Sashe 15
Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin Fatima ta fashe da wani kuka mai radadin gaske , dajin irin zancen da 'yan uwanta suke a kan ta .
A wannan yanayi ta fara magana cikin kuka tana cewa.
"Shi ke nan aunty, ku yi duk abin da kuke so ,amma ina so ku sani zan koyi da bayan Zarah , idan kun so ku dauko lauyan da zai sanya a kashe Zarah a zaman farko , ni kuma zan yi iya yina domin bayyana muku gaskiya, cewa Zarah ba tai kisa ba duk da bani da hujja , amma Allah ya sani kuma zai bayyana gaskiya."
Faruk ya ce .
"To shi ke nan sai mun hadu a kotun , amma ina tabbatar miki karki sake kukan rashin mahaifiya, kuma karki sake tunanin kina da wasu 'yan uwa a wannan duniya." Ya karasa magana cikin matukar zafi da fusata
Sannan ya kalli su Ahmad yana cewa .
"Ku tashi mu tafi zamu samu gida mu zauna, har zuwa kammala wannan shari'ar ."
Wani zafi Fatima taji ya daki zuciyarta dajin cewa zasu bar gidanta
Kamal ya fara basu hakuri amma Faruk ya tasa su a gaba tare da kayansu suka bar gidan.
Wani kuka Fatima ta sake rude wa dashi tana cewa.
"Ya Allah , yanzu mene laifi na dan kawai ina son bayyana gaskiya."
Ta kai kasa tana kuka mai matukar ban tausayi
Duk su Mahmud suka ji tausayinta ya rufe su , bari ma Nasir da hawaye suke zubo masa .
"Allah sarki aunty Fatima, dalilin Zarah dubi halin da take ciki ta rasa mahaifiyar ta kuma 'yan uwanta duk sun tafi sun barta , Allah Ka kawo mana dauki ."
Nasir ya karasa maganar a cikin zuciyarshi yana gangaro da hawaye .
.....
Kotu ta sanya ranar fara sauraran shari'ar Zarah da ake tuhuma da kisan kai , wannan zance yana matukar yawo a tsakanin masoyan rubutun Zarah Sale Salisu
A halin yanzu Fatima tana hanyar zuwa gidansu sakamakon kiran da Alaji Mustapha ya yi mata .
Cikin gidan Alaji Mustaphan kuwa Abba Alaji ne zaune a falo shi da Hajjiya Binta.
Abba Alaji ansha wasu manyan kaya , har da hula , saidai kayan ba wani kyau sukai masa ba , saboda bai saba sawaba kuma wannan halayyer tashi da 'yan shaye -shaye bai dena ta ba .
Hajjiya Binta ta kalleshi d murmushi tana cewa.
"Haba kai kuwa Abba wallahi har ka fito ka yi kyau , ai idan ka dore a haka Alaji zai ji dadi ."
Abba Alaji akai dariya kafin a ce .
"Ai in sha Allah na tuba aunty."
Ta ce ."To Allah ya tabbatar. "
A lokacin Hajjiya Rukayya ta shigo tana murmushi nan ita ma taji dadin ganin Abba Alaji a wannan yanayin .
Daga nan kuma su kai sallama ya tashi ya tafi
Nan su Hajjiya suka cigaba da hira yayin da Fatima ta shigo tare da sallama
Babu wacce ta amsa mata sallamar a cikinsu
Sai Hajjiya Rukayya dake cewa .
"To mene kuma aka zo yi mana gida , ai muma yanzu dole mu nisanta dake a kashe mahaifiyarki amma ko a jikinki banza mara ilmi ."
Fatima ta sunkuyar da kai cikin rashin jin dadin jin maganar ta hajjiya Rukayya.
Hajjiya Binta ma dorawa tai da cewa .
"An dai yi asara ma'asaranciya ."
A lokacin Alaji Mustapha ya fara sakkowa daga saman bene , yayin da ya hangi Fatima a kasa ne ya dakata da sakkowar yana cewa.
"Au Fatima ashe kin karaso to bismillah hawo sama ."
Ya juya ya koma , Fatima ta wuce ta barsu suna harararta suna tsaki
Tana karasawa saman ta samu guri ta zauna a falo , sakamakon nan ta ga mahaifin nata yana zaune .
"Ina yini Daddy."?
Ba tare da ya amsa ba ya ce da ita .
" Tashi ki hau kujera Fatima. "
Babu musu ta mike ta zauna
Bayan sun gaisa sai Alaji Mustapha yake cewa .
"Da gaske ne kun yi fada dasu Faruk kuma kin zabi kare zarah a kotu ."???
Ya jefa mata tambayar lokaci guda
Wani faduwar gaba Fatima ta ji ya ratsa mata zuciya
Cikin daburcewa da kame kame ta fara cewa ." Daman Daddy daman ."..
Alaji Mustapha ya dakatar da ita cikin gaggawa yana fadin .
"Dakata kawai amsata eh ko a'a ce ."
Cikin kwarin gwiwa Fatima ta ce .
"Eh haka ne ."
Ajiyar zuciya ya yi sannan ya fara cewa .
"Allah ya bayyana gaskiya ki je kotu ki yi abin da ya dace Fatima, domin ni yanzu na yarda da ke , kuma komai zai wuce Allah ya kare ki ya bada sa'a Allah ya jikan mahaifiyar ki ."
Fatima wani farin ciki taji ya rufe ta dajin yadda mahaifin ta ya goya mata baya ,
Cikin kauna ta kalleshi tana cewa.
"Daddy na gode da goyan bayanka , hakan yake nuna tabbatar zan samu nasara , babu wanda ya fahimce duk a cikin su , hakika Daddy ina kaunar 'yan uwana amma yanzu duk sun juya mini baya ."
