani mugun hanzari,hakan yasa taji bai kamata tace komai ba,don tsakanin miji da mata sai Allah,fatanta kawai ubangiji yasa ba wani abu mara dadi baje ya faru a tsakaninsu ba,kuma Allah ya kawo daidaito tsakaninsu nan kusa.

Kadan ta zuba abinda baba tabawan ta dafa ta fara tsakura,saida kadan taci ta tashi,saboda tana jin cikinta gaba daya ya cushe,kamar babu wani sauran space na zuba abinci,data dawo saman kujera ma kwanciya tayi,yau ko hirar da sukanyi da baba tabawan jifa jifa ta dinga yinta,tans ankare da ita,lokaci lokaci sai tayi kamar ta tafi tunani,sai kuma ta sauke ajiyar zuciya taci gaba da abinda takeyi.

Kafin azahar jiki da zuciyarta yayi laushi qwarai,sanda ta shiga sallar azahar mamakin kanta ta dinga yi,me yasa abinda ya farun a daxun ya tsaya mata a rai ta kuma kasa mantawa?,me yasa har yanzu take jinta kamar rungume take cikin jikinsa?,me yasa qamshinsa da kamanninsa suka kasa bace mata?,me yasa take hango idanunsan nan take jinsu da nauyi?,saita sake wata irin ajiyar zuciya me nauyi tana tabe baki kamar yaron dake shirin sakin kuka,kafin daga bisani tayi qoqarin daidaita mode dinta ta wuce bandaki don ta dauro alwala.
Chapter 58 · 0% Book details