← Book details Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 20

Sashe 6

Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fatima ta fad'a yayin da ta ga kallon ya mata yawah

Ajiyar zuciya Kamal ya yi sannan ya fara cewa ."Lafiya mana Fatima , ko lefi ne dan na kalli amaryata ."

Wani yammm Fatima taji sakamakon karan farko da ya fara nuna mata irin wannan yanayi

Ta masa murmushi

Sannan Kamal ya ce ."Fatima ina son sanar dake na shirya rayuwa dake komai tsanani , zan kula dake ga dukkan iyakar kulawata , duk yadda Allah ya tsara maka rayuwa shi ne daidai , a domin haka ina son ki sani ina son ki , ina kaunar ki , domin kin zamanto mini wani babban sashi lokaci guda a rayuwata, son ki ya kamani a yanayin da ban yi tsamani ba, wallahi Fatima daga zuciya ta ne wannan sakon yake zuwa gare ki ."

Murmushi Fatima ta yi na matukar jin nauyin Kamal
Sannan ta kau da kai tana cewa ." Masha Allah Kamal, hakika naji dadin jin wannan. "

Shima Kamal murmushi na farin ciki ya yi yana cewa ."To yanzu mene ne kike da bukata."..

BAYAN AURE

Kamal da Fatima tuni ansha biki , komai ya yi matukar kyau , an sha shagali sosai da sosai , har mutanen saudiya sun koma , auren Kamal da Fatima babu wata matsala.

Hajjiya Amina ce da Alaji Mansur a zaune suna hira

Sallamar Kamal ce tasa su duk shiga wani farin ciki

Nan ya durkusa ya gashshe da iyayen nasa

."To ya 'yar tawa ."?
Alaji Mansur ya tambayi Kamal

Murmushi Kamal ya yi yana cewa. "Tana lafiya Daddy."

Hajjiya Amina ta ce ."To masha Allah, Allah ya kara zaman lafiya ."

Alaji ya kalli kamal yana cewa. "Mene yake tafe da kai ne , domin tun jiya kake zuwa kuma akwai magana a bakin ka ."

Kamal ya durkusar da kai yana sosa 'keya.
Alaji ya yi dariya yana cewa. "Ai ni na sani ,wannan yaron naki akwai maganar da take kawo shi ya kasa yi ." Ya karasa magana yana kallon Hajjiya

Hajjiya ta ce ."Ai Alaji a kan maganar auren yarinyar nan ne Zarah yake son kasa baki a kai ."

Alaji Mansur ya 'bata rai lokaci guda yana cewa. "Wanne irin Zarah kuma , wata kuma zaka kuma aura ? Yaushe ka auri Fatima."

Jin hakan ya sa hankalin Kamal tashi tsaye , take ya shiga wani hali

Ya d'ago cikin maraicewa ya ce ."Daddy dan Allah, ka duba ."....

Alaji ya dakatar dashi yana cewa. "Ka yi min shiru Kamal, karka sa yanzu na bata maka rai."

A take yaji kanshi yana sara masa ya kalli mahaifiyar tashi Hajjiya Amina cikin matukar damuwa da shiga wani hali .

Cikin takaici Hajjiya Amina ta kalli Alaji tana cewa. "Haba Alaji , Kamal kuwa bai cancanci haka ba wallahi, ka dubi yaron nan yadda ya maka biyayya a auren Fatima, bayan ba shi da ra'a yinta , amma saboda ganin girmanka da tasiri ya amince , amma yanzu ya zo da zance a ce masa ba haka ba , ai kuwa wallahi Kamal bai cancanci wannan ba daga gare mu ."

Babu annuri ta karasa magana tana ajiyar zuciya ta takaici

Shima Alaji Mansur ajiyar zuciya ya yi yana cewa.. "Alhamdulillah Hajjiya Amina, kin yi gaskiya, shi ya sa nake sake kaunar ki , da zarar na bar hanya kike dawo dani daidai .Allah ya miki albarka."

