Sashe 20
Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka ita ma Zainab ta sami wannan labarin, kuma an tabbatar mata da Harun shi ne wanda ya aikata mata wannan abu.
Zainab ta shiga wani hali tana ta kuka , yayin data tuna Lokacin da Mahmud yake shirin rabata da Harun take masa wani kallo, har ya kai ta wulakantashi , haka ta ringa kuka tsawon yini guda tana nadama .
A Yanzu babu wanda take son ji da gani idan ba Mahmud ba , amma yadda ta ga ba ta da damar , ya sa hankalinta ya sake tashi , cikin kuka ta nufi wajen Hajjiya ta sanar da ita komai kuma ta roketa da ta 'kar'bo mata wayarta wajen Alaji.......
"Umma yau ne za a zaman kotu na biyu." Jibril ya sanar da mahaifiyar shi
cikin mummunan 'bacin rai ta kalleshi tana cewa, "To mene."?
" Ba komai. " Ya ba ta amsa
"Ni tsakanina da Sahid kawai Allah ne zai mana hisabi , idan ma kotu ta sake shi ya dawo gidan nan ya ci gaba da zama , amman a ranar gobe akwai tsaiwa tsakanina dashi da mahaifin sa."
Jibril ya yi ajiyar zuciya yana jinjina dajin tsoron maganar mahaifiyar tasu."
Anan cikin kotu Lauyoyi sai musayar hujjoji suke , domin lauyan Sahid ya yi iya yinshi , har ya ke son gamsar da kotu cewa Sahid sam ba mai laifi ba ne bai kuma aikata wannan tuhuma da ake
masa ba .
Nan Lauyansu Jafar ya fara sanar da kotu manyan shaidu da kotu ta gamsu dasu , daga karshe haka Sahid ya rasa ta cewa har ya amsa tuhumar, yayin da lauyanshi bai iya kare shi ba .
Daga karshe lauyansu Umar ya nemi kotu data umarci Sahid da ya fito da dukkan dukiya da kadarori mallakin wannan marayu har wanda ya kashe ya fita birtaniya ,
Sannan lauyan ya mikawa kotu adadin kudade da kadarori da Sahid ya zaune."
Bayan alkali ya gamsu ya sanarwa da Sahid umarnin kawo wannan kadarori a zaman kotu na gaba........
Ana tashi daga zaman kotu Sahid asubiti ya wuce sakamakon ciwon kafarshi ,
Umar dai yana can , amma duk sanda akai zaman kotun yana bibiyar yaji yadda aka tsaya , wannan babbar shari'ar har gidan radio ake saurara..
"Malam wannan wacce irin rayuwa ce na shiga uku malam."
Mahaifiyar Maryam take fada cikin kuka yayin da take rike da gawar Maryam a hannunta .
"Malam Maryam ta rasu ta bar mana duniyar , ina zansa kaina , wallahi bazan yafewa wannan yaron ba , ya Allah ka ga yadda ya yi mana..." Ba tare data karasa maganar ba ta sake rushewa da kuka mai matukar gwanin ban tausayi .
Malam na lado shi ma baisan lokacin da wasu hawaye suka zu'bo masa ba , ya kalli gawar Maryam yana cewa, "Na yafe miki Maryam."
Ya yi sauri ya fita waje yana kuka .
Zainab hankalinta ya kuma matukar tashi sosai dajin labarin mutuwar kawarta Maryam, aiko cikin radadi da nadama ta dauki wayarta ta kira Mahmud amma bai dauka ba kira uku ta yi amma tana shiga ba tare da ya d'auka ba.
Ta jefar da wayar gefe cikin kuka tana cewa, "Ya yi fishi dani, ba laifin ka ba ne dole ka tsaneni." Ta sake fashewa da kuka tana cewa
"Na juya maka ba ya na cutar da kai,na cancanci duk wani hukunci yaya Mahmud.wallahi yanzu na yi nadama."