Murmushi Alaji Mustapha ya yi yana kallon Fatima da cewa .
"Karki damu Fatima, ai komai lokaci ne , kuma gaskiya zata bayyana karki sa komai a ranki, idan Zarah ce ta kashe mahaifiyar ku , to tabbatar dole za a hukuntata amma Allah ne mafi sanin daidai."
Ajiyar zuciya ta yi tana fadin.
"Gaskiya ne Daddy , bani da shaidar cewa ZARAH bata kashe mommy ba , amma babban amincin yana daga zuciyata domin Zarah baza ta aikata ba ."
Alaji Mustapha ya ce .
"Allah ya sa mu dace Fatima."..
Fatima tana komawa gida ta samu kamal a zaune a falo , duk ya wani rame dashi yayi baki kamar ba shi ne ba
Murmushi kawai ya yi mata sanda ta yo sallama, saida ta karaso ta zauna sannan ya amsa sallamar.
" Daddy yana goyon bayana Kamal, har naji komai zai tafi daidai tabbatar
Yanzu na samu kwarin gwiwa."
Murmushi ya kuma yi na jin dadin batun nata yana fadin .
"Ai Daddy mutum ne mai fahimta Fatima hakika ina alfahari dashi matuka."
A lokacin Barrister Khadija ta turo kofar falon tare da sallama
Ta karaso
Nan suka gaisa da Kamal ta sake masa ta'aziyya sannan ya tashi ya shiga ciki .
Nan suka gaisa da Fatima tare da sake mata gaisuwa
Barrister Khadija ta kalli Fatima tana cewa.
"Duk kin rame wallahi Allah ya jikan Mom."
Fatima ta yi murmushi tana gyara zaman rigar jikinta tana cewa.
"Amin Khadija, to ya shari'a kin kammala ne ."?
Barrister Khadija ta yi ajiyar zuciya tana cewa.
" A wallahi.
Dama wani zance nake ji da ban gane kanshi ba , zaku shiga kotu sannan kuma kin tsaya domin kare Zarah Sale kin bar 'yan uwanki ."
Ta aje maganar tana wurgawa Fatima kallon takaici
Fatima ta yi murmushi tare da gyara zama tana kallon barrister Khadija.
Alkalamin Autar
Marubuta ne
FATIMA DA ZARAH🎀
Na
Autar Marubuta
________________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><
Editing❌
Page 36 & 37
Fatima haka kawai taji ta kasa cewa da Barrister Khadija komai
Hakan yasa ta kuma ajiyar zuciya
Gani da jin haka ya sa Barrister Khadija cewa .
"Okay ashe gaskiya ne ai dole ki rasa abin cewa , amma wallahi kin bawa ahalinki kunya , sannan kuma ina sanar miki Barrister Nuhu suka d'auka , sai ki shirya kare me laifinki da gaske ."
Barrister Khadija ta tashi tsaye tana cewa.
"Na tafi Allah ya kyauta sai mun hadu a kotun ."
Ta fita ba tare da Fatima ta iya cewa komai ba
A take a gun Fatima taji wani ciwon kai ya risketa mai matukar radadi
Kawai kujerar da take zaune ta kasheta ta fara bacci
Anan kuwa Alaji sani ne zaune a falo shi da matarshi
Matarshi Hajjiya Nana ta kalleshi da fadin
"Wai Alaji yau na ga duk farin ciki ya same ka , ko kuma ma batun yau na kula da hakan ba ."
Alaji Sani dariya ya yi yana cewa.
"Haba Hajjiya Nana kema dai kinsan farin cikina ba zai wuce Abba ba , kamar yadda bakin cikina ba ya wuce shi ne sula."
Dariya Hajjiya Nana ta yi tana fadin .
"Wannan haka ne muna godiya ga Allah da ya fara shirya mana shi ."
Alaji ya ce .
"Ina son yaron nan wallahi Hajjiya, halinshi ne bana kauna amma yanzu alhamdulillah."
Hajjiya Nana ta yi dariya tana kallon agogon dake dakin yayin da take kuma sauraran kiran sallar la'asar .
Fatima har yanzu tana falo tana bacci a lokacin Kamal ya fito daga daki yana kallon inda take kwance cikin mamaki
Da sauri ya karaso ya fara tashinta
Lokacin da ya ga ta bud'e ido tana mammatsa idanu tare da dafa goshi ya fara cewa .
"Haba Fatima kin san zamu je gurin Zarah, ga shi kwanaki kad'an ya rage shiga kotu amma kin kwanta bacci haba dan Allah idan na rasa Zarah ya zanyi ."
Wani abu Fatima taji ya sake tokare mata zuciya cikin bacin rai ta sakko ta tashi tsaye yayin da kanta ya ke sara mata ta fara cewa.
"Mene haka dan Allah, kowa ba ya iya fahimta , sanin kanka ne ina cikin tashin hankali kamal na rasa abubuwa da yawah saboda Zarah."
Wasu hawaye ne suka zubo mata cikin kuka da karyayyar zuciya ta cigaba da cewa .
"Ya zan yi ne dan Allah ni kam ."
Shima kamal cikin karyewar zuciya ya rungume Fatima a jikinsa yana ajiyar zuciya tare da cewa .
"Yi hakuri Fatima, wallahi ina cikin tashin hankali bana ga ne yanzu waye zan yi wa fada komai na babu dadi Fatima, dan Allah ki yi hakuri."
Fatima ta janye jikinta tana cewa .
"Bari na shiga na shirya sai mu tafi ."
Ta wuce ciki
Kamal ya zauna , a lokacin Nasir ya fito daga dakinshi yana isowa falo
Yayin da Kamal ya kula dashi ya fara cewa .
"Kai dama kana ciki ."?