Sashe 5
Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wajen minti biyar ke nan su kamo can su kamo can cikin farin ciki , kamal duk sai yaji ba abin da yake damun shi
Lokacin da Habib yake basu wani labari suka ke ce da dariya , sai ga Alaji Mustapha ya shigo falon
Girgiza kai ya yi alamun mamaki yayin da ya fara takowa wajen su ya fara cewa
."Sannunku jarumai , yanzu dama Kamal d'in ne ya zo amma kun sa shi a gaba kuna ta wani dariya , maimakon ku sanar da fatima amma kuna ta masa surutu."
Kamal ya zube kasa yana gaida Alaji Mustapha cikin girmamawa
Bayan sun gaisa Alaji ya ce ."Yi hakuri fa Kamal, wai nan duk sojoji ne , amma babu kai ."
Dariya ce duk ta kusan kwace musu dajin zancen Alaji
Habib ya mi'ke yana cewa. "A yi hakuri Daddy bari a kira masa Fatiman."
"Wacce Fatima kuma zaka kira , yanzu lokacin kun cinye shi , dan haka ku tafi masallaci ku dawo tukun ."
Habib ya ce ."To Daddy bari muje kafin mu rasa sallar ."
Alaji ya dubi Khalid da Habib yana cewa. "Saura idan kuka dawo ku sake sashi gaba kuna zance, kuna dawowa ku sanar da Fatima."
Khalid ya ce ."In sha Allah Baba. "
Sannan suka wuce suka d'auro alwala suka tafi masallaci .
A 'bangaren Zarah babu abin da ya canza , domin yanzu tana tafe cikin motarta ta nufi asubiti, tana zuwa babu jira ta fara duba marasa lafiya .
Bayan su Habib sun dawo daga masallaci, suka shiga ciki suka kira masa Fatima, yayin da suka shige ciki.
Minti biyar ke nan Kamal yana zaune, kafin daga nan yaji sautin tafiya daga saman bene , wanda hakan ya tabbatar masa da cewa wannan Fatima ce take zuwa
Idanu ya zuba mata kafin ta karaso , tsayinta daidai dana Zarah, wannan tafi Zarah hanci da manyan idanu , ta sanya bakar riga tare da ash din mayafi , cikin fatar hutu da kyau
Numfashi yaja yana kauda kanshi kafin ta fahimci yana kallon ta , ya yi ajiyar zuciya
Lokacin da Fatima ta karaso gaban Kamal duk yabi ya rude ya kid'ume sakamakon wani kwarjini da take masa
"Assalamu alaikum." Fatima ta yi sallama tare da zama cikin nutsuwa
'Dago kai ya yi ya kalleta , maimakon ya amsa sallamar da tai ,cikin kidumewa ya ce
."Baku da yarah ne a gidan ."
Murmushi Fatima ta yi domin tabbas ta fahimci halin da ya shiga da ganin ta
Kamar za tai dariya ta ce ."Bamu da yarah , fatan ka zo lafiya ."
Sa da ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce ."Lafiya kalau wallahi tun d'azu nazo muna ta hira dasu Khalid har mun je sallar mun dawo ."
Murmushi ta sake yi a karo na biyu yayin data kasa cewa komai ta durkusar da kai kasa
Shima haka Kamal ya gaza magana domin duk ya rasa kalmomin da zai magana dasu
Wajen minti guda kowa yana sa'ke-sa'ke a cikin ranshi
Sannan Kamal ya yi kokari ya ce ."Malama Fatima, nasan kin san iyayen mu sun saka ranar auren mu .
Nan bada jimawa ba zasi mana aure. "
Fatima ta d'ago kai tace dashi ."Haka ne."
