← Book details Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 22

Sashe 2

Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" To har kafin a aiko ma munje mun dawo rakani za ki fa."
Ya karasa maganar kamar zai had'e jikinsa da nata,
Murmushin ya'ke ta yi tana cewa, "A'a gaskiya baby."

Had'e rai ya yi sosai yana cewa, "To Gaskiya na yi fishi."
Rufaida tace, "Yi hakuri to ka fad'i wani abin da zanma sai ka hakura."

Cikin fushin Harun ya kalleta yana cewa, "Abu daya za ki mini ."
Ta sake fuskantarsa tana cewa, "ina ji."
Yace ,"To rufe idanunki."
Rufaida ta rufe idanunta tana murmushi, ba zato ba tsammani kawai taji Harun ya cafki bakinta yana tsotsa
Furgita tayi tana ture shi tare da saurin fita daga motar
shima sauri ya yi ya fito yana cewa, "Haba mene hakan kuma."
Ta kaici ya hana Rufaida cewa komai kawai yawu take tofarwa tana share bakinta

"Ai ni dama na dad'e da sanin ba sona kake ba kawai kanason lalata dani ne Harun." Ta sake tofar da yawu tana cewa, "To wallahi indai ni ce daga sama na har kasana haramun ne a gare ka, kwarton banza mahaukaci , malalaci kawai ."
Ta tofa masa sauran yawun dake bakinta tai shigewarta gida .

Share yawun ya yi yana cewa ,"Na kwafsa na yi gaggawa ,amma shi ke nan."
Ya shige motarsa ya tafi .

Ma daidaici ne mai fad'in jiki wasu sa iya kiransa da kyakykyawa, yana zaune cikin falon Alaji Idris, yana kallon yadda wannan gidan ya burgesa , bayan su gaisa da dukkan mutanen gidan ne , sai suka tashi suka bashi guri shi da Kalisa.

kallon Kalisa ya yi ya kuma yana kwarai da gaske kyakykyawa ce , "Kamar yadda dai kika sani suna na Sahid , sannan ina aiki ko ince ni ne manager company na Alaji Tasi'u mai turare."
Kalisa da zancen Sahid ya isheta ta bukaci komawa cikin gida , aiko hakan yasa Sahid komawa gidansu.

SAHID

Sahid dai d'an abokin Alji Idris, kuma Amininsa wato malam Aminu , a kwai matukar Amana a tsakaninsu ,
kuma Alaji Idris ya yi wa Sahid sanin mutumci da tarbiya, ga tsoron Allah da sanin ya kamata , hakan yasa dukkan wasu kadarori daga abin da ya shafi ,gonaki , filaye gidaje da sauransu na Alaji Idris suna karkashin kulawar Sahid , domin Alaji kallon d'an cikinsa yake masa, hakan yasa yake son ya ba shi auren Kalisa domin yana da ya'kinin zata samu farin ciki, saidai Kalisa babu wanda ta mallakawa zuciyarta sai Umar.

Anan gidan Alaji Kabiru , Zainab ce kwance a kan gadonta tana karanta littafin Hausa wato novel, hangen wayarta tai ta kawo haske , hakan ya tabbatar mata da message ne ya shigo , ta mike ta ciro wayar a caji tana kokarin ganin message d'in da ya shigo mata .

Share and comment...📚

Gubar Rayuwata⚡🌹

By

Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta).

_________________________________________

*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><>

Editing❌

Page 3 & 4

Number ta gani babu suna an rubuta ,"masoyiya ya kike ? ya gida Allah yasa kina lafiya."
A zuciyarta tace to waye wannan ni dai nasan ba yaya Mahmud ba ne .
Typing ta fara tana mayar masa da cewa ,"lafiya kalau nake amma waye ."?

Harun da ganin sakonta ya zabura yana murna ya sake maida mata da cewa, "Bani da suna amma mafi yawanci ana kirana da mai kaunar Zainab."

