← Book details Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 22

Sashe 3

Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dogon tsaki Uncle Yahaya yaja yana cewa, "Dama dai sona take da gaske shi ne , amma kana ji fa , wai gayyatata take na kwana a d'akinta fa."

Kafin ya rufe baki ya hangota tana tahowa inda suke kawai Uncle Yahaya ya juyar da kanshi yana tsaki ,

hakan yasa Shu'aibu kallon inda take yana sakin baki , riga da wando tasa wanda suka kama jikinta sosai , tun daga nesa Shu'aibu yake jin kamar ya rungumota , bari ma lokacin data 'karaso bada ban ya daure ba da Fa'iza taji wani abu😂.

,"Haba Yahaya, sai ne manka nake a cikin garin nan ."

Uncle Yahaya ya yi mata shiru ko kallonta bai ba , ta sake cewa, "Na yi maka girki jazo muje ."
Kallon wayarta tai dake hannunta sakamakon kiran da ya shigo, Abdul Salim , kawai ta kashe wayar tana cewa, "Da kai fa nake magana Yahaya."

Uncle Yahaya yaja dogon tsaki yana cewa, "Ke ni fa babu inda zani , baza ki ta'ba samun abin da ki ke so ba , kawai dan kinga kirjinki dam -dam shi ne za ki tunanin za ki rud'eni."
Ya sake jan dogon tsaki ya bar waje , shi kuwa Shu'aibu ya tsaya yana kallonta dama shi ne .

Fa'iza cikin ranta tace, "To wallahi matukar na cika karuwai gaske sai na jawo Yahaya jikina, mu zuba mu gani ." A'a ni ko na ce Allah ya ba mai rabo sa'a .

Uncle Yahaya a yau ya shirya ya baro legos, lokacin da dare ya yi tazo ta sami Shu'aibu, yake tabbatar mata da Uncle Yahaya ya koma Kano , aiko ta yi takaici , kawai ta amshi numbarsa ta koma.

Zainab da Mahmud ne a kan hanyarsu ta zuwa asubiti, Mah.mud ya kalli Zainab wanda duk hankalinta yake kan had'uwarsu da Harun yana cewa, "Kin san wazan dubu ."

Zainab tace, "A'a Yaya Mahmud."

Mahmud ya jawo hannunta ya ri'ke , hakan yasa Zainab tsayawa tana kallonshi , shi ma ya kalleta yana cewa, "A haka zamu taafi."

Tai ajiyar zuciya suka ci gaba da tafiya badan taso ba .

Sisters kar a manta comment dina a private za a ajen.

Share , like and comment.........📚

Gubar Rayuwata⚡🌹

By

Fatima Abdallaah kano
( Autar marubuta )

_________________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><

Page 5&6

Shigarsu asubitin ke nan Mahmud ya saki hannun Zainab yana nuna mata guri yace ta zauna ta jirashi .

Tsayawa tai tana kallon shi , yayin dashi kuma ya shige d'akin gwajin cuta mai karya garkuwa jiki ,

Zainab hankalinta ya sake tashi ta kasa zama tanata sake-sake a ranta har Mahmud ya fito tasha gabansa da sauri tana cewa, "Wai me yake faruwa? mene ne ka yo a ciki , nifa ka fara bani tsoro ."

Mahmud ya yi murmushi yana cewa, "Babu komai kawai ki taho."
yasa kai ya fita waje yana cewa, "Harun zan kasheka."

Zainab sauri tai tasha gabansa tana cewa, "Ni gaskiya yaya ka fad'a mini abin dake faruwa."

Mahmud ya yi ajiyar zuciya yana cewa, "Budurwata ce Maryam, ake jita-jitar tana da HIV, kuma an tabbatar mini da anan take ansar magani, a halin yanzu ina cikin mummunan yanayi, na ro'ki alfarma a bincika mini , sun ce kuma zasu kirani ."
Ya kauda kanshi yana cewa, "Harun idan tana da wannan cutar zan kasheka ." Cikin tsananin fusata ya yi maganar har saida idanunsa ya yi jah , Zainab ta kalleshi tana cewa, "Yaya kamar kana magana ko gaskiya kana cikin damuwa."