Sannan Kamal ya yi ajiyar zuciya yana sake cewa ."Rayuwa kaddara ce , a matsayinmu na musulmai dole mu amshi kaddarar , a ko yaushe ta zo ." Ya karasa magana yana kallon Fatima
Murmushi Fatima tasa kana ta fara magana."Gaskiya ne , ina son karka mini karya a kowanne yanayi ka sanar dani gaskiya komai muninta da zafinta ."
Kamal ajiyar zuciya ya yi daga bisani ya kalli Fatima ya fara cewa ."Najin dadin jin hakan , kamar yadda kika sani suna na Kamal, aikina a company ne , sannan ina da Zarah wacce kullum ita ce mafarkina da nake son aura , amma Allah ke ce ya zaba mini ."
Ya kalli Fatima tare da sake cewa ."Sai dai banajin koda na aure ki bazan auri Zarah ba , ina son Zarah kuma in sha Allah idan Allah ya so ita ma zan aure ta ."
Fatima wani zafin kishi taji ya dakar mata zuciya, amma lokaci guda ta share shi ta fuskanci kamal tana fad'in
."Eh to yin Allah shi ne daidai ."
Murmushi ya sake mata a karo na ba adadi yana cewa
."Amma ni ban san komai game dake ba ."
Ita ma murmushi ta yi sannan ta d'aga idanunta tana kallon Kamal
Sannan ta fara magana. "Uhm .
Na yi karatun lauya a yobe , ni 'yar kasuwa ce , sannan kuma a halin yanzu ni lauya ce , ina kuma fuskantar kowacce irin shari'a."
Murmushi ya yi har sai da hakoranshi suka bayyana
Sannan cikin ranshi yake cewa ."Okay yanzu kin fiddani duhu barrister. "
Sannan ya fito fili yana cewa. "Barrister Fatima.
Tabbas kuwa zan aikata abin dana ke so ko."?
Dariya Fatima ta yi sannan......
Hajjiya Amina ce zaune a falo ita da Laila
Laila ce take cewa ." Mommy kin ga har yanzu Yaya Kamal bai dawo ba ."
Hajjiya ta ce ."Ai duk inda yake yanzu yana hanyar gida ."
Laila ta sosa 'keya ta kalli Hajjiya, sannan ta fara cewa ."Mom Ahmad ya ce fa zai turo ."
Kallon Laila ta yi tana cewa. "Wai me yake ci na baka na zuba , yanzu ta auren Kamal ake , ya bari a gama tukun ."
"To mommy a had'a mana dana yaya da namu ."
Hajjiya ta kalli Laila cikin mamaki tana cewa
."Eh gaskiya ne zamani ya lalace , to sannu Laila da wannan 'karfin halin , to kije ki sanarwa da Alaji mana ai shi ne zai miki auren ."
Dariya Laila ta kwashe da ita tana kwanciya a kafar Hajjiya
Ita ko Hajjiya tana sake jin mamakin zancen Laila ta ce ."To ai kuwa ana yin na kamal zan sa Alaji ya kawar dake tunda kin fara tuna ....."
Bata karasa magana ba , sallamar Kamal ta katseta
Kamal ya karasao ya zauna tare da cire hular kanshi
."Sannu da zuwa Yaya Kamal. " Laila ta fad'a
Yayin da ya amsa mata
."Mommy na dawo kuma Fatima tana gaidaku ."
Kamal ya fad'a yana cire agogon hannunshi
Murmushi najin dadi Hajjiya ta yi, ganin yadda d'an nata yake ta farr 'a
Kafin ta ce komai ya tashi yana cewa. "Bari na watsa ruwa Mom." Ya nufi sama
Bayan wasu kwanaki
IBADAN
Samari ne su uku suna zaune suna karatu a cikin dakinsu cikinsu kuwa har da Nasir , duk babu wanda yake cewa da kowa komai , duk booklet ce a hannunsu
Sautin kawai Bashir ake ji , da yake yin karatun a zahiri
Tun d'azu Khalifa yake gallawa Bashir harara , sannan yaja tsaki
"Wai Khalifa idan baza kai karatun nan ba ka ajiye mana , sai tsaki kake mana ."
