← Book details Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 22

Sashe 9

Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a sannan shugaban makarantar ya tabbatar ya ya yi kuskuren barin wannan abin da ya faru

Kneel down aka sa Khadija a gefe guda yayin da suke shirin kai Laila asubiti

mikewa tai Khadija ta nufi hanyar fita daga makaranta da gudu tana kuka ta nufi gidansu Laila

yayin da duk malaman mamaki ya matukar kamasu da fitar ta
hakan ya sa aka tura malamai mata biyu suka bita, domin a zatonsu aljanu ne

Bayan sun isa asubiti aka kwantar da Laila dake asubitin gwamnati ne kuma babu wadatattun ma aikata
likita daya aka samu ya yo kanta .

Khadija tana shiga gidansu Laila ta sanar da mahaifiyar ta , ita ma da sauri tayiwa Barrister waya
kafin ka ce komai sai ga shi ya dawo cikin tashin hankali
sauran malaman da suke tafe da Khadija suka nufi asubitin
sakamakon barrister Adam yana zuwa matarshi da Khadija ya dauka suka tafi .

Yana zuwa ya ga da gaske Laila ce cikin mummunan yanayi, bai ce da kowa uffan ba ya dauketa ya sata a mota .A Lokacin malaman suka ringa kokarin yi masa magana , amma babu wanda ya kula a cikinsu ya shiga mota ya nufi babban asubitin yayanshi . Suma suka bi bayan shi.

Tom ni Fatima Abdallaah kano

Ina sanar daku akwai masu yawo suna 'bata mata suna

wato ana bud'e group na batsa na iskanci ana dora novels din mu jikin wannan link ana share.

zaki shiga d nufin samun novels, tom sai ki ga ba haka ba
dan haka muna sanar d ku ba mu bane ba kuma zamu yafewa wanda suke shirin 'bata mn suna ba

A kiyaye

Kalisa ce cikin d'akin mahaifiyarsu cikin tsananin kadaici da kewa , bayan tasha kuka ta more , sannan ta zauna kan gado , wata loka dake kusa da gadon ta jawo , haka idanunta suka kai kan wasu takardu
d'ebosu tai kallo guda tai musu ta ji jikinta ya mutu , a sa'ilin data fahimci takardun gidan Hajjiya ne wanda Alaji ya bata , ta mayar ta aje

Wayarta ce ta fara ringin ta dauki wayar ba tare da yanayin ta ya canza ba ta ce ,"My Umar har ka zo."

Umar ya yi ajiyar zuciya yana cewa, "Haba My Kalisa ta ya zan yi wasa da lafiyarki , bayan an ce yau ne dactor zai zo , kawai maza ki fito mu tafi ."
Kalisa ta ce ,"Tom shi ke nan." Ta aje wayar ta fita
tana fita falo ta yi sallama dasu baba anje , suka mata fatan samun lafiya sannan ta fita , tana fita
Umar suka nufi asubitin,sakamakon ba nisa ne dashi ba , a kafa suka isa suna hira .

Doctor jamil ne zaune cikin office dinsa tare da laptop a gabanshi , a lokacin sukai sallama suka shiga . Cikin girmamawa doctor ya tashi ya taro su , sa'ilin da ya basu wajen zama
"Sannunku fa , wato Umar duk an mance damu."
Doctor Jamil ya yi maganar cikin kyakykyawan yanayi

Umar ya mai da masa da cewa ,"Kai fa ka fiye surutu dan Allah haba naga kusan kullum muna gaisawa a online. "

Jamil ya ja tsaki yana kallon Kalisa da cewa ,"Kalisa ya karin hakuri. "?

" Mun gode Allah dactor. " Kalisa ta ba shi amsa
a lokacin wata nurse ta shigo , yayin da Doctor ya kalleta tare da mika mata wata takarda yana cewa,"Ku je tare da Kalisa ai mata wannan gwaje-gwajen , yanzu fa ."

Nurse din ta amsa yayin da Kalisa ta bi bayanta .

Umar suna zaune suna hira ba jimawa Kalisa ta shigo da takardar binciken lafiyar da aka mata.
Ta mikawa dactor sannan ta zauna tana kallon Umar yana mata murmushi.

Bayan dactor ya bude sakamakon ya yi ajiyar zuciya yana kallon Kalisa .Wanda duk hankalinasu ya koma ga dactor Jamil .

A zube min comment a private mu had'u next page.

Share, like and comment.........,📚

Gubar Rayuwata⚡🌹
By
Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)

*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><>

Page 19&20

Ba editing

"Wato Kalisa zahirin gaskiya wannan ciwon naki , sai an miki aiki , domin a halin yanzu ma hunhunta ya samu matsala." Ya karasa maganar yana kallon Umar
wani faduwar gaba Umar ya ji ya bigi zuciyarsa ,

"Kuma gaskiya wannan aikin na gaggawa ne , don haka zan yi magana da dactor Aisha dake babban asubiti, zan tura ku can ." Doctor ya kuma fade

Kalisa cikin mutuwar jiki ta kalli Umar tana cewa, "Ka ga ni ko Umar , na kusan mutuwa."

"Haba Kalisa ai cuta ba mutuwa ba ce , an yi wa mutane da yawa aikin kuma sun sami lafiya dan haka kema insha Allah zaki warke , saidai aikin gaskiya akwai kud'i sosai ,duk da nasan baku da matsalar sa ."
Umar ya ce "Yanzu dai yaushe ne za mu je asubitin.".....

Ahmad ne yake wa Zainab fad'a sosai a kan Harun, amma sai kare shi take tana nuna Mahmud ne yake son bata masa suna , Ahmad saida ya matukar yi mata gargadi tare da mata barazanar sanar da Alaji abin dake faruwa duk da hakan dai har zuciyarta bata shirin barin Harun .

