← Book details Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 20

Sashe 18

Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na shigo baki sani ba kina ta tunani haka."

Ajiyar zuciya ta yi sannan ta gyara zama tana cewa .
"Gobe za a koma kotu Nasir, bani da wata hujja, bani da kwarin gwiwa, dole rayuwata baza tai mini dadi ba ."

Nasir shima ya yi ajiyar zuciya yana cewa.
"Aunty, akwai abin da zan fada miki , wata kila ya zama wani abin daban ."

Da sauri Fatima ta kalleshi tana cewa.
"Ina jinka Nasir."

Ajiyar zuciya ya kuma ajewa me zafi sannan ya ce .
"A ranar da abin nan ya faru aunty Fatima ina gida babu inda naje , ina tsoron zama abin zargi shiyasa ban yi bayani ba , amma wallahi bansan komai game da mutuwar mommy ba duk da ina cikin gidan."

Da sauri Fatima ta gyara zama tana fadin .
"Karka damu Nasir ka sanar dani duk wani abu da ya faru wanda ka sani , kuma wanne dalili ne ya hanaka zuwa makaranta a wannan ranar bayan ka tafi ."

Nasir ya fara mata bayani filla- filla kamar yadda take da bukata .

"Haba Alaji dan Allah yanzu haka gobe za a koma kotu , kana gani wannan yarinyar tana wani tsare Hajjiya Binta da tambayoyi harda rashin mutunci a kotu ."
Hajjiya Rukayya ta fada tana kallon Alaji Mustapha

Ita kam Hajjiya Binta kawai ta sunkuyar da kai

"Ya kamata a yi wani abu akai Alaji amma wannan bai kamata ba , kuma duk fatima tana zargin Hajjiya Binta ne da zata kashe hajjiya Samira .Amma ka yi shiru akai ."
Ta karasa maganar ta

Alaji Mustapha ya kalli Hajjiya Rukayya
Sannan ya fara cewa .
"Idan zaki ja da shari'a ne ga hanya , banda rashin hakuri irin naki ki bari gaskiya ta bayyana mana, kuma fatima babu wani abu da ta yi ko kece abin da zaki ke nan ."

A lokacin ne Habib da Khalid suka shigo

Hajjiya Rukayya ta ce .
"Ai shi ke nan ."

"Kotu ta shirya cigaba da sauraran bangarori ."

Cewar alkali
Barrister Nuhu ya kalli Barrister Fatima
Barrister Fatima ta jefa masa murmushi😇

Autar Marubuta ce 😤

FATIMA DA ZARAH🎀
Na
Autar Marubuta
________________________________________

*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><

Editing❌

Page 42 & 43

Barrister Fatima ta tashi ta nufi wajen Hajjiya Binta dake cikin akwatin tuhuma

Sannan Barrister ta kalli alkali tana fara cewa .
"Ya mai girma mai shari'a, kowa ya sani sanda aka kashe hajjiya Samira mutum biyu ne cikin gidan, amma ya mai shari'a wannan a zahiri ke nan ."

Alkali ya sake gyara zama yana sauraran Barrister Fatima, tare da kowa hankalinshi yana wajenta .

"Ya mai girma Hajjiya Binta ta boye mana cewa Nasir yana cikin wannan gidan , a baya da haka ma d'an gidan yayan ita Hajjiya Binta ya shigo cikin gidan yayin da wannan kisan yake gafff da faruwa."

Wani firgici ne ya mamaye zuciyar Hajjiya Binta, taji duk ta rude ta razana

Babban tashin hankalin ta ma saida Barrister Fatima ta matso kusa da ita tsoronta ya bayyana a zahiri

"Malama Binta me yasa kika boyewa kotu wannan.Bayan kin sani sarai wannan ya sake tabbatar wa akwai abin da kike boyewa kotu."

"Ina da jahh ya mai shari'a." Barrister Nuhu ya yi hanzari ya fada

Alkali ya kalleshi da cewa .
"Kotu ta baka dama."

