← Book details Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 22

Sashe 17

Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba tare da sun ce komai ba suka dauko shi su su hudu , biyu sun rike hannaye , biyu sun rike kafafu .

Haka suka fito suka wurgo Uncle waje

"Kan uban can dama har yau wannan yana nan , to Allah ya kuma tonaki ."

Abdul ya karasa maganar yana kallon Uncle da yaji wurgi yana kwance a kasa

Suka rufe gidan suka hau mota sukai tafiyarsu .

Cikin mummunan takaici Fa'iza ta fara tattara kayan da aka watso mata , waje guda ta had'a su tana kallon tare da tunanin sauran kayan dake ciki, a cikin ranta ta lissafa yadda zata dauki kayan a hannunta ba tare dasun mata yawa ba .

A lokacin kuma hankalinta ya kai ga uncle yahaya da yake zararar da hawaye .
Wanda sa'ilin ta kuma kula da yadda gari ke rugugi sakamakon had'owar hadari .

Had'e rai ta yi tana kallon Uncle tare da matsawa kusa dashi tana cewa "Ni zan tafi , domin babu inda nake dashi bare na je dakai ."

Cikin tashin hankali Uncle yahaya ya zaro idanunsa ya fara magana a yanayin wahala.
"Ya za ai ki barni a nan Fa'iza, ga hadari , ina zan sa kaina , ban zata zaki mini haka ba."

Ajiyar zuciya ta yi sannan ta ce ,"Ka so gaskiya mana Yahaya ina ne zan kai ka , dama kowa yana da kaddarar shi , to ka dauki wannan matsayin abin da ba za ka ta'ba mancewa ba , shi ne Gubar Rayuwarka."

Tana gama magana ta juya da sauri tana kwashe kayanta , sakamakon tsawa da iska da aka fara.

Ba tare da ta ko kalli Yahaya ba tasa kai cikin sauri ta fara tafiya, sakin baki ya yi yana kallonta cikin mamaki ganin cewa da gaske fa tafiya ta yi ta barshi .

Wasu hawaye ne suka zubo masa yayin da ya fara ba za idanu da nufin neman wani ya taimake shi , amma babu wanda ya gani sai wani yaro dake gudu a keke sakamakon yayyafin da aka fara .

"Yanzu ya zan yi , wallahi da nasan abin da zai faru ke nan bazan zo legos ba , basu da mutunci yanzu sai su kone ni a gun nan ." Uncle cikin kuka ya sauke maganar yayin da aka tsuge da ruwan sama .Domin ko ita Fa'iza kafin taje inda zata wannan ruwan ya dake ta , bare Uncle naku dake guri daya.

Yau tun da gari ya waye Maryam take murna da fitar da zasi da Harun , mahaifiyar ta kawai ta sanar wa da wannan labarin , domin ta san malam na lado mahaifinta idan ya ji bazai yadda da wannan shirme ba ,

A tsakanin uwa da 'yah haka sukai maganar su , nan ta ba ta goyon baya tare da umarnin karta jima har Mlm ya tambaye ta.

Doya da kwai take soyawa , daga gefe kuma kana iya hangar wani kunu na gero wanda yasha kayan kamshi.

"Wai Nabila har yanzu ba a gama girki ba yunwa fa nake ji nasan ita ma Baba haka ."

Jafar ya shigo madafa yana wa Nabila maganar cikin mita ,

"Hmmm ." Kawai abin da Nabila ta iya fad'a ke nan

Jafar ba tare da hakan ya dameshi ba ya sake cewa "Kin san dai yau ne Yaya Umar ya ce zai kawo 'kannenshi ko , to ki musu girki dan Allah."

Ta kalleshi tana cewa, "Ban fa mance ba Yaya Jafar."

Ya karaso yana daukar doyar da zummar d'and'anawa.

Bayan Harun ya iso
ba 'ba ta lokaci Maryam ta fita suka tafi

"Ya kamata mu biya ki gaida momy na fa." Harun ya yi maganar yana kallon Maryam

Cikin shagwa'ba Maryam ta kalleshi tana cewa.

Share , like and comment......................📚

Gubar Rayuwata⚡🌹

By
Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)

Editing❌

________________________________________

Page 37 & 38

"Amma gaskiya ba za mu dad'e ba."

Harun wani dad'i yaji ya rufe shi dajin amincewarta , hakan ya sa ya ce ,"Haba sarauniyata yadda ki ke so ai haka za ai besty na." Cikin 'kwarewa da farin ciki ya cigaba da tuki ya nufi gidan da yake kiran gidansu.

Wani gida ne babba suka shiga , Harun yana mata kalamai masu kwantar da zuciya har suka shiga cikin falo.

Maryam dakatawa tai cakk , sakamakon duhun da ta gani a cikin falon , saida Harun ya kunna haske sannan ta ji hankalinta ya kwanta .

"Duk kin wani furgita zauna mana baby bari shaf-shaf na shiga ciki na kira momy."
Harun ya yi maganar yana shige wa ciki.

Nabila kam tasha aiki sosai ta yi girke girke , duk saboda 'kannen Umar da zasu kawo musu ziyara .

Wajen minti biyar Harun ya yi bai fito daga dakin ba ,

Hakan ya sa Maryam ta yi shiru tana sa'ke-sa'ke cikin zuciyar ta

ba ta gama tunanin abin da ya rike su a ciki ba , sai ga Harun ya shigo jikinshi duk a mace ."Mene kuma ya faru."?

Maryam ta yi maganar tare da tashi tsaye

"Ina shiga ciki, na ga momy kwance wallahi hawan jininta ya tashi."
Inji Harun

"Subhanallahi." Maryam ta fad'a

"Amma karki damu , ki shiga ciki ki kula da ita dan Allah, ki kula min da mahaifiyata zan kira likita."