Nasir ya yi magana yana aje handout nashi
Cikin haushi Khalifa ya ce ."Wannan banzan ne mana Bashir ya yi karatu a zuciya ya'ki sai damuna yake. "
Dariyar 'keta Nasir ya kwashe da ita .
Yayin da Khalifa ko sauraransu bai yi ba , ya cigaba karatun shi
Haushin hakan ya sa Bashir fisgar handout din yana jefarwa gefe
Nasir ya sake fashewa da dariya , kawai Khalifa yaja tsaki yana fad'in
."Ka kiya ye ni fa , ni wallahi ma inajin nan da sati zanje gida ."
Nasir ya ce ."Ka bari sai bikin Yaya Kamal wallahi sauran kwana kad'an , muje ana d'aura aure mu dawo ."
Bashir ya ta'be baki yana cewa. "Allah ya sauwake muna exam a lokacin zamu je kano mu dawo, wallahi baza ni ."
A lokacin Abba Alaji ya ban kad'o kofa ya shigo , alamun ya sha ya bugu , yana shigowa ya fad'a gado ya fara bacci .
Ran Khalifa ya matukar baci ya kalli Nasir yana cewa. "Wallahi wataran sai na yiwa Abba shegen duka ."
.Su ka kwashe da dariya .
Alkalamin
Autar marubuta ne .
FATIMA DA ZARAH🎀
Na
Autar Marubuta
_______________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><
Editing❌
Page 12 & 13
Duk ana ta shirye-shiryen biki , 'kanwar Hajjiya Samira, Murja sun zo ita da sauran yaran Alaji Mustapha
Domin gobe ne d'aurin aure
Alaji Mansur ne a zaune a falo, yana waya
A lokacin Kamal ya shigo ya zauna a kasa
."To Alaji Musa bari. , sai kun shigo goben, dan Allah a sanar dasu ambassador da Malam Mu'azu ."
Alaji Mustapha shiru ya yi sakamakon abokin nashi daga can barin yana magana , bayan ya gama Alaji ya ce ."To shi ke nan , na gode sosai sai mun had'u."
Sannan ya aje wayar cikin farin ciki ."To ya maganar gidan naka ya yi maka ."?
Alaji ya tambayi Kamal
Kamal cikin girmamawa ya ce ."Daddy ya yi babu wata damuwa ."
Alaji ya ce ."To alhamdulillah,
Abin dana ke son ka sani Kamal, wannan sabuwar rayuwa ce zaka fara , ka sauke hakkin Fatima, kar ka cutar da Fatima, matukar ka cutar da ita ka cutar dani duniya da lahira ."
Da sauri Kamal ya kalli mahaifinsa cikin mamaki ."Haba Daddy, wallahi bazan cutar da Fatima, ka za'ba mini Fatima, kuma naji na gani na amince kuma Daddy samm bazan baka kunya ."
Murmushi Alaji Mustapha ya yi kana ya ce ."To gaskiya naji dadi kamal, Allah ya yi maka albarka ya sa ka gama da duniya lafiya. "
Kamal ya ce ."Amin daddy. "
Sannan Alaji ya sallami Kamal ya tafi , yana fita ya nufi arabar motoci sannan ya hau mota ya nufi gidansu Fatima
Isar shi ke nan suka gaisa da mai gadi sannan ya shiga ciki
Bayan ya gaisa da Hajjiya Rukayya, suka gaisa da Murjanatu nan ake sanar masa kanwar mahaifiyar Fatima ce
Cikin girmamawa ya gaisa dasu faruk da Ahmad nan ake ta farin ciki
Bayan ya tashi tafiya ne Fatima ta rakoshi har wajen motarshi yayin da ya zuba mata idanu
Ta yi wani kyau matuka irin na amare sai sheki take
."Uhm lafiya kuwa Kamal. "