← Book details Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 20

Sashe 8

Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Barrister Fatima na saukewa ta sake d'auka da cewa ."A junior Barrister earns an average of £42,00 per year, while a senior Barrister earns up word of £132,000 annually.

To barristers ba abin wasan ki bane dactor Zarah. " Barrister Fatima ta rufe maganar da yaren Hausa

Murmushi Zarah ta yi na matukar alfahari da jih da kai sannan ta ce

."Yanzu wannan'kananun kudaden shi ne kika tadah jijiyoyin wuyah Fatima, wallahi sam ki ce wahala dai kuke yi .To kinsan mene ne salary na cardiologist dactor kuwa .

To interventional cardiologist salary is $ 356,000---$ 400,000per year, and electro physiologist salary is $678,495."

Zarah ta yi ajiyar zuciya kana ta cigaba da cewa
."Ki sa a ranki mu ba sa anninki ba ne Barrister Fatima Mustapha. "

Alkamin Autar Marubuta

07040805269
WhatsApp only

FATIMA DA ZARAH🎀

Na
Autar Marubuta

_________________________________________

*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><

Editing❌

Page 18 & 19

Zarah ta dora da cewa
."Mu cardiologist ba sa an nin ku bane Fatima, kuma kisa a ranki ko babu Lauyoyi to al'uma zasu rayu ."

Fatima ta yi murmushi kafin ta ce ."Ko babu likitocin zuciya, baza ai asarar al'uma ba , amma matukar bamu taimakawa mutane ba , mu lauyas a lokacin kuke samin hanyar cin abin cin ku da salary din da kuke takama dashi ,

Da zamu cire hannu mu daina shiga kotu , to tabbas ina tabbatar miki marasa lafiyan zuciya zasu karu sosai , amma idan muka hada kai muna yin aiki , to lallai a karshe zaku rufe asubitocinku , domin babu me zuwa gare ku

Rashin samun kulawar lauyoyi a al'uma ina tabbatar miki babbar annoba ce , amma a wannan yanayin marasa lafiyan zuciya zasu yawaita sanadin rashin samun kulawarmu da kwato musu hakki a cikin kotu ."

Zarah ta nutsu ke nan don shirin fara magana wata zabiya mai zazzakar murya ta doko sallama

Ji da ganin ran Fatima zai sake baci ya sa ta tattara kayanta ta nufi cikin dakinta .

Tashi Zarah ta yi tsaye tana murmushi tare da taro bakuwar tata kuma kawarta , nan ta zauna a falo suka gaisa

"Atika kin buya wallahi." Cewar Zarah tana magana da kawar tata da hankalinta ba ya kanta .

Atika ta yi kasa da murya tana cewa
."Wai fad'a kuke yi ne , na ga ta tashi ta shiga daki ranta a bace ."

Murmushi Zarah ta yi tana kallon kofar dakin Fatima, kana ta juyo ta na cewa

."Fad'an lafiya kuma Atika , ta dawo daga kotu ne , kinsan shari'a akwai wahala to gajiya ta yi shi ya sa ."

Atika taja tsaki tare da tabe baki tana cewa. "Aikin kawai ai wallahi kin bani mamaki Zarah kin kuma bani haushi da kunya ."

Zarah ta kalli Atika cikin matukar bukatar karin bayani

."Kunya fa kika ce , mene na aikata to ."

Atika ta gyara zama da samun guri ta ce ." Kina marubuciya , mai rubuta labarai kala-kala , amma kina zaune da kishiya , masoyanki ma duk abin haushi yake basu , karki ka yadda ake kus-kus a social media. "

Atika ta sake fad'in
"Gaskiya zamanki da kishiya bai yi ba , dan haka a sake lissafi kawai ta yi waje ."

Murmushin takaici Zarah ta yi , kana ta tashi ta koma kujerar da Atika take

Ta dafa ta tana fad'in

."Ni fa kawai 'yar Adam ce kamar kowa , matan Kamal su biyu ne Fatima da Zarah,
Abin da nake so ki sani Atika , Fatima bata damuna

Ina da kudi , tana da kudi
Ita lauya ce , ni kuma doctor ce
Tana da kyau , ina da kyau ."

Zarah taja ajiyar zuciya tare da cire hannunta a kan Atika

Sannan ta cigaba da cewa ." Bani da wata damuwar da zance sai tabar gidan nan , kuma maganar social media ni ban taba ji ba sai yau.

Idan ma ana yi , to a zo shafina a yi dani , amma ni bani da damuwa da Fatima. "

Atika da ranta ya matukar baci dajin zancen Zarah ta tashi tsaye

."Au haka ma zaki ce ."?

Zarah ta ce ."Eh mana ai gaskiya ce ."

"To shi ke nan Zarah, ki cigaba da zama da ita , Allah ya kawo ranar da zata nuna miki bakin halinta ."

Ta juya ta nufi kofar fita , kafin ta kai zuwa kofar
Ta juyo tana fad'in

"Kar ki manta darajarki ce da mutuncinki a ce Kamal ke kadai yake aura , na barki lafiya ."

Ta ja kofa ta fice

Zarah ta juyo ta kalli laptop din ta

Kana ta ce ."I kon Allah, ko ruwa bata sha ba ma , sai kace Fatiman a kanta take ."

Ta tabe baki tana fad'in.
Allah ya kyauta ya shirya mu ."

Ta zauna a kasa ta bud'e laptop ta cigaba da typing.

Wajen minti goma taji ana buga kofa , jin maza ne kuma ta shaidi murya , ya sa ta amsa sallamar tana tashi da daukar mayafi .

"Ku shigo ."

