← Book details Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 20

Sashe 9

Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wannan lokaci Zarah ta fito daga dakinta, sanye da rigar likitoci da jakah a hannunta

Fatima tana ganin haka ta kauda kai tana dariya

Zarah tana kula da hakan ta yi murmushi, kana ta ce da Kamal.

"Zan tafi saida safe."

Kamal ya d'ago yana cewa.

"Ohhh kina da night ko , to Allah ya tsare hanya."

"Mene kike mini dariya."?

Zarah ta tambayi Fatima

Fatima ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce .

" Shi kin ga aikina babu fitar dare , ga shi zaki barni da Kamal a gidan ." Fatima ta yi maganar cikin son cusawa Zarah kishi

Zarah ta kauda kai , kawai ta fice cikin haushi

Kamal ya kalli Fatima yana cewa.
"Data kula ki baza ta tafi yanzu ba , ga shi ta samawa kanta samala ."

Dariya Fatima ta yi sannan ta ce .

"Wallahi ba 'kin kulani tai ba , nasan zata rama ne ."

Kamal ya ce .

"Wato Fatima ina alfahari daku ina san ku fiye da komai .
Amma wannan kace-nace d'in tsakaninku Allah ya nunan ranar dena shi ."

Fatima ta yi dariya.

Wasu kwanaki

Nasir da Kamal suna zaune suna kallo , Zarah kam tana duba wasu takardu
Babu sautin da ake ji saina gidan TV da suke kallo

Fatima ce ta turo kofa sanye da kayan lauyoyi da bakar jakarta ta gun aiki .
Cikin matukar far'a a tare da ita ta ce .

"Assalamu alaikum wanda nafi kauna a duniya ta ."

Jin hakan ya sa duk suka d'ago suna kallonta

Kamal ne ya fara murmushi yana cewa.
"Ga dukkan alamu an gama shari'a cikin nasara ."

Fatima ta saki wani murmushi ta samu guri ta zauna

Fatima ta kalli Kamal tana cewa .

"Wannan gaskiya ne dear ."

Sannan ta kalli Zarah cikin wannan farin cikin dai tana cewa .

"Wato Zarah yau na kammala shari'a cikin nasara ,kar ki ga yadda komai ya yi daidai a kotu , farin ciki matuka, zan so a ce kin shiga kotun an yi a gaban ki ."

Zarah ta tabe baki sannan ta ce cikin yaren turanci.
"Na ta ya ki murna ."

Sannan ta juya harshe zuwa Hausa ta cigaba da cewa .

"Allah kar ya nunan ranar da zan shiga kotu a rayuwata, domin bani da lokacin ta ."

Fatima ta yi dariya

Nasir ya ce .

"Aunty Fatima ni kam zan so watarana ki gayya ce ni kotu , nasan in dai ke ce zaki karbi shari'a to tabbas dole a sara miki ."

Fatima ta yi murmushi sannan ta ce da Nasir.

"Kar ka damu akwai wata shari'ar ma ."

Kamal ya ce .

"Naji dadin nasarar ki sosai ."

Ta yi masa murmushi.

Fatima ta ce .

"Ya Allah na gode maka da wannan nasarori da kake jaraftata dasu ."

Zarah ta kalleta yayin da suka hada ido , ta kauda kanta .

Wayar Nasir ce ta fara ringin , ya yi sauri ya katse ta , aka sake kira ya yi sauri ya kuma kashewa .

Kamal ya jefa masa wani kallon zargi , Nasir ya yi masa murmushin ya'ke

Bayan minti guda ya ji shigowar sako wayarshi .

"Ka fi to ina waje ."
Abin da aka turo ke nan

Ya yi ajiyar zuciya ta bacin rai ya tashi ya fita waje . Yayin da Kamal yake binshi da kallo

Fatima tana ta duba wani abu cikin fayil tana murmushi,
Ita ma Zarah ta na aikinta .
Nasir yana fita
Ya ci karo da Abba Alaji.

Cikin mummunan bacin rai Nasir ya fara masa magans .

"Wai kai uban mene kake bukata ne Abba , wallahi ka rabu dani abotar an dena ka rabu dani mana ."

Abba Alaji ya ce .

"Haba Nasir ni ne fa , zuwa na yi mu gaisa , wai waye ya shiga tsakanin mu ne ."

Nasir ya ce .

"Wallahi ka kiyaye ni , babu ni ba kai , kai matsala ne mai haddasa annoba , duk sanda na fara samun nasara kana nufoni komai ya ke lalacewa .

Wallahi ka kuma kirana ,ai yaya Kamal yana falo ka cigaba ."

Yana gama magana ya koma ciki bai jira cewar komai daga Abba ba .

Cikin wata fuska ta rashin gaskiya ya koma ciki , a wannan lokacin dai Kamal yana masa wani kallo , har ya zauna , amma Allah bai nufe shi da ya furta komai ba .

Fatima ta rufe fayil din da take dubawa , lokaci guda kuma tana kai idonta kan TV

Nasir cikin son Kamal ya dena masa kallon zargi ya ce .

"Bikin laila fa ya zo .Ga shi ban fara aiki ba ."

A lokacin kamal ya yi murmushi sannan ya ce .

"Ai kai ne ka yi wa kanka , da tuni kana aikinka , yanzu ma idan ka yi wasa da damar ka babu abin da zan iya maka .

To mene idan ka fara aikin mene zaka mata kake wani zance."

Nasir ya sosa kanshi , sannan ya ce .