"Barrister Fatima tana son dawo mana da shari'a baya ya mai shari'a, tare da shirin sanyawa Hajjiya Binta maganar da bata da tushe cikin bakin ta ."
Barrister Nuhu ya 'kar'kare

Alkali ya mayar masa da cewa .
"Barrister Nuhu kotu guri ne na sauraran bangarori , ka bar barrister Fatima ta fito mana da abin da take son kotu ta sani ."

Barrister ya koma ya zaunazauna

Fatima ta kalli alkali tana cewa .
"Ina rokon wannan kotu mai adalci data bani dama domin fito da babbar shaidar nuna cewa dan Hajjiya Binta yaje wannan gida domin kare inkaren barrister Nuhu ."

"Kotu ta baki dama ." Alkali da babban murya ya fada

Nan Nasir ya fito ya tsaya, tun a gida kamar yadda Fatima ta bukaci kar yaji tsoro komai ya tsaya cikin kwarin gwiwa , haka Nasir ya tsaya babu wani tsoro a tare dashi

Sannan ta matsa kusa dashi tana cewa .
"Malam Nasir shin mene ne tsakanin da Kamal ."?

Nasir ya ce .
" Shi yayana ne kuma gidansa nake zaune ."

Fatima ta ce .
"Alhamdulillah, kana nufin wannan kisan ya faru kana gidan ke nan ."?

Wani tsoro ne ya ziyarci Nasir dajin wannan magana ta Fatima

Yayi saurin fara cewa .
" A'a ba haka nake nufi ba. "

"Zaka iya sanar da kotu abin daka sani a wannan ranar , bayan kuma kana da lecture a makaranta, amma ka kasance a gida ."

Ajiyar zuciya Nasir ya yi sannan ya fara magana .

"A wannan ranar kowa na gidan ya sani har ita marigayiya Hajjiya Samira cewa zanje makaranta, domin a gaban idanunsu na tashi na tafi dakina a domin shiryawa , bayan na fara shiri sai ga kiran aboki na yake tabbatar mini professor bazai zo makarantar ba .

Hakan yasa na fasa zuwa makaranta kuma nayi farin ciki da hakan

Ina kwance a daki sai ga kiran wayar abokina wanda shi kamar d'an yake gurin Hajjiya Binta yake sanar dani cewa zai zo wai yana jin yunwa . Ni kuma nace kar ya zo amma yace sai yazo ."

Ajiyar zuciya ya yi sannan ya dora.

"Na fada masa zan masa rashin mutunci idan ya zo , amma saida ya zo hakan yasa ban fasa yi masa rashin mutunci ba ya fita cikin fusata , wanda babu jimawa na jiyo kuka a falo, amma ni sam bansani ba cewar ma Hajjiya Binta ta zo wannan gidan ."

Barrister Fatima ta kalli Nasir tana cewa .
"Nasir kotu zata so taji wanne dalili ne yasa baka son zuwan wannan abokin naka ."?

Nasir ya ce
" Saboda ya sha sa na rasa damammaki na cigaba a rayuwata, karatu na wanda sanadinshi aka kore mu a makaranta, sannan yayana Kamal ya bani dama ta karshe , shi yasa nake gudun wannan abokin nawa domin gina rayuwata. "

Fatima ta yi murmushi tana cewa .
"Kana son sanar da kotu ba abokin kwarai bane ke nan ."?

Nasir ya ce .
" Haka ne domin har shaye-shaye yana yi."

"Mene sunan abokin naka ."? Ta tambaya

A takaice Nasir ya ce .
" Abba Alaji. "

Barrister ta yi murmushi ta kalli alkali ta fara magana

"Ya mai girma mai shari'a, ina fatan wannan kotu mai albarka ta fahimci wannan sako na Nasir, Hajjiya Binta tana falo Abba Alaji ya shigo , sannan tana falo ya fita , babu jimawa kuma kisan ya faru ."