Da sauri Maryam ta fad'a dakin cikin tausayin Harun.

Duhu ta kuma gani cikin dakin , amma ba tare da ta nemi inda glove yake ba , ta nufi gadon wanda tana iya ganin mutum a kudundune a kai.
"Mama , Mama." Tana ta'ba mahaifiyar Harun tana kiran sunanta .

Wani tashin hankali ne ya bigi zuciyar Maryam tare da tsoro , sakamakon yadda taji tulin kayan Harun ne a kan gadon ba wai mahaifiyar shi ba ce .

Da firgici ta tashi tana shirin fitowa taji an rike ta.

"Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un." Maryam ta fad'a sa'ilin da take da tabbacin Harun ne a gabanta

Dauuuuuu ya kunna glove din dakin yayin da yake rike da hannunta yana dariya.

A yadda mamaki ya kasheta ne ya sa ta kasa cewa komai, zuciyar ta tamkar ta fito musamman jin yadda ya fara magana.

"Kin ga yadda shiri na ya yi koh. Ga ki gare ni yau Maryam zaki ga irin san da nake muki , babu kowa a gidan nan daga ni sai ke yawan."
Ya karasa maganar yana fincike mayafin dake jikinta .

"Inna'ilaihir wa inna'ilaihir raji'un Harun , kaji tsoron Allah, na roke ka karka rabani da mutunci na , dan Allah." Cikin matukar kuka da firgici Maryam ta yi magana.

Dariya ya yi yana cewa ,"Haba Maryam, karki zama yarinya mana , wallahi tun lokacin da nake zuwa wajenki Wannan ranar nake jira , ban samu Zainab ba , domin na so mu shiga irin wannan yanayin da ita ,amma shegen yayan ta Mahmud ya hana."....

"Dan Allah Harun kar ka cutar dani, wallahi bazan jure ba."

Ya tunkud'eta ta fad'a kan gadon , haka har mai faruwa ta faru .
Sannan Harun yaji dadin rayuwar shi .

Bayansu su Umar sun shigo suka zauna a falo nan suka fara hira dasu Jafar da baba anje

Ya yin da Nabila ta fito daga wanka tana shiryawa.

Da siririyar murya kanwar Umar Salma , wacce take kusa da yayanta Nasir ta ce ,"Wai ina Nabilan ne to."?

Jafar ya ce ,"Ta na zuwa yanzu. "

Nabila ta karaso cikin falon sanye da wata doguwar riga abaya , wacce taji ado ga launi mai matukar kyau.

Tun daga 'bullowarta Nasir ya kasa jire idanunshi a kanta , har ta karaso ta zauna

"Ya ya Umar har kun zo."? Nabila ta yi maganar da Umar yayin da kuma ta ke kallon Nasir da Salma

" Kanwata mun iso, yau dai ga salma nan." Ya yi maganar yana nunawa Nabila kanwar shi .

Murmushi Nabila ta yi tana cewa, "Eh yayana ka cika alkawari kuma naji dadi."

Nasir ne ya 'ba ta rai yana kallon Umar da cewa ,"Haba Yaya Umar to ni ba za a gabatar dani ba."

Jin hakan ya sa kowa ya kalleshi suna masa Murmushi.

Umar tsaki ya yi yana cewa, "Nabila wannan matumburin kanina ne sunan shi Nasir."

"Haba Yaya Umar matumburi kuma." Nasir yayi maganar yana kallon shi .

Dariya suka kwashe da ita baki dayansu har da Umar yayin da ya ce ,"Ai Nasir din ne ya cika zance wallahi. "

Nasir ya kalli Nabila yana cewa ,"Baki gabatar mana da kanki ba sister. "

Cikin haushi Umar ya Had'e rai yana cewa, "Kun ji ba , baka ji an ce Nabila sunanta ba ,banan surutu bama kasan mene za ka na tambaya ba."

Dariya suka kuma yi wacce tafi ta d'azu , har ita Nabilan ya yin da Nasir yake kallon yadda dariya take mata kyau.

Sannan ta tashi ta nufi dakin girki domin kawo musu abinci , Nasir harda lekenta .

Lomar farko ta Nasir ya ce ,"Gaskiya Nabila kin iya girki sosai , sai ka ce a Australia. "

Wata harara Umar ya watsa masa tare da cewa ,"Su Australian girki suka iya? dan Allah ka yi hakuri ka yi shiru haba."

Dariya suka sake yi a karo na ba adadi
haka suka gama cin abincin cikin farin ciki da walwala .

Bayan su kammala suka tashi tafiya, nan ne Nasir ya karbi number Nabila sannan suka yi sallama. Sun matukar jin dadin wannan ziyara baki dayansu."

Fa'iza a gidan kawarta ta samu guri , inda ta tabbatar wa da kawarta zuwa gobe zata koma garinsu .

Tana tsakar gida a zaune ta yi tagumi , a lokacin ne wannan kawarta ta ta fito daga daki .

yadda ta ga Fa'iza ta yi tagumi tana kallon taurarin dake sama ya sa
kawarta cewa ,"Haba Fa'iza lafiya , kin zauna a farin wata kuma kina kallon sama ."

Fa'iza ta yi ajiyar zuciya tare da cire hannu daga tagumin da ta yi
"Ki dena damun kanki fa dan Allah." Cewar kawarta

Ajiyar zuciya Fa'iza ta kuma yi tana cewa, "A kwai abin da ban fad'a miki ba kawata, kuma nasan yanzu duk wannan ruwan saman da akai ga dare yana kwance a wajen nan."

"Topha waye ke nan." Cewar kawarta
Chapter 17 · 0% Book details