← Book details Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 20

Sashe 10

Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani ihu ta kwalla ta rungume wanda ya fara shigowa wato mai sanye da kayan turawa wato Ahmad

Sannan cikin farin ciki ta sake rungume dayan wanda shi ne Najib

"Haba matsala dake ke nan 'yar Nigerian nan idan kin yi kewar mutane baki iya hakuri ba ." Ahmad ya fada cikin farin ciki yana sake shigowa cikin gidan , lokaci guda kuma yana hango su Hajjiya Sa'adatu a zaune

"Wayyo Allah gaskiya kun yi mini zuwan ba zata Yaya ."

Ta yi magna cikin shagwaba da matukar shaukin kaunar su .

Suka nufo inda su Hajjiya suke zaune domin samun masauki

Hajjiya ta kalli Umar tana cewa.
"Su waye kuma su ."

Umar ya ce .
"Wallahi ban sani ba mommy."

Bayan sun zauna lokacin da Hajjiya ta kare musu kallo tabbas tana iya ganin kamanninsu da Fatima.

Hakan ya sa ta saki fuska da jiki suka gaisa cikin girmamawa

Bayan sun gaisa ne Fatima cikin wannan fatin cikin ta kalli hajjiya tana cewa.

"Mommy wannan 'yan uwana ne daga saudiya ."

Ta nuna Ahmad tana cewa.
"Wannan shi ne Ahmad, ga kuma Najib ." Shi ma ta nuna
Shi

Lokacin hankalin Hajjiya ya sake kwanciya, suka sake sabuwar gaisawa tare da tambayar mahaifiyar su .

Fatima ta kalli su Ahmad tana cewa.
"Wannan mahaifiyar Zarah ce , ga kuma 'yan uwanta ."

Wani farin ciki ya sake rufe su , suka fara hira

Umar ne ya ce .
"Kun sha hanya sannuku ."

Najib ne ya mayar masa da cewa .

"Ai dake ma muna can gidan mahaifin mu , kuma yanzu zamu koma domin nan da minti kad'an jirginmu zai tashi ."

Fatima ta murtuke ranta matuka tana cewa.
"Wanne irin yanzu kuma yaya gaskiya ni wai mene haka ."?

Bacin rai ya bayyana a fuskarta .

Najib ya ce.

" yanzu kuwa , zamu koma ."

Hajjiya ce ta ce ."Fatima baki kawo musu komai ba , kina ta murna ."

Fatima ta dafa kanta alamun sha'afa tana cewa.

"Wallahi mommy na manta ."

Najib ya ce .
"Kar ki kawo mana komai domin daga gidan Alaji mu ke , kuma ba za mu bari mu rasa jirgi ba ."

Fatima ta sake hada ranta jin cewa da gaske tafiyar za si .

Ahmad ya kalleta kana ya ce.
"Wai ina Kamal din ne da Zarah."?

Tana cuno musu baki ta ce .
" Sun fita amma zaku jira su dawo ai . Me ya sa Aunty Murja bata zo ba ."?

Najib ya yi murmushi kafin ya ce .
"Zata zo ne , mommy na nan zuwa a sabon wata mai kamawa in sha Allah."

Wani dadin gaske Fatima taji tana sake bazo idanunta tana cewa.

"Allah ya kawota wallahi na yi kewar mommy na ."

Hajjiya Sa'adatu ce ta yi murmushi tana cewa.
"Ai dole , amma dan Allah idan ta zo karta tafi baki hada mu ba Fatima, domin bazan ji dadi ba ."

Fatima ta ce ."In sha Allah mommy zan hada ku , idan ta zo ."

"Ta shi mu koma Ahmad." Najib ya fada cikin yaren larabci

Duk suka tashi tsaye

"Haba dan Allah yaya wai tafiya zaku yi ."? Fatima ta fada da matukar haushi .

Ahmad ya CE ." In sha Allah, kina so mu kwana anan ne , karki damu nan da wata biyu zamu zo mu yi sati a Nigeria. "

Ya karasa magana yayin da sukai sallama dasu Hajjiya da Mahmud

Kafin su isa bakin kofa

Kamal da Nasir suka shigo suna dariya suna hirarsu .

A wannan lokacin ne suka lura da irin manya manyan bakin da sukai

Kamal ya ma kasa cewa komai , domin ya rasa dasu waye ma zai fara magana

Da sauri ya karaso cikin falon yana cewa.

"Ka ce yau manyan baki mu kai , ai dana san zaku zo babu inda zan fita ."

Suka mika hannu suka gaisa da su Ahmad da Najib dake tsaye

Sannan ya karasa ya gaida Hajjiya suka kuma gaisawa da su Mahmud

Kamal ya kalli Fatima yana cewa.
"Yana gansu a tsaye ."

Fatima ta ce ..
"Wai tafiya zasi fa ko minti 30 basi ba ."

Kamal ya karasa gabansu yana cewa.
"A haba dai yaushe rabon ku zo , kuma ku ce zaku tafi Ahmad."

Ahmad ya yi dariya sannan ya ce .
"Wallahi zamu rasa jirgi dole mu tafi , tunda Allah ya yi zamu gaisa da kai ."

Najib ya ce .
"Gaskiya ne , sai wani lokacin kuma ."

Suka nufi hanyar fita yayin da Kamal da Zarah su kai musu rakiya

Bayan sun dawo ne Hajjiya take cewa .
"Ku tashi ku yi sallah muma mu tafi ."

Kamal ya dubi Fatima yana cewa.
"Wai ina Zarah ne , ko dai bata dawo ba ."

Fatima ta ce .
"Eh."

