← Book details Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 20

Sashe 2

Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin farin ciki shima Alaji Mansur ya fara cewa ,"Karka damu ai kawai mu fara shiryawa domin babu abin da zai lalata mana wannan zumuncin ,kawai Allah ya kaimu ranar ." Alaji Mansur ya karasa maganar yayin da driver ya bude masa mota ya shiga .

Sannan sukai sallama da juna , driver ya tu'ka motar suka tafi .

Fatima ce kwance kan gado tana kokarin yin bacci gefe guda ta kalli wasu curin takardu tana tsaki

"Allah ka bani hutu , yanzu na dawo daga office, kaina ciwo yake wallahi ya kamata na yi bacci , ni koma ya jikin umma."

Ta karasa maganar tana daukar wayarta domin kiran Ahmad

Amma tana d'auko wayar sai ga kiran Najib ya shigo , babu jira ta d'auki kiran tana cewa ,"Yanzu nake shirin kiran Ahmad. "

Daga can cikin larabci ya fara mata magana yana cewa, "'Yar Nigeria ya aiki ya Nigeria, daman mommy ce ta ce zaku gaisa."

Murmushi Fatima ta yi , kana cikin yaren Hausa ta fara cewa ,"Aiki kalau kuma haka kasarku Nigeria tana lafiya , wallahi ina kewar ku."

Najib ya yi dariya sannan ya canza harshe ya koma Hausa yana cewa, "To ya shari'ar ko ba a yi."

Fatima ta yi ajiyar zuciya tana cewa, "Dan Allah ka ba mommy na wayar , ina matukar mutuwar son jinta yanzu."

Najib ya yi dariya sannan ya bawa Hajjiya Samira wayar .

"Assalamu alaikum ."

Fatima ta amsa sallamar mahaifiyar tata cikin matukar kewar ta

"Mommy fatan kinji sauki sosai wallahi ina kewar ki mamana."

Murmushi ta yi sannan ta ce ,"Naji sauki Fatima, ai banso suka sanar dake bani da lafiya ba , sun d'aga miki hankali. "

Fatima ta ce ,"Haba mama ke fa uwa ce a gare ni , bani da fatan da ya wuce ki samu lafiya , in sha Allah ciwon zuciyarki sai ya zama tarihi ."

Hajjiya Samira ta ce ,"Fatima ke nan , to ya mutanen gidan , nasan zaman hakuri kike Fatima, aita hakuri wata rana sai labari ."

A jiyar zuciya Fatima ta yi kafin ta ce ,"Babu wani zaman hakuri mommy, ni kawai kewar ku nake , kuma ina nan zuwa ."

Hajjiya ta yi murmushi tare da cewa ,"Fatima ke nan nifa nasan ba rayuwar farin ciki kike ba kawai dai bakya son fada mini ne."

Fatima cikin wayantar da zancen ta ce ,"Ni fa mommy gaskiya zaku gànni wajen shekara biyu fa banganki ba , sai dai video call, dasu yaya Faruk da Ahmad, ina aunty Murja ."

Hajjiya Samira ta sanar da ita kowa lafiya kuma komai daidai

Bayan sun gama wayar ne sai ga Murjanatu ta shigo wato 'kanwa ga Hajjiya Samira....

Yadda Fatima taji kewar mahaifiyar ta da yadda idan ta tuna yadda take rayuwa a gidan mahaifinta ya sa ta fad'a gadon nata ta fashe da kuka , kuka take mai gwanin ban tausayi abin ta

Yayin da taji ana mata bugun kofa ne ya sa ta tashi da sauri tana share hawayenta , sannan ta bud'e kofar

Hajjiya Binta ta gani tsaye tana kallonta

wata harara ta jefawa Fatima sannan ta ce ,"Kin dawo daga office, shi kuma wanke-wanke da girkin daren wane zai mana ko so kike aiki ya kashe mu ne ."

Ajiyar zuciya Fatima ta yi tana cewa, "Dama mommy yanzu nske shirin fitowa ."