Murmushi tasa da ganin ganin sakon nashi , kafin ta sake turawa ya turo mata cewa,"Mai kaunar Zainab da fatan rayuwa da ita har abada ".
Kawai Zainab tai a jiyar zuciya.
" Yanzu Uncle tafiya zakai."
Laila ta fad'a cikin damuwa

Uncle Yahaya ya kalleta yana cewa, "Haba Laila kwana biyu ne fa , ni dai kawai idan na dawo ina san kalamaina masu dad'i."

Laila tai murmushi, saida ya sake komawa gidansu ya sake sallama da kakarshi sannan ya tafi.

Ita kuwa Laila sai 'ku'kewa take tana had'o masa kalamai. tana cikin yin ne Khadija tazo ta warta, aiko ta bita .

Yau ma Sahid yaje gidan Alaji Idris, saidai ita Kalisa har yanzu bata jinshi a zuciyarta, kullum saidai Umar kuma ta'ki fito mana da Umar mu ganshi.

Alaji Idris yana cikin a zaune, sai ga Garba nan ya shigo Alaji ya kalleshi yana cewa, "Ahh, haba Garba sai kace ba ka garin , nan da nan baza a ringa zuumunci ba ko na yi laifine."

Garba da sauri da Girmamawa ya fara cewa, "Haba Alaji, wallahi babu abin da kai mini , kasan zaman birni , motar tawa ce ta lalace shi yasa ba a ganina har saida aka gyarata."

Alaji Idris ya had'e rai yana cewa, "Haba Garba yanzu motar taka ta lalace amma ba za ka sanar dani ba , to mene amfanin ...."

Dakatar dashi Garba ya yi yana cewa, "Haba Alaji , Yanzu ni saboda abin kunya da raashin tausayi , motar tawa ta lalace shi ne sai na jira ka gyara mini .

To mene amfanin kud'in da nake hayar da ita ."
Garba ya sake gyara zama cikin tausayi da girmama Alaji yana cewa, "Haba ! Ai wallahi bazan mance da abin da kai mini ba , ka kawoni birni ka bani sana'a ka ko ya mini zama da mutane, ka se mini..."

Alaji Idris ya dakatar dashi yana cewa, "Karna sake jin kana fad'e , to mene 'yan uwanta kar GARBA."
Garba yace ,"Gaskiya ne ."
Nan dai suka gaggaisa Garba ya koma , domin gidansa yana cikin gidan Alajin daga wajen gefen gate , ya dauko shi daga 'kauye ya ba shi mota ya ara masa gida , domin Garba da Alji Idris 'yan uwa ne , mahaifinsu d'ya wanda yanzu basu da kowa.

Ahmad ne zaune kan kujera , Zainab kuma na kwance kan 'kafar yayannata suna hira, hirarsu suke cikin kwanciyar hankali da farin ciki , ga shi kuma anata 'kwad'o sallama amma babu wanda yaji a cikinsu , saida Hajjiya Salima ta fito daga d'akin girki ta tsaya kansu cikin b'acin rai sannan suka san halin da ake ciki ,

Kafin su ce komai Hajjiya Salima ta je ta b'ud'e kofar

Yaya Aminu da Yaya Mahmud ne
Hajjiya ta dawo gabansu Ahmad tana cewa, "Kuna ji ana sallama amma kun yi shiru ."
Zainab ta tashi kan 'kafar Ahmad yayin da Ahmad yake cewa, "Wallahi momy bamu jisu ba ko kad'an."

Mahmud da ke tsaye ya kalli Zainab yana cewa, "Taya za ai kuji , kullum ba ka da aiki sai shagwa'ba wannan yarinyar."

Da sauri Ahmad ya cafe yana cewa, "Haba Mahmud kasan bani da kowa , sai ita kawai , ai dole na sota na nuna mata soyayya kafin ta barni , kuma momy ta'ki haifo wasu."
Dariya yaya Aminu yasa ya kallon Zainab

Hajjiya ce ta kalli Ahmad tana cewa, "To aku , sai kai musu shiru ai su zauna su huta ko ."