"Bari na kirata mana ." Ya dauki wayarsa

Hajjiya ta ce .
"A" a barta wallahi, Fatima ma tace zata kirata ni na hanata , ai baza mu jira ba gaskiya, in tana son ganin mu ta zo gidan kawai ."

Kamal ya yi ajiyar zuciya ya aje wayar yana cewa.
"Ai ya ci a ce ta dawo ."

Hajjiya ta tashi ta dauro alwala , bayan suma su Mahmud sun yi sallah suka koma gida .

Next page in sha Allah🙏

FATIMA DA ZARAH🎀
Na

Autar Marubuta

________________________________________

*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><

Editing❌

Page 24 & 25

Lokacin da Zarah ta dawo ta yi matukar takaici na rashin samun bakin da akai .

Anan cikin gidan Alaji Mustapha kuwa

Hajjiya Binta ce , zaune a falo ita da Abba Alaji, sakamakon yau ya zo gidan

Kallon shi ta yi sannan ta ce .
"Yau kuma an tuna dani ke nan har an kawon ziyara ,
To ka gama makarantar ne ."?

Murmushi Abba Alaji ya yi sannan ya d'ago yana cewa.
" Tun yaushe ma kuwa ai sakamakon ya yi kyau ."

Dogon tsaki hajjiya Binta ta ja kana ta ce .
"Ka ji makaryacin banza , daman jin bakin ka zan , tun yaushe Alaji yake sanar mini , ka yi abin da ka yi an kore ka ."

Abba Alaji ya d'ago yana kallon ta da idanunsa na rashin kunya yana cewa.

"Au to tunda kin sani mene na tambaya kuma ."

Hajjiya Binta ta yi ajiyar zuciya tana sake kallon takaici ga Abba tana cewa.
"Wallahi ka kiyayi duniya Abba, yayana yana iya yinsa don ganin ka zama mutumin kirki , amma kai kullum kana yawo kana jawo masa magana ana zaginsa , to ka cigaba Allah ya gani ai idan ka kashe shi sai hankalin ka ya kwanta ."

Abba Alaji ya d'ago da jajayen idanunshi yana cewa.
"Ke kinji ki Aunty ta ya Daddy zai mutu, ai kuma Daddy yana sona ."

Hajjiya ta ce .
"Dah ne yake son ka wallahi Abba da zaka zama mutumin kirki, ba karamin dadi za ka samu wajen Alaji ba , amma kai ne can neman fitina iri-iri .

To wallahi daman ya ce komai ya ishe shi zai jire hannunshi a kan ka .

To tun kafin haka ta faru ka gyara halinka , ka zama mutumin kirki, ka dena shaye-shaye, yanzu dubi irin askin dake kanka kamar ba d'an musulmi ba ."

Abba Alaji cikin bacin rai ya tashi tsaye yana cewa.

"Ke kinji ki , shi ya sa bana son zuwa gidanki wallahi , gara ma na tafi sai anjuma ."..
Ya nufi kofar fita tana kiran shi , ko juyowa bai ba ya fice abinsa .

Ta yi ajiyar zuciya tana cewa.
" Allah ka shirya mana wannan yaro ."

Yau su Fatima suka kai ziyara gidansu kamal, har suka gano kayan lefen Laila wanda biki sauran sati biyu .

Misalin 9 na dare .
Duk su kamal suna zaune a falo suna kallo .

A lokacin Laila ta turo kofa ta shigo tare da sallama da wasu ledoji a hannunta.

Kamal ya yi ajiyar zuciya kafin ya ce .

"Yanzu a wannan daren Alaji ya barki kika fito , ba an ce ki bari gobe ki kawo kayanka ba ."?

Laila ta tabe baki tare da fara yo taku zuwa cikin falon tana cewa.
" Wallahi yaya bana son fita da rana ."

Kamal ya ja tsaki

Nasir ya ce .
"Ka ga wai ita amarya tabb , za a ga wani abu ."

Fatima da Zarah sukai dariya

Laila ta kalli Nasir tana cewa.
"Kai dai kaji kunya wallahi, kullum tsokana mtww."

Nasir ya yi dariya yana cewa.
"Naji dadi ma sanda zan dawo gidan ba kyanan ai gara ...."

Bai karasa magana ba kamal ya katse shi da cewa .

"Zaka bari ta yi abin da ya kawota ko kuwa sai dare ya kuma yi ."

Nasir ya yi shiru
, Laila ta masa kwalo , sannan ta zo ta zauna

"Aunty Fatima da Aunty zarah ga kayan zuwa dinner din ku , yau muka am so su har da nawa ."

Suka amsa suka bud'e nan suka yaba katafaren kyan da dinkin ya musu .

"To tashi Laila tashi maxa dare na yi ." Cewar Kamal

Laila ta tashi tana cewa.
"Haba yaya kamal daga zuwana ."

Zarah ta ce .
"Ai shi ne ."

Kamal ya ce .
"Ni wallahi bansan me ya sa su mommy suka bari kika fito ba ma ."

Ya kalli Nasir yana cewa.
"Tashi ka rakata har gida ."

Haka Nasir ya sa Laila gaba har suka isa gida

Zarah ce ta ce .
"Za'a sha dinner kam zamu sha liki ."

Fatima ta yi murmushi

Kamal ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce .
"To duk nasan halinku wallahi kar wacce taje ta lika sama da Naira , na dai fada muku ."

Ya tashi ya shiga ciki .

To Allah ya kai mu wannan biki , domin Alaji Mustapha ya yi matukar yin sa don samun farin cikin Laila, yadda ya riketa bata taba kukan rashin iyaye ba , to haka ma a wannan biki ya aje mata abin da zatai alfari dashi matukar gaske .
Chapter 10 · 0% Book details