Ta kalli Hajjiya Binta tana cewa.
"Shin ko ke da Abba Alaji kuka kashe Hajjiya domin wata manufar."?

Cikin matukar hassala da babban murya Barrister Nuhu ya ce .
"Ina da jah ya mai shari'a.

Barrister Fatima tana yunkurin juya wannan lefi ga Hajjiya Binta har ma ga dan yayanta ."

Ya kalli Nasir yana cewa .
"Malam Nasir kana shaye-shaye."?

Nasir ya ce .
A'a ko cigare ban taba sha ba."

"To me yasa kake son cinnawa abokin ka wuta har kake kiran yana fita wannan kisan ya faru , shin kaima ba abin zargi bane ."?

Nasir kamar yadda yaji jan kunne na Fatima kan karya ji tsoro ya fara magana cikin kare kai

" Ita Hajjiya Binta shaida ce , tunda ta zo bata ganni ba , har Abba Alaji ya shigo ya fita bata ganni ba ko da wasa , ta ya kuma zanzama abin zargi bayan wacce aka kashe tana tare da ita ."

Wani murmushi fatima ta saki najin dadin yadda Nasir ya bada amsa lokaci guda kuma tana kallon ZARAH

Sannan ya koma gaban Zarah yana cewa .
"Shin kina ina sanda wannan yaron ya shigo ."?

Zarah tai ajiyar zuciya mai zafi kana ta ce .
" Ina cikin daki, sannan ban ma taba ganin shi ba , kawai sunanshi..."

Barrister Nuhu ya dakatar da ita da cewa" kin bani amsa ta ".

Sannan ya yi godiya
Barrister ya koma ya zauna

Fatima ta kalli Hajjiya Binta tana cewa.
"Zaki iya fada mana dangane da shigowar Abba Alaji cikin gidan, shin ya hadu da Hajjiya Samira ko ya akai."?

Wani yanayi ne mai matukar wuya ya rufe Hajjiya Binta, kowa yana hangar wannan yanayi na tashin hankali a tare da ita

" Kotu na sauraran ki ." Fatima ta sake tunatar da ita

Wani takaici ne ya rufe Barrister Fatima hakan yasa ta kalli alkali ta fara maganar da ta sake tadawa Hajjiya Binta hankali.

"Ya mai girma mai shari'a
Hajjiya Binta tana tsoron bayyanawa kotu cewa ita ta kashe Hajjiya Samira, wanda nasan da cewa da tasan Hajjiya Samira ciwonta ya tashi ,lokacin da ta zo Nigeria to da wannan zata fake , amma rashin sanin hakan yasa ta dorawa Zarah Sale kazafi na kisa.

Me yasa kika kasheta."?

" Ina da jah ya mai shari'a. "

Barrister Nuhu ya fada

Kotu taki amincewa da jansa

Hakan ya sa Hajjiya Binta ta fara kuka tana cewa.
"Wallahi ba haka bane akan mene zan kashe Hajjiya Samira, babu abin da ta yi mini duk da cewa mum yi zaman kishiyoyi, ni wallahi bazan iya kasheta ba ."

Barrister Fatima ta ce.
"To me yasa kike tsoron sanar da kotu cewa Abba Alaji shi ne ya kasheta. Tun da bake bace , shin kina tsoron a kashe shi ne ."?

Sabon kuka ta sake fashewa dashi

Tana cewa.
" A'a A'a ya mai shari'a, Abba Alaji ya shiryu.
Bani da burin da ya wuce naga wannan yaron ya samu rayuwa mai kyau , shima haka mahaifin sa .

Kwarai da gaske Abba ya shigo a wannan ranar ."

Cikin sabon kuka ta sake cewa .

"Ya shigo a wannan ranar , muna zaune da Hajjiya a falo
Kai tsaye ya shige dakin Nasir, Ni kuma a wannan lokacin nake cewa hajjiya ta bani turare na ,
Chapter 18 · 0% Book details