← Book details Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 22

Sashe 21

Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Musa ya ce ,"Wallahi ba zai mutu ba , amma wata kila ya karye."

suka kwashe da dariya Musa ya ce ,"Tsoron da nake kada malam ya samu labari."

"Ba ta yadda za ai ya samu." Cewar Allaro

Mutanen anguwa ne suka taimaki Harun suka kaishi asubiti

bayan ya samu kanshi ya kira wani abokin shi Jamilu

"Yanzu wane ya maka wannan abin da Allah Harun."

Harun cikin zafin ciwo ya ce ,"To Allah ne masani ai domin wallahi ta baya naji an rufe ni da duka ban san komai ba banga kowa ba."

Jamilu ya ce ,"Wallahi dukan mutuwa su kai maka dubi kunne ka amma Likita ya ce ba matsala koh."?

Harun ya yi ajiyar zuciya tare da cewa ,"wallahi matukar ciwo wannan kunnen yake min , ni bama wannan ba so na ke na koma gida yau ."

Jamilu ya ce ,"Wai Tiga kake magana.Ka bari ka warke mana."

Harun ya ce ,"Ka ga idan zaka kai ni tom idan ba za ka kaini ba saina kira Yahaya duk da ina ta kiran wayarshi a kashe."

"Dan Allah ka bari kaji sauki mana haba Harun ."

Cikin bacin rai Harun ya ce ,"Wato na zauna sai yau a biyo dare a kashe ni koh ? Wallahi yau gida zan koma."

Jamilu ya ce ,"To ai shi ke nan Allah ya kyauta."

Yau dai Mahmud ya shigo kano, Zainab ta matukar farin ciki sosai ya ga kauna da soyayya a zahiri wajen Zainab,

Daga karshe har gidansu Hauwa yaje ya gaida mahaifinta wanda shi lu'utanal da kanshi ya ba shi invitation na bikin Hauwa ya sanar dashi yana gayyatar shi.

Sahid yana can yana fama da rayuwa sai yanzu yasan da cewa tabbas ba shi da gata ya yi matukar shiga tashin hankali yayin da ya lura tabbas hakkin mahaifishi sai ya bishi ,

Ga ciwon kafa da yake matukar fama da ita , a cikin satin ne da likita ya je bursun din aka duba masa ita aka kuma tabbatar cancer ce ta kama kafar tashi.Nan hankalin Sahid ya sake tashi matukar gaske .

___________________________________________

Yau su jafar duk suka shirya
domin tafiya ta ya Umar murna na passing out din da zasi

Nasir da Salma , Nabila, Jafar da Baba anje suka tafi

Soyayyar Nabila da Nasir ta yi matukar nisa sosai

Umar farin ciki kamar ya kashe shi amma yana ganinsu ya fashe da kuka mai matukar gwanin ban tausayi

"Haba Yaya Umar mene haka kuma." Jafar ya yi maganar yayin da ya rungume shi

Umar kuka wiwi tare da hawaye

Duk sai jikinsu ya yi sanyi

Umar cikin kukan ya fara musu magana, "Wallahi tun jiya nake jiran ku Jafar cikin matukar shauki , lokacin dana hango ku Kalisa na gano a tare daku tana ta min murmushi sai da kuka karaso na ga Nabila ce."

Wani tausayi suka ji ya sake rufe su mummunan Nabila data fara kuka .

Salma ta ce ,"Ku yi hakuri dan Allah Yaya , dama aunty Kalisa ai tana tare da kai addu'a kawai zamu cigaba da yi mata. "

Baba anje ta ce ,"Haka ne a dena kukan haka dan Allah domin farin ciki ne ya kawo mu."

"Yi hakuri Nabila, inajin zafi da wannan kukan da kike, ki dena baby dan Allah." Nasir yake yiwa Nabila magana yayin da ba kowa ke jin maganar ba .

Umar ya yi musu iso zuwa ciki , suka sami guri , ana ta gaisawa nan farin ciki ya karu aka ci aka sha cikin farin ciki .

Harun dai ya koma Tiga , nan iyayensa lamarin ya d'aga musu hankali, musamman jin bai samu aikin soja ba, ga kuma abin da ya faru dashi, haka sukai hakuri suka kuma fara nema masa magani , domin kunnenshi ba a cewa komai .

Bayan wani lokaci.

Wani irin kallo Zainab take yiwa Mahmud,
Mahmud ya yi murmushi yana cewa, "Mene kuma Zainab."

Zainab ta ce ,"Yaushe ne auren mu yaya Mahmud. "

Mahmud ya rike baki cikin mamaki yana cewa, "Eh tabbas kanwata ta girma har aure ma take so."

Ta ta'be baki tare shagwa'ba tana cewa, "Ni fa da gaske nake yaya Mahmud."

Mahmud murmushi ya sake yi yana kallonta yana gyara zaman hular dake kanshi yana cewa, "Ni ma Zainab wannan ranar nake jira , domin..."

Bai karasa maganar ba Ahmad ya shigo falon yana cewa, "Tashi mu tafi."

Mahmud ya kalleshi sannan ya tashi tsaye yana kallon Zainab.

"Amma zaka dawo ko."? Zainab ta yi wa Mahmud tambaya

ajiyar zuciya ya yi kana ya ce da ita ," Gaskiya Zainab bazan dawo ba , da zarar an d'aura auren zan wuce ba sai na dawo baya ba."

Zainab ba tare da taji dad'i ba , ba kuma ta so hakan ba ta yi musu sallama suka tafi

Mahmud da Ahmad suka nufi d'aurin auren Hauwa, eh tabbas an yi buduri an yi wasa da kud'i mu dai sai dai muce Allah ya sanya alheri.