Hajjiya Binta ta juya tana cewa, "Ya dai fi." Sannan ta koma falo inda Alaji Mustapha yake zaune tare da Hajjiya Rukayya

Fatima kanta yana matukar ciwo ta fito , tana nufo falo ta ga Alaji shima yana zaune ta nufi bangaren madafa wato d'akin girki , kafin ta sa 'kafa ta shiga taji muryar mahaifin nata yana kiran ta

Hakan ya sa ta juyo ta nufi wajen shi , tana isa ta zauna a kasa cikin matukar tsoro da fargaba , domin tasan tunda ta ga wannan makiran matan nasa biyu to tabbas sun had'a ta da mahaifinta

'Tashi ki zauna a kujera ."Alaji Mustapha ya fad'a cikin takama

Fatima ta aiwatar da umarninsa kamar yadda taji

"Mene zaki a dakin girki ."?
Ya tambaya cikin jiran amsa

" Daddy zan yi abu ne ."

Jin amsar Fatima ya sa Alaji Mustapha wani murmushin takaici yana dariya mai ciwo

Yayin da kuma ya fara cewa ,"Fatima ke ce kawai Allah ya bani 'ya mace , hakan yasa koda muka rabu da mahaifiyar ki Samira ban bari ta tafi dake ba .

Amma sai dai Allah ya jarabe ki da zama cikin azzaluman kishiyoyin uwa da basa kaunar ki ."

Cikin mamaki Hajjiya Binta da Hajjiya Rukayya suka kalli juna

Hajjiya Rukayya ta tari numfashin Alaji tana cewa, "Haba Alaji, duk kokarin da muke wa yarinyar nan baka gani , ai ko 'yar muce ....."

"Yimin shiru." Alaji Mustapha ya katse ta cikin matukar fushi , sannan ya d'ora da magana

"Duk kallon ku nake tarrrrr wallahi, Fatima tana shan wahala a hannunku matuka, amma na zuba muku idanu domin ganin gudun ruwanku , tsawon lokaci yarinyar nan ko sau daya ba ta ta'ba kawo karar ku ba . Amma dake baku da imani ko a jikin ku."

Cikin huci Alaji Mustapha ya dubi kowacce a cikinsu yana cewa, "To daga yauuuu kar wacce ta sake saka Fatima aiki a cikin gidan nan , komai mene ne na haramta .

Mene ne amfanunku , duk wacce baza ta iya ba ga hanya Allah ya tsare."

A karo na biyu suka sake kallon juna

Alaji Mustapha kam ya ci gaba da fad'an shi yana cewa, "Tsinke idan Fatima ta sake d'auka a cikin gidan nan zaku ga yadda zami daku , ai wallahi kawai shiru nake muku babu irin kissar ku da munafunci da ban sani ba tun lokacin Samira , Samira ta fiku komai kawai kaddara ce ta raba mu .

To wallahi kun yi na farko kunyi na karshe , kun yi na marmari ya gundire ku , an yi walkiya na gama ganin ku , kuma ni da ku shege ya fasa ku tashi ku bani waje mutanen kawai."

Zumbur suka tashi Hajjiya Binta na gajeren tsaki wanda Alaji bai ji ba

Bayan sun fita Alaji ya yi ajiyar zuciya, yayin da Fatima ta kalli mahaifinta tana cewa ,"Dan Allah Daddy ka yi hakuri."

Alaji Mustapha ya ce ,"Karki damu Fatima ba zaman lafiya suke so ba ,
Ke yarinya ce mai tausayi da hakuri kamar mahaifiyar ki .Allah ya yi miki albarka."

Fatima ta amsa da ,"Amin Daddy. "

Alaji Mustapha zama ya gyara yana kallon Fatima da niyyar fara sabuwar magana

"Sannan kuma Fatima akwai al'amarin da nake son sanar dake , domin ina da tabbacin baza ki bani kunya ba."

Ta ce ,"In sha Allah Baba. "

Jin haka ya sa ya cigaba da cewa ,"Na yi magna da mahaifiyar ki , sannan na sanar da ita na tsayar da ranar auren ki."