Mahmud yace ,"A'a ba komai mu tafi kawai ." Suka d'auko hanya

Bayan sun zo gida 1:25 hakan yasa Zainab ta kaici rashin samun da mar fita , kafin ta Zauna Harun ya turo mata sa'ko cewa zai zo har gidansu wani lokacin.
Bayan Mahmud ya koma bai sanar da Ahmad komai ba, a kan zan cen Harun , amma abin yana matukar cinsa.

Alaji Idris kuma yana 'ko'karin fara azumi , wanda fad'ar Allah ce domin yaron da ya kad'e ya rasu .
Kakar yaron mai suna Baba anje a halin yanzu ta dawo gidan Alaji Idris da rayuwa, har zuwa lokacin da Allah zai raba , bayan haka ta sanarwa da Alaji Idris cewa bata bukatar diyyar yaron kawai Allah yasa mai ceto ne .

A halin yanzu Harun ya sami labarin zuwan Mahmud, hakan yasa yake Shankar zuwa gidan .

Yana zaune daga cikin harabar gidan ganin fuskarshi kawai zaka gane yana cikin damuwa, Zainab ce ta zo tana kiran sunanshi hakan yasa Mahmud d'ago kai yana kallonta da murmushi

"Haba Yaya ka yi hakuri da tunani , to Yanzu tun ba a sanar maka tana da cutar ba kana haka , idan aka fad'a fa."

Mahmud ya kalleta yayin da yake tuna tsohuwar soyayyar su yana cewa, "Mene kuwa ai ke zan aura ."
Saukar maganar taji kawai a kunnuwanta Zainab tasa idanunta cikin nashi tana kallon shi,

"Kina mamaki ne ."? Ya fad'a yana kallonta

Kawai ta juya ta shige cikin gida , Mahmud yana cewa," ko da Maryam ko ba Maryam kaunarki a cikin jinina take kuma bazan sarara b."

.
Uncle Yahaya ne zaune cikin staff room a cikin makaranta babu abin da yake sakamakon a halin yanzu d'alubai sun fito break.

Wayarshi ce ta fara ringing ya kalli wayar a sa'ilin da ya ga ba suna, d'auka ya yi yana karawa a kunnensa yana cewa, "Hello."
Daga can 'bangaren yaji wata siririyar murya mai cike da yaudara ana cewa, "Hi Yahaya daga legos ne ."

Wani fargaba yaji da tashin hankali sun ziyarce shi , hakan yasa shi ajiyar zuciya yana cewa, "Wai ke wacce irin ce ne."

Ajiyar zuciya Fa'iza ta yi tana cewa, "Haba Yahaya, wai mene laifin mai son ka ne , wai duk irin abin da nake ma ka'ki yadda dani mene haka to."

Uncle Yahaya yaja dogon tsaki yana cewa, "Tukun nama waye ya baki number har za ki kirani."

cewa tai ,"Uhum to number ka ai bata da wahala kamar yadda zan taho kano kwanannan."

Zaro idanu ya yi yana cewa, "me za ki zo yi a kano bana san shirme."

Fa'iza tai dariya tana cewa, "To waye nake dashi a kano , gurinka zanzo mana ."

Kawai ya kashe wayar yana tsaki

Ya lalu'bo takardar da Laila ta kawo masa yana karantawa, kamalan soyayya masu dad'i da suka ja hankalinsa sosai kuma yaji sun fi na kullum dad'i hakan yasa ya yi godiya ga Allah.

Yau Alaji Idris ya gudanar da azuminsa na goma ,aiko saiga Garba d'an uwanshj ya zo masa da labarin an sace masa mota ,

nan Alaji Idris ya ba shi hakuri yace masa insha Allah yana gama azumi zai siya masa sabuwar mota ya cigaba da sana'arsa, aiko Garba harda kukan farin ciki da matukar ganin girman Alaji.