Ta sake 'kan'kame fulo tana kuka
kimanin minti biyar tana kuka tana tunanin Mahmud ta ji wayarta ta fara ringin
Cikin jajayen idanunta na kuka da dake ganin dishi-dishi taja wo wayar
Yadda idanunta suka nuna mata tai saurin share hawayen tana tashi zaune
"Yaya Mahmud." Ta fad'a da mamakin ganin kiranshi
Ta kara wayar a kunne tare da sallama
Bayan Mahmud ya amsa ta ce ,"Yaya fishi kake yi dani koh , dan Allah ka yi hakuri ka yafe min."
Wata karamar dariyar shi taji a can kasa kafin ya ce ,"Haba 'kanwata ni ban yi fishi dake ba , domin babu abin da kika min."
Ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce ,"Dan Allah yayana ka yafe min , nasan na yi maka ba daidai ba lokuta da yawa.".......
Ba tare data karasa maganar ba ya dakatar da ita yana cewa, "Hmmm Zainab ke nan to na yafe miki."
"To yaushe zaka zo."?
Ta yi tambayar tana ajiyar zuciya
Mahmud ya ce ," Zuwa kuma , ai gaskiya ba ranar zuwa domin ayyuka sun min yawan."
Cikin muryar shagwa'ba Zainab ta ce ,"Auu baka da lokacin masoyiyarka."
Mahmud yaji wani zummm da shaukin yadda ya yi maganar ya ce ,"Ai masoyiyar ba ta sona, har yau, hakan ya sa na mance da ita."
Zainab ta fara kukan shagwa'ba da yake jin sautin sa yana masa dadi tana cewa, "Wai Yaya ka dena sona koh."
Mahmud ya yi dariya sannan ya ce ,"Ina kika ta'ba jin Yaya ya ce ba ya son kanwarshi , ai har abada bazan dena san ki ba Zainab. "
Zainab ta ji dadin maganar matukar gaske cikin shaukin soyayyar shi ta ce ,"To idan haka ne ka zo kano ina jiranka. "
"Gaskiya babu lokacin Zainab."
Ya fad'a kai tsaye
"To gaskiya ni idan baka zo ba a cikin satin nan na yi fushi kuma rijiya zan fad'a."
Mahmud dariya ya kuma yi mata yana cewa, "Kanwatyna zan zo kinji na yi alkawari, amma ina Harun yake."
Wani yarrrr ta ji da kiran sunan Harun , baki daya sai ta koma sabon yanayi mara dadi .................
"Tun da Maryam ta rasu malam dai kun ga ba shi da lafiya,kuma hakan ya tsayar mana da karatu , gashi malam bai d'au mataki a kan shi wannan mutumin ba."
Wani daga cikin almajiran malam na lado mai suna Garzali yana karantawa sauran gardawan su uku abokan karatun shi .
Wani mai suna Allaro ne ya ce ,"Ai wallahi ko ni bazan yafe masa ba ."
Nazifi ne ya kalli Musa yana cewa, "Kaji su , to ai ba ido zamu zuba ba , tun da aunty Maryam ta rasu shi wanda ya kashe tan ma ko gaisuwa bai zo ba ."
Garzali ya ce ,"Ai wallahi da munsan inda zamu ganshi sai ya gane ba shi da hankali, sai mun masa shegen duka wallahi. "
Musa ya ce ,"Allah sarki aunty Maryam. Allah ya sa kin huta Allah ya jikanki ."..
Harun yana jin jita jitar Allah ya yi wa Maryam rasuwa sai dai bai yadda ba domin bai samu tabbaci ba .
Malam na lado ne kwance a daki cikin zazzabi
Matarshi ta zauna kusa dashi tana cewa, "Malam yanzu babu abin da zaka yi wa wannan yaron Haruna , kai fa malami ne ko yanzu yana daga d'aki zaka iya kashe shi , amma ka ki aikata komai akai , ka ki daukar mana fansa ."