Kalisa har sun je wajen doctor Aisha a yau , nan ta tabbatar musu da dinbin kud'in da aikin zai ci .

Bayan sun dawo gida suka sanar da baba anje komai . Nan akai waya suka sanar da Sahid halin da Kalisa ke ciki ga kuma irin kudaden da ake bukata
Nan ya tabbatar musu ba wata matsala zai turo da kud'in
har yake sanar musu ma zai basu dukiyarsu ta dawo wajensu.
Amma har washe gari shiru , Sahid bai ce komai ba , wayarshi ma a kashe
Jafar ya je companin da Sahid yake aiki amma bai samu ganin shi ba .

A halin yanzu Laila ta sami lafiya, amma har yanzu Barrister Adam bai ce da makarantar DR.DD komai ba
Ansha matukar jinya kuma ana kansha a kan ciwon Laila , barrister yana kashe kud'i sosai
babban abin da ya ke ci masa rai wai Laila 'yarshi za a wa wannan tozarci har hakan ya jawo mata ciwon zuciya.

Rashin sanin irin matakin da zai dauka a kan makarantar ya sa har yanzu bai ce komai a kan lamarin ba .
Su ma malaman makaranta sun shiga rudani , musamman ma shugaban , yarinya ta kamu da ciwon zuciya lokaci guda , to da zuciyar bugawa tai ta mutu fa .
wannan kaddara ce ta shigo masa makaranta, kuma yadda ya biyewa Uncle Yahaya har hakan ta faru .

"Wai Khadija yaushe zaki dawo makaranta". Wata Zainab kawarta ta fad'a

Khadija ta kalleta tana ta'be baki ta ce ," Ni na bar wannan makarantar wallahi, domin dady ma ba zai takurani ba."

Zainab ta ce "To Allah ya kyauta ya bawa Laila lafiya, ni Wallahi ma abin da yake bani mamaki ashe da gaske Laila haka take son Uncle, ki dubi yadda zuciyarta ta so bugawa. ai wallahi Allah zai saka mata."

Khadija da duk kan 'bacin rai ta kalli Zainab ta fara magana, "Ai wallahi Uncle ya yi asara , kuma jira nake kawai dadyn Laila ya yi magana."

Zainab ta ce ,"Allah dai ya kyauta."

Cikin tsananin fad'a baba anje take magana
"Wannan ai wulakanci ne , haka ake yaron nan ya bamu kud'i amma har yau shiru , tun yaushe ake masa magana kuma kullum ciwon Kalisa girma yake."

Umar dake zaune a gefe guda cikin falon ya girgiza kai alamun goyon bayan abin da baba anje take fad'e

Jafar ne ya ce ,"Gaskiya kam dai Sahid bai kyauta ba kaka , to mene abin yi."

Kalisa ta ce ,"Me zai hana muje gidansu yanzu Umar, kasan babanshi abokin dady ne, kuma da zarar mun je zai masa magana. "

Baba anje ta ce "Eh gaskiya ne Umar ku tashi ku je yanzu domin wannan lamarin bana zama ba ne ."

Kalisa cike da kwalla ta kalli baba anje tana cewa ," Muna matukar godiya Baba anje , kina tsayawa da nuna damuwa a kan lamuranmu Allah ya baki.......".

Dakatar da ita tai tana cewa, "Haba Kalisa ai zan tsayawa lamarin ku bakin rai bakin fama ku amana ne gare ni . Tashi ku je kawai a dawo lafiya ."

Umar ya tashi yayin da Kalisa tabi bayanshi , sannan ta juyo ta kalli Jafar tana cewa, "Bari na tafi da mota jafar."

Jafar ya ce "To a dawo lafiya daman akwai mai a ciki ai."

Suka nufi harabar gidan ita da Umar.

Anan kuwa cikin makaranta duk kan malamai sun had'u suna tattaunawa a kan matsalolin makaranta, ana cikin haka wani mutum ya shigo a mashin
guri ya samu ya yi burki sannan ya sauka ya nufi ofishin shugaban makaranta,
ai kuwa duk malamai suna cikin office din
mutumin karasawa ya yi yana gaida shugaba, sannan ya mika masa sako ya fito , bai jira cewar komai ba ya fito ya hau mashin din sa ya tafi .

"Ikon Allah".
wani a cikin malamai ya fad'a, Uncle Yahaya ma yana zaune shugaban makarantar ya bud'e takardar

jin abin da Dr Dauda ya fad'a yasa duk hankalin malaman tashi

Cikin yaren turanci wata malama yare ta ce ," Me ke faruwa sir."

Sauran malaman kunne suka kasa domin jin amsar da zata fito daga gareshi , domin a halin yanzu suma ita ce damuwarsu

Ido ya kafa wa uncle Yahaya cikin tashin hankali, hakan ya sa Uncle tsarguwa yana cewa ,"Shugaba lafiya kuwa."

Cikin zafi shugaban makarantar ya tashi tsaye yana cewa, "Barrister Adam ya shigar damu kotu , wannan takardar tuhuma ce ." Ya karasa maganar yana cillawa Uncle Yahaya takardar

Wani tsoro da mamaki ne ya ziyarci malaman

Dr. Dauda ya zauna yana kifa kansa kasa yana cewa, "Innalillahi, yanzu sunan wannan makarantar zai baci a idon duniya , na tabbatar har mane ma labarai za su yad'a wannan case a labaransu , innalillahi wa Inna.....".

Uncle Sani ya kalli sauran malamai yana cewa," To yanzu mene abin yi , ya kamata a nemi mafita wallahi. "
Chapter 9 · 0% Book details