"Wallahi yaya Kamal mota nake son siya ."

Zarah ta d'ago kai ta ce .

"In sha Allah nima kafin bikin zan canja mota ."

Fatima ta ce .

"Canza mota ai dole ne nima ."

Kamal ya ce ."Ai akwai motoci masu kyau wajen Alaji Mamman sai ku samu a can kawai ."

Zarah ta ce ."Eh tabbas akwai motoci masu kyau a gun shi , can zamu je ."

Fatima ta bata rai jin yadda Zarah ta yabi motors din

Sannan ta ce .

"A'a ni gaskiya bazan se mota a can ba , babbar motarshi bata wuce million 5 ba , dan haka bazan siya a can ba ."

Ita ma Zarah ranta ya baci yadda taji Fatima na magana

"Me kike nufi Fatima."?

Fatima ta ce .

" Ina da kudin da zan se motar sama da million 5 don haka bazan siya anan ba , ba karama nake so ba ."

Zarah ta rufe takardun dake hannunta ta aje su gefe sannan ta fara magana .

"Ke kin san ina da kudin da zan se motar da baki isa ki hau ta ba , kin sanni kin san mahaifina, kinsan yadda na yi suna a harkar rubutu , to ki tabbatar dole kina baya na ."

Nasir ya zuba kunne cikin mamaki yana kallonsu

Yayin da ran Kamal ya matukar baci dajin abin da suke

Fatima ta yi murmushi na kasaita kafin ta ce .

"Kwarai kuwa nasan mahaifinki yayi suna , amma ina tabbatar miki ba zai nuna maka kudi ba , sanin kan ki ne su waye iyayena , mahaifiyata tana saudiya , tare da yayannina , kuma ina mai tabbatar miki komai kudin ku , baza ku fimu ba , kuma ina da darajar da zan shiga wani guri , wallahi baki isa ki shige shi ba ."

Zarah ta ce.
"To shi ke nan , mu zuba ni dake muga wanda zai se motar da tafi karfin wani ."

Kamal ne ya tashi tsaye tare da daka musu wata tsawa yana cewa.

"Wannan wanne irin hauka ne ."

Duk suka sha jinin jikinsu

Autar Marubuta
07040805269
Ku ne meni a WhatsApp

FATIMA DA ZARAH🎀

Na
Autar Marubuta

________________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><
><><><>🌹<><

Editing❌

Page 22 & 23

Kamal cikin fushi da bacin rai ya cigaba da cewa .

"Kuna son nuna wa duniya ilmin ku , duk na banza ne ke nan , na yi muku shiru tsawon lokaci, amma abin naku gaba yake yi ,

Mene amfanin hakan , almubazzaranci daidai ne ?

To wallahi duk wacce baza ta hau motar kasa da million 7 ba , duk na haramta muku siye , aikin banza , wallahi zan yi maganinku ."

Ya wuce ya futa waje ya bar musu gidan .

Nasir ma ya yi ajiyar zuciya , ya tashi ya nufi dakinshi .

Fatima ce kawai a cikin gidan , sakamakon Kamal yana company tare da Nasir.
Zarah kuma tana wajen taron karawa wani marubucin abikinta girma .

Yau babu wanda yake da aiki a cikin gidan .

Gama girkinta ke nan , Fatima ta d'auka wayarta don ganin meke faruwa a duniya .
Sallama taji ana yo wa amma an kasa shigowa jin muryar mace ce ya sa ta fadin .

"Shi go ."

Hajjiya Sa'adatu ce ta fara shigowa sannan Mahmud da Umar suka biyo bayanta .

Murmushi na farin ciki Fatima ta saki , tai saurin tashi tana taro su .

"Oyoyo mommy sannu ku da zuwa ."

Su ma su mommy murmushi sukai mata , ta musu iso suka zauna

Bayan sun gaisa

Fatima take cewa .

"Mommy bari na kawo muku abinci domin yanzu na gama shi ."

Bata jira sun ce komai ba ta nufi dakin kirki .

Mahmud ne ya kalli mahaifiyar su hajjiya Sa'adatu yana cewa.

"Masha Allah mommy, suna zaune lafiya ."

Murmushi hajjiya ta yi sannan ta ce .

"Ai dama haka ake so ."

A lokacin fatima da murmushi ta kawo abinci, ta koma ta kawo lemo da ruwa .

"Tom mommy ga abinci, nasan wata kila kafin ku gama Zarah zata iya dawowa ."

Hajjiya Sa'adatu ta kalli Fatima sannan ta ce.
"Au bata nan ."

Fatima ta ce .

"Eh taje wani taro , amma bari ma na kirata ."

Ta dauki wayarta tana kokarin kiran lambar Zarah

Kafin ta kira ne hajjiya Sa'adatu ta ce .

"Ba sai kin kirata ba Fatima, ai dama lafiyarku muka zo gani , idan ta dawo kafin mu tafi sai mu gaisa ai ."

Fatima ta yi murmushi tana cewa.

"Wallahi mommy da an kirata ."

"Ba sai kin kirata ba wallahi Fatima." Cewar Hajjiya

Fatima badan taso ba , ta fasa kiran Zarah.

Bayan su Hajjiya sun gama cin abinci ne , suka fara shirin sallah da zummar idan Zarah bata dawo ba , zasu koma

A wannan lokacin ne ta ji ana kwankwaso kofar falon

Ta tashi ta nufi kofar tare da bud'e ta
Chapter 9 · 0% Book details