Ta yi maganar cikin ciwo da matukar damuwar rashin 'yar ta .
Share, comment and like ................................📚
Gubar Rayuwata⚡🌹
By
Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)
Editing❌
________________________________________
Page 45 & 46
Malam na lado ya kalli matarshi tare da cewa , "Ubangiji Allah shi ne mai rayawa da kashewa haka ya kaddarowa Maryam rayuwarta , ke ma ina baki shawara ki fawwalawa Allah komai, domin ni na bar shi da Allah, a ranar gobe su tsaya da Maryam su yi Shari'a dan haka babu abin da zan yi a kai wannan shari'ar sai a lahira ."
Ta fashe da kuka tana cewa, "Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un Allah ya jikan ki Maryam."
Malam ya yi ajiyar zuciya.
Bayan alkali ya yi rubutu ya ci gaba da sauraran lauyoyi duk kan shaidun lauyansu Umar sun gamsar da kotu , sannan Sahid ya gabatar da wannan kadarori
Daga bisani ne alkali ya du'kufa yana rubutu ,
Yayin da kotu ta yi shiru , lauyoyi suna tattaunawa kowa yana jiran hukuncin da kotu zata yankewa Sahid
Bayan alkali ya gama rubutu ya d'ago ya fara gabatar da hukunci ..........
Ana fitowa daga kotu Nabila ta fara kiran wayar Umar, domin tana son sanar dashi irin nasarar da suka samu a kotu amma bai dauki kiran ba
Haka suka tafi gida suna ta murna da farin ciki ,har da su baba Garba wanda bayan sun koma gida ya wuce 'kauye cikin farin ciki .
Bayan wani lokaci ne Umar ya biyo kiran Nabila, nan suke sanar dashi irin nasarar da akai .
Ya yi matukar farin ciki sosai da sosai
"Mama Allah ya sa mu dace Allah ya jikan baban mu , kin ga ita gaskiya ba ta 'ya'ya yanzu ga shi Sahid ya rasa komai sai gidan bursun aka tura shi."
Jibril ya karasa maganar yana kallon mahaifiyarshi
Mahaifiyarshi ta yi ajiyar zuciya tana cewa, "Farin ciki na kawai yaran nan an mayar musu da dukiyarsu, shi kuma da aka tura shi kurkuku Allah ya shirye shi , Allah ya sa mu dace."
Jibril ya ce ,"Amen mama."
Su Garzali ne zaune suna karatu , Musa ya fado kansu cikin gudu yana haki
Allaro ne cikin fargaba ya tambaya, "Mene ya ke faruwa jikin malam d'in ne."?
Musa cikin wata murya kamar yana barbara ya ce ," Ku taso muje ga wanda ya sanadin mutuwar aunty Maryam can na ganshi a bayan layi."
Garzali ya ce ,"To mene zami masa kada malam ya sani fa.'
Musa ya ce ,"Babu yadda za ai ya sani kawai ku taho."
Suka shiga suka d'e'bo sanduna suka fita da gudu
Sauran almajiran 'kolawa suna kallon su .
Da gudu suka nufi inda Harun ya ke yana tare da motar shi a kofar wani gida
kafin ya an kara ya fara jin saukar duka ta ko'ina, ya fara ihu , dukanshi suke dauu dauu dass dasss har ya kai kasa ba su dena dukanshi ba har suka fara fasa masa jiki , ganin ya kai kasa ba ya motsi
Musa ya ce ,"Ku taho mu tafi mu bar maye anan."
Garzali ya d'aga sanda ya makawa gilass din motar na baya sannan ya sake 'kwalawa Harun sanda suka gudu.
Buja-buja suka koma gida alamun su duk mara sa gaskiya
"To idan ya mutu fa .Ya zami mun kashe rai."
Allaro ya yi maganar yana kallon su