Umar ne ya nufo gidan su Jafar sanye da kayan sojoji yana tura kofar gidan ya ci karo da Nabila da Nasir suna hira, Umar ya yi sand'a ya lalla'ba ta bayansu ba tare dasun sani ba .

Share, like and comment......................📚

Gubar Rayuwata⚡🌹
By
Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)

Editing❌

Page 47 & 48

A hankali ya karasa bayan Nasir yayin da yaji yana cewa da Nabila ,"Tun da komai ya yi daidai a gaskiya sai a daura mana aure domin a halin yanzu babu wata..."

Kafin ya 'karasa yaji an tallafe masa 'keya, yana juyowa ya ga Umar

Duk kunya sai ta rufe Nabila musamman jin maganar da Umar ya fara ,"Eh lallai yaron nan wato ka girma harda zance aure , to ai sai ka bari ta gama makaranta, kai ma ka tsaya da kafafunka kafin ka yi maganar aure ko , amma ka ban mamaki Nasiru."

Umar ya karasa maganar yana rike ha'ba

Dariya suka yi a tare yayin da Nasir ya bawa Umar hanya domin ya wuce ciki

Wani mamaki ne ya kama Umar

"Me kake nufi." Ya tambayi Nasir

"Yaya ina ce wucewa zakai ciki."

Dariya Umar ya sa yana sake kaiwa kanin nashi duka yana cewa, "Dallah wuce muje ciki babu wata sauran soyyaya tunda na zo ."

Nabila da gudu tasa kai ta shige ciki , yayin da Umar ya dafa 'kanin nashi suka nufi cikin gidan .

Yauu tunda Harun ya tashi ya kasa gane inda yake masa ciwo , hakan ya sa ya yi 'kokari ya nufi asubiti wajen wani abokinshi Dactor Sa'id

Yana isa asubitin ya nufi office din shi yana bude kofa kuwa ya ganshi zaune yana cike wasu takardu

"Ahhh Aboki Harun kai ne tafe , masha Allah karaso." Cikin farin ciki doctor ya yi maganar

Harun yana zama doctor ya kula da tabbas ba shi da lafiya mussaman ganin Fuskarshi a kunbure ga kuma rama hakan ya sa kafin ma su gaisa ya fara cewa "Kaiiiii Harun sannu , baka da lafiya haka ."?

Ajiyar zuciya ta takaici Harun ya yi sannan ya ce ," Bari kawai Sa"id , ina cikin wani hali. "

Shima doctor ajiyar zuciya ya yi yana cewa, "Meke damunka haka dan Allah."

"Abokina ka ga ina fama da ciwuka da bansan daga ina suke ba , domin ka ga ina ciwon kunne."

Dactor , ya ce ,"Eh tabbas ga shi na ga yana ruwa."

Harun ya cigaba da cewa ,"Ciwon ciki , kasala , kai hatta futsarina ya canja , dama kuwa HIV ba bakuwata ba ce ."

Da mamaki abokinshi ya ce ,"Kana nufin kana da ita Harun wa'iyazubillah."

Harun ya had'e rai yana cewa, "Ka ga ni dai bana san wani iyayi kawai ka bani magani."

Murmushi Dactor ya yi yana cewa, "Gashi ma ko gaisawa bami ba , amma bari na kira nurse ummi taje ta raka ka a yi maka gwaji , shi kuma kunnen naka gaskiya sai ranar da dactor ya zo."

Harun ya ce ,"Okay ."

Likitan ya d'auki waya ya kira nurse sannan ya durkusa yana rubutu a cikin takarda lokaci guda kuma yana cewa, "Idan ka je a kai maka sai ka dawo mu yi hira kafin result din ya fito."

Yana rufe baki Ummi tana turo kofa ta shigo

Wani shegen kallo Harun ya zuba mata , sakamakon yadda ta shigo wani sindi-sindin da wani karamin hijabi

Had'iye yawu ya yi yanayin shi duk ya canja

Sa'id ya bata takardar yana cewa, "Ummi ki kai shi a dubashi bako na ne , idan result ya fito sai ki kawo min ."

"Okay sir ." Shi ne abin data fad'a

Tana fita Harun yabi bayanta , harda hard'ewa da tuntu'be yana tafiya , yadda ya ga ta ba shi baya tana tafiya yaji kamar ya yi abin da ya saba , domin ta matukar shiga ranshi a wannan yanayi

Jitai an sa hannu ana shafa mata baya cikin wani salo , hakan ya sa taji wani yarrrr ta juyo cikin tsananin mamaki da tashin hankali

Harun ta gani yana mata wani murmushi, hakan ya sake fusatata

"Kutumar uba .Kai wanne irin d'an iska ne wawa shasha ."

"Allah ya baki hakuri." Ya yi magana yana duban da hange karta tara masa mutane

"Allah wadaran jahili irin ka , baza ka gama da duniya lafiya ba wallahi Allah ya isa. Wallahi ba da ban doctor Sa" id bane ya had'a ni da kai sai ka ga abin da zan maka ".

Ta buga wani tsaki tare da harara ta cigaba da tafiya

Ana yiwa Harun wannan gwaji ya koma wajen doctor kamar yadda ya ce

" Sannu Harun ." In ji abokinshi
"To ya kake ya kwanaki ai wallahi na yi zaton zaka dawo da kakin soji."

Harun ya ce ,"Ina ta lafiyata ina wani maganar kakin sojoji , wallahi kunne na kamar , kaiii ina shan wahala dactor. "

"To Allah ya sauwake yanzu ya ake ciki ne ."?

Cewar dactor Sa'id
Chapter 21 · 0% Book details