Duk dariya suka saka yayin dasu Aminu suka zauna .

Aminu da Mahmud kamar 'ya'ya suke wajen Alaji Kabiru, domin dukkansu 'ya 'yan kannensa ne da suke zaune a Kaduna, wanda Yanzu sun kawo musu ziyara ne .

Aka kawo musu kayan motsa baki masu da kyau suka ci suka sha, yayin da wata iska ke shigarsu suka fara hira.

Mahmud ne ya kalli Zainab yana cewa, "Su Zainab'yan mata."

Wani kallo ta jefa masa tana cewa, "Uhum."

Wayarta ce ta nuna mata alamar sa'ko hakan yasa ta 'bud'e wayar tana karantawa,"Dan Allah my life ki amshi soyayyar da nake miki dan Allah. "
Zainab ta mayar masa da , "Bana san zancen banza koma waye kai ka fito fili mana ."

Su kam su Aminu hirarsu kawai suke , amma Mahmud rabin hankalinshi yana wajen Zainab da ba ta sauraransu.

Harun ya dawo mata da amsa, "Idan kin shirya ina son mu had'u gobe ."
"Ina zamu had'u."
Ta tura masa .

"Gidan abincin dake bayan gidanku da karfe 11na safe."
Kawai ajiyar zuciya ta yi ta mi'ke zata shiga d'akin ta, Mahmud ne ya dakatar da ita da kiran sunanta ,"Zainab. "
Ta juyo tana kallonsa

sannan yace , "Ina son gobe da safe za ki rakani asubiti zan je wani aiki."

Tsayawa tai tana cewa, "Gobe kuma da safe."
Mahmud yace ,"Eh."
Saida ta d'anyi jimmm sannan tace ,"To Allah ya kaimu."
Ta shige cikin d'akinta .

Yau Alaji Idris shi da Hajjiya Maryam ziyara ya kai wa wani tsohon abokinsa . a hanyar dawowa ne ya kad'e wani yaro wanda yake tafe da kakarshi ,
aiko hankalin Alaji ya matukar tashi sosai , hakan yasa ya garzaya asubiti da yaron , sai dai ina rai ya yi halinsa domin yaron ya rugamu gidan Gaskiya,

Hankalin kowa ya matukar tashi sosai , aiko Alaji Idris ganin cewa wannan tsohuwa bata da gata yasa ya taho da ita gidansa , ta tabbatar musu yaron jikanta ne da iyayensa duk suka rasu , su kad'ai suke zama .

Tare da gawar yaron ya taho gidansa , anan akai masa komai aka kaisa makwancinsa.

Bayan Uncle Yahaya ya isa legos , sun yi biki , aiko suka ringa yawon bud'e ido da abokansa ,
a garin yawon ne Allah ya had'ashi da wata karuwa wacce ta manne masa .

Yanzu haka yana zaune da wani abokinshi ranshi a matukar 'bace yace , "Ni wallahi Shu'aibu zuwa na legos bai amfane ni da komai ba sai masifa."

Shu'aibu ya kalli Uncle Yahaya yana cewa, "Haba !Karka bada maza mana , kawai don yarinya ta mannema shi ne masifa , to wallahi kafin ka tafi ka amince mata kawai inba haka ba Wallahi za kai asara."

Cikin haushi Uncle Yahaya ya kalli Shu'aibu yana cewa, "Wai wannan banzar yarinyar , sanin kanka ne karuwa ce , me zan samu a gunta."

Dariya Shu'aibu ya kwashe da ita yana cewa, "Wallahi ina ma ni ne , ai ko ita ce zaka samu wani abu agunta kana ganin yarinya cikakkiya , ai wallahi dani take so tuni an wuce gun , kuma wallahi babbar karuwa ce , domin ko kud'in yaharta bani da shi."
Chapter 2 · 0% Book details