Ya kalli Kamal yana cewa. "Kamal Allah ya maka albarka kai ma , kuma wannan yarinyar Zarah take ko wa , in sha Allah zaka aure ta ."

Wani farin ciki ne ya rufe zuciyar Kamal da Hajjiya Amina

Bari ma Kamal ya kasa rufe baki

"Daddy na gode Allah ya saka da alheri ." Kamal ya fad'a yana washewa mommy baki

Alaji ya ce ."A'a dena godiya, ka wuce haka , babanta naji kamar ana cewa Alaji sale ne ko ."?

Kamal ya ce ."A Dad shi ne ."

Alaji Mansur ya ce ."To masha Allah. "

Bayan wasu kwanaki

Kamal ne zaune a cikin falo , ya d'auki wayarshi ya kira Zarah, bugu daya ya yi ta d'auka bayan sun gaisa ne

Fatima ta shigo falon ita ma ta zauna, nan kamal ya cigaba da wayarshi da Zarah suna ta soyayyarsu

Fatima kuwa tana ta danna wayarta

Bayan ya gama ya dubi Fatima yana cewa. "My love ya ya aka yi ne , wai ko kishina ba kye yi koh."

Dariya Fatima ta yi tana cewa ."Kishi kuma , ai ni wallahi dear na matsu Zarah ta shigo gidan nan ."

Kamal yaja ajiyar zuciya yana cewa. "Tabbb gaskiya kina bani mamaki , amma ai shi ke nan .

Na ji kina zaki je office to ki shirya nima zani company sai na aje ki , sannan na biya gidan Hajjiya."

Fatima ta ce ."Dah ka bari na tafi a mota na ."

Kamal ya galla mata harara yana cewa. "An ki , ni fa ko kad'an bana so kina nesa dani , kishirya idan ma zaki dawo ni ne zan d'auko ki."

Bai jira ta ce komai ba ya tashi ya koma kujerar da take zaune

Sannan ya karbi wayar dake hannunta ya aje gefe yana cewa. "A karon farko dana kalli shari'arki kin sani jin sabon alfaharin da nake yi dake matata .Kin iya aikin ki my life, na yi matukar farin ciki sosai Fatima ina kaunar ki ."

Murmushi ta yi tana sake damke hannayenshi tana cewa. "Ina alfarin zamowa matarka Kamal nima ina kaunarka ga dukkan yaki nina."

Junansu suka rungume cikin matukar shaukin juna

Sannan Kamal ya ce ."Kuma ki shirya ina nan zan aikata 'barna domin nasan zaki wanke ni a kotu ."

Fatima tsare shi tai daga jikinta tana kallon shi da cewa ."Kana aikatawa zan aje aiki ."

Dariya ya kwashe da ita yana cewa. "Oho dai gara ma ki shirya , domin shari'ar dazan jayo miki me wahala ce , kuma dole ki karbo ni Barrister Fatima ta ."

Dariya ta yi tana cewa ."To mu shirya kafin lokaci ya 'kure ." Ta yi maganar cikin harshen turanci

Minti 30 suka bata da suka fito Kamal ya aje Fatima a wajen aikinsu

Yayin dashi kuma ya karasa gidansu

Kamal yana shiga tunkan ya karasa falo ya fara jin muryar mahaifiyar tashi , sama-sama sai fad'a take

Yana shiga ya yi sallama , Laila ta amsa ya shigo ya sa mu guri ya zauna

Yadda ya kalli Nasir ya tabbatar mommy shi ne takewa fad'a

Lokaci guda Kamal ya canja ya karbi bakin mommy

."Wai kai wanne irin yaro ne Nasir, kullum sai ka 'batawa mommy, yaushe ma ka baro makarantar. "

Mommy ta amshe da cewa ."Rabu dashi kanshi ya yi wa asara gashi nan an kore su a makarantar ai. Ba shi ke nan ba ."