Cikin mamaki da tashin hankali Fatima ta kalli Alaji

"Aure kuma Daddy." Cikin mamaki

Ya kalleta cikin sake jaddadawa ya ce ,"Eh Fatima aure , baki da mahaifin da ya fini , kuma zan yi domin farin cikin ki , duk inda zan shiga in fita domin sama miki farin ciki shi ne burina Fatima, kuma zan shiga dukkan hatsari domin baki kariya, wannan shi ne za'bin da na miki a matsayina na mahaifin ki Fatima. "

Ya yi shiru yana jiran Fatima ta ce wani abu

Jin bata ce komai ba ya sa shi cewa ,"Baki ce komai ba Fatima. "

Murmushi ta yi sannan ta d'ago kai tana cewa ,"Daddy ni fa 'ya ce a gare ka , na yi imani kana son farin ciki na , ka yi mini komai Daddy, wallahi na amince da wannan auren har cikin zuciya ta."

Wani abu Alaji Mustapha yaji ya takure masa ran sa na farin ciki da matukar tausayin Fatima

Cikin ajiyar zuciya ya fara sabuwar magana ,"Ban yi zaton abin dana shirya zaki kar'ba ba , ban yi zaton farin cikin da nake hangowa zan samu ba ." Kawai Alaji kuka ya fashe dashi cikin wani yanayi mara dadi

Hakan yasa Fatima tashi tsaye cikin tashin hankali tana cewa, "Dan Allah ka dena kuka , Baba ka haifa ne mene amfanina idan ban share maka hawaye ba kawai ka dena kuka dan Allah na roke ka."

Ajiyar zuciya ya yi mai zafi sannan ya share hawaye ya dubi Fatima

"Dole na yi kuka Fatima, domin a wannan zamanin akwai wahalar samun 'ya kamar ke, Allah ya yi miki albarka ya sa ki ciki da Kalmar shahada."

"Amin ya Allah Daddy." Abin da fatima ta fad'a ke nan

Kallon shi tai cikin kunya da son jin amsa ta ce ,"Da waye za ai Daddy. "

Sai da ya yi mata murmushi ya gyara zama kana ya ce ,"Zumunci mai kyau Fatima zamu kasance har a aljanna tare , Yaron Alaji Mansur wato Kamal. "

Dauuuuuu

Abin da zuciyyarta ta fad'a ke nan , tasan dai da cewa Alaji Mansur guda daya ne kuma haka Kamal shi ne d'anshi wanda ta sani

Murmushi ta yi kawai ba tare da cewa komai ba domin karta 'batawa mahaifinta yanayin da yake ciki

"Allah ya faran ta maka Baba ya cika muradan ka."

"Amin Fatima ki fara shiryawa a sanarwa ga duk wanda ya dace , sannan kamal din yana nan zuwa."

Wata zabiya ce ta rad'o sallama cikin falon , hakan ya sa maganar tasu ta dakata

Sa'arr Fatima ce ta shigo gidan cikin shiga da zamu iya cewa matar aure ce

Nan ta durkusa suka gaisa da Alaji cikin ladabi da biyayya .

Sannan su kai cikin daki da Fatima

Bayan sun gaisa Fatima ta kwanta kan gado kamar mai shirin bacci hakan yasa kawar tata mai suna Fiddausi ta ce ,"Fatima ke nan hala dai kina da damuwa."

Sai da Fatima tai wani irin kashe idanu tana kallon Fiddausi sannan ta tashi zaune tana cewa, "Rasss nake kawata , kawai dai ina sanar dake mun kusa shigowa sayun ku."
Ta karasa maganar cikin kasalalliyar murya

Dariya Fiddausi ta yi tare da cewa ,"Kina nufin fa aure ke nan ."

Nannauyar ajiyar zuciya fatima ta aje tana cewa,"Kwarai kuwa nan da wata guda ma."
Chapter 2 · 0% Book details