Lokacin da Alaji Idris ya ci dabino da ruwan shayi ne ya zauna ya yi tagumi,
Hajjiya Maryam data shigo ta kalli Alajin tana cewa,"Lafiya kuwa Alaji. "

Ko motsawa baiyi ba ga dukkan alamu bai san tana yi ba ,"Alaji lafiya. ".

Ta sake fad'e matsawa tai tana shafa fuskarshi hakan yasa Alaji Idris ya dawo hayyacinsa ,

Kauda kai ta yi tana cewa," Innalillahi , wai ya haka ne Alaji, kana sawa kanka damuwa ."

Ajiyar zuciya ya yi yana tashi tsaye yana cewa, "Wallahi Hajjiya yadda mahassada suke nuna mana 'kiyayya shi ne damuwata , kawai dan Allah ya fifita mu a cikinsu ."

Hajjiya Maryam ta kama hannun Alaji Idris tana cewa, "A kullum ina fad'a ma , addu'ar da muke yi , ita ce Allah yake hanasu yi maka wasu abubuwan , mu da muke da Allah, Wallahi duk sharrinsu a kan zu zai tattare , kawai addu'a zamu cigaba da yi."

Alaji ya girgiza mata kai alamun yaji dad'in zancen ta yana cewa, "Gaskiya ne."

Kalisa ce ta shigo ta katse su da cewa ,"Momy Dady , abinci ya kammala ku taho ."

Alaji ne ya kalleta cikin kauna yana cewa, "Tom Kalisa Yanzu zamu taho."

Matsowa ta sake yi tana cewa, "Haba Dady tsawon yini fa kana azumi, kuma babu abin da kaci , ka dena biyewa momy ka taho mu tafi ." Ta ja masa hannu ya bita suka fita yana yiwa Hajjiya Maryam murmushi. Ita ma murmushi tai ta bi bayansu.

Duk sun zazzauna su baba anje , Nabila, Jafar , Alaji na fitowa gun kawai duk suka d'auke wuta kowa ya yi shiru , su Hajjiya Maryam su ma suka zauna , aka fara cin abinci amma abin mamaki da tambaya kowa shuru ya yi kamar wanda aka aikowa da mutuwa , jikinsu duk kasala ta ziyarcesa bayan sun gama cin abinci
sai aka fara kallon-kallo ba tare da kowa ya bar wajen ba .

Alaji Idris ne ya bud'i baki yana cewa, "Kalisa gobe ki sanar da Sahid ina san ganinshi."

Wani fad'uwar gaba taji ba zato ta shiga yanayi tana tunanin ba dai dady zai maganar aure ba .

"Kalisa ba ki ji mene na ce ba ne ".
Alaji ya fad'a

Da sauri ta kalleshi tana cewa," Naji dady ."

Sannan ya d'auke kai a gunta yana cewa, " Idan Allah ya kaimu gobe ,ina son magana da kowa da me nan bayan kun yi break fast. "

Maganar suka ji wani iri harsun fara tunanin meke damun Alaji yau .

Kawai ya tashi ya nufi d'akinsa , Hajjiya Maryam ajiyar zuciya tai tana binshi da kallo

Nabila ce ta kalli Jafar tana cewa, "Mene dady zai fad'a mana gobe , nifa har na fara jin tsoro ."

Baba Anje tace ,"Too Allah masani ku bari goben ta yi , Allah ya kai mu , mu kuma ji alheri."

Suka ce ,"Amin."

Washe gari da safe Aminu ya fara shirya kayansa domin komawa Adamawa inda yake karatu , bayan ya shirya kayanshi tsaf
Hajjiya da Alaji Kabiru suka fito sukai sallama har Alaji ya ba shi wasu kud'i

Sai Ahmad da Mahmud suka d'auki kayansa domin rakashi
Chapter 3 · 0% Book details