Cikin mamaki kamal ya ce ."Mommy kamar ya an kore su a makaranta."

Autar marubuta.

FATIMA DA ZARAH🎀
Na

Autar Marubuta
____________________________________________

*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><

Editing❌

Page 14 & 15

Mommy kawai ta kauda kai cikin takaici
Kamal ya kalli Nasir cikin fushi ya kuma fad'in. " An kore ku kamar ya ?Wanne rashin mutuncin kuka aikata ."?

Nasir yaja doguwar ajiyar zuciya na takaicin wannan yanayi , sannan ya kalli Kamal cikin nuna damuwarshi yana cewa
."Wallahi yaya Kamal, ba abin da muka yi , Abba Alaji ne ya yi laifi duk ya shafe mu , daman suna neman hanyar rage d'aluban , amma bami komai. "..

Kamal ya dakatar dashi yana cewa." Yi min shiru dan Allah, zan cen banza , Abba Alaji ubanka ne ko ran ka ne da baza ka barshi ba . To wallahi na yi abin da zan iya maka , saboda karatun ka ne har yau bamu bud'e sabon company ba , zan nemi wani kawai , kaje kai ta rashin mutuncinka ."

Cikin sauri Nasir ya kalli Kamal idanunshi sun ciko da hawaye yana cewa. "
Dan Allah yaya karka mini haka , wallahi ba a san raina komai ya faru ba , na yi iya yina don gudun hakan ."

Ya share hawayen da suka zubo masa sannan ya cigaba da cewa ."Ka yi hakuri dan Allah ka sake bani wata damar ka nema mini wata makarantar ko anan kano ne , in sha Allah bazan baka kunya ba Yaya. "

Kamal ya sunkuyar da kai kasa bai ce komai ba

Ganin haka ya sa Nasir kallon Hajjiya Amina yana cewa ."Mommy dan Allah, wallahi ina yin komai dan in gyara gobe na ki roka mini Yaya Kamal dan Allah. "

Laila cikin jin tausayin yayan nata ta kalli Kamal tana cewa. "Yaya ka yi hakuri."

Hajjiya Amina ta kalli Kamal tana cewa. "Shi ke nan Kamal, ka masa kokari , amma idan ka nema masa makarantar ya koma gidan ka da zama nima na huta ."

Kamal ya d'ago yana aje ajiyar zuciya sannan ya ce da Nasir. "Shi ke nan amma dole ne ka rabu da wannan mahaukacin abokin naka ."

Nasir ya ce ."In sha Allah zan yi iya yina Yaya Kamal na gode. "

Barrister Fatima ce zaune cikin office, tana duba wasu takardu da zatai shari'a a kai

A lokacin wata barrister Khadija ta shigo tana shigowa ta dubi Fatima tana mata dariya ,sannan ta nemi guri ta zauna .

Fatima kallon ta ta yi ba tare da tace komai ba , sannan barrister Khadija ta ce .
"To Fatima ya kika ga shari'ar zaki karba ne ."

Ajiyar zuciya Fatima ta yi tare da rufe kundin tana cewa. "A'a gaskiya Khadija, domin wallahi bana son shari'a me wahala yanzu. Kawai zan karbi shari'ar Alaji Muhd zan tsaya masa

" Tabbb sannu ." Cewar Barrister Khadija

Sannan ta cigaba da cewa ."Kawai dai kice aure ya sangartaki , wannan shari'ar wallahi baza ta miki wuya ba , shari'a nawa kika yi wacce tafi wannan wahala, sai yanzu zaki ce wani-wani .Kawai dai Kamal ya sangartaki kuma zan masa magana ."
Ta karasa magana tana wani jujjuya fuska

Dariya Fatima ta yi sannan ta juya suka gaisa da wani Barrister Aminu
Chapter 6 · 0% Book details