Cikin far 'a su Habib suka shigo gidan

Ita ma tana farin cikin ganinsu ta basu guri suka zauna

."Lallai kam yau an tuna damu ke nan , su Habib da Khalid, kamar mun yi laifi ."

Zarah ta fad'a cikin far 'a

."Hhhh wallahi ba haka bane kawai dai ayyukan ne sai a hankali. " Khalid ya fad'a yana kallon Habib dake murmushi

"To shi ke nan , ya gidan yasu baba ." ? Zarah ta tambaya

Habib ne ya ce .
"Lafiya suke wallahi suna gaida ku sosai ."

Fatima ta shiga madafarsu ta d'auko abinci ta zube musu , ta kawo musu kayan marmari

Khalid ya ce ."Haba dan Allah, sai ka ce baki ne mu ."

Zarah ta yi dariya, kana ta ce .

"To ai saboda ku ba ba'ki bane shi ya sa zaku cin ye min shi tasss , sannan na kira muku Fatima."

Dariya suka sake yi a karo na biyu

Habib ya ce .

"Wallahi ba yunwa muke ji ba ."

Zarah ta ce ."Okay saboda ba Fatima ba ce ke nan koh ."

Habib ya ce ."A'a wallahi ai duk kun zama daya ."

Ta kallesu da cewa .

"To idan gaske ne sai ku ci ai ."

Khalid ya yi dariya yana cewa
"Wallahi halunku daya da Fatima kun iya kafa tarko ."

Dariya sukai baki dayansu

Yayin da su Habib suka kai hannu suka fara shan wannan kayan marmari

Sannan Zarah ta nufi sahin Fatima ta kira ta

Sai gasu sun fito a tare

Da matukar farin ciki Fatima ta karaso wajen yayannin nata

"Manyan baki kam , gaskiya yaya Habib naji dadin zuwanku , kwana biyu duk kun manta dani ." Ta karasa magana tana zama kusa da kujerar da Zarah take tsaye

Khalid ne ya yi dariya kana ya kalli Habib yana cewa
."Wai kaji mun manta da ita ."

Kafin wani ya sake cewa komai Zarah ta sunkuya ta dauki laptop din ta tana cewa
."Bari na shiga na shirya yau night ne dani Fatima. "

Ta karasa magana tana kallon Fatima lokaci guda kuma tana cewa dasu Khalid

"Ku fa cinye abincin nan dan Allah."
Tana murmushi ta nufi sashinta

Ya yin da Habib yake cewa ."To mun gode sosai ."

Fatima da murmushi ta ce dasu
"Yasu Daddy ya ayyukan naku ."

Khalid ne ya ce
"Aiki kalau wallahi, suma gida lafiya

Amma naji ance kina shari'a ta dau lokaci, to ya akai haka."

Murmushi Fatima ta yi kana ta gyara zaman ta a kujera tana fadin

"Wallahi lamarin ne , amma in sha Allah ranar 20 ga wata za ai zaman karshe ."

Khalid ya ce .
"To masha Allah, fatan nasara ."

Fatima ta ce .

"In sha Allah yaya na gode ."

Ta kalli abincin da Zarah ta kawo musu tana cewa.

"Ku ci abincin mana yaya."

Habib ya ce .

"Keee mu fa ba yunwa muke ji ba kuma gashi min sha fruit."

Khalid ya kalli Fatima yana cewa.

"Ina Kamal d'in fa ."?

" Kamal bai dawo ba wallahi yana company. "
Fatima ta ba shi amsa

Kad'an sukai hira suka tashi kamar wanda aka muntsu suka tashi a tare .

"Haba Yaya muna hira kuma zaku tafi , to ku bari Kamal d'in ya dawo mana ai yanzu yana hanya ."

Fatima ta yi musu maganar yayin da suke a tsatstsaye

Khalid ya ce .

"A'a fa sai wani lokacin, ki gashe shi kawai ." Suka isa wajen kofar

Tana taka musu zuwa wajen kofa tana cewa a gaida mutanen gidan.

Habib yana sa hannu zai bud'e kofar

Nasir ya turo kofar ma'kale da jakar makaranta, ga dukkan alamu daga makaranta ya dawo .

Yana hada ido dasu ya sakar musu murmushi.

07040805269
WhatsApp only.

FATIMA DA ZARAH🎀
Na
Autar Marubuta

________________________________________

Editing❌

Page 20 & 21

"Ka ga sojoji barkan ku wai har zaku tafi ."
Nasir ya yi magna a sanda yake shigowa ciiki

Suma duk murmushi sukai fara masa kafin
Habib ya ce .

"Ai kuwa har zamu tafi ya makaranta, ya mancewa damu ."

Nasir ya yi dariya kana ya ce .

"To wallahi makaranta ce take boye ni , domin so nake kawai na kammala karatun nan na koma gidan mommy, yaya Kamal ya buden company na ."

Habib ya ce .

"To Allah ya taimaka Nasir."

Sannan ya basu guri suka wuce tare da sallama

Suna fita Fatima ta rufe kofar

"Aunty Fatima na dawo ."
Nasir ya yi magana da Fatima

Halinta na murmushi ta masa sannan ta ce .

"To sannu da zuwa ."

Ya shige dakinshi yana murmushi
Yana shiga ya aje jakar shi , sai yaji wayarshi ta fara ruri

Kafin ya cire takalmin kafarshi ya duba wayar don ganin me kira

Dogon tsaki yaja yana cewa.
"Abba Alaji ko mayen mutum wallahi."

Ya sake jan tsaki yana katse kiran

Kamal da Fatima ne zaune a falo suna kallo
Misalin karfe 8saura na dare
Chapter 8 · 0% Book details