← Book details Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 20

Sashe 14

Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><

Editing❌

Page 32 & 33

Zarah kawai bangon dake gefenta ta fara bi tana zamewa cikin mugun yanayi ,
Nasir da ya kasa gane lissafin kamar kanshi ya buga yake ji

Hajjiya Binta kuwa sai kuka

Ita kuwa Hajjiya Amina innalillahi wa innailaihir rajiun take ta ambata .

Kamal shiru ya yi yana jinjina lamarin ubangiji

Fatima kuwa babu hawaye a idanunta amma tamkar zuciyarta ta fito take ji

Karfin hali ta yi ta kalli Kamal tana cewa.
"A yanzu komai ya kare Kamal a sanarwa da kowa mu koma gida ."

Zarah wani kuka ta ruruce dashi tare da zaucewa cikin wata murya da baza a gane me take cewa ba ta kalli Fatima tana kauda kai tana fadin .
"Bani da idanun kallon ki Fatima. Fatima da idanun kallon ki Fatima."

Fatima ta fashe da kuka

Yanzu Alaji Mustapha da Alaji Mansur suke samin labari

Kafin ka ce komai kuwa zance ya isa saudiya.
Kowa aka kai masa labarin to zancen Zarah yana shigowa ciki

Dactor Ahmad ya tabbatar musu ba ciwon zuciyarta bane ya tashi har yayi sanadin mutuwarta , domin tun binciken farko da suka yi matakin ciwon shi ne dai harta rasu , kuma bai motsa koina ba , bare ya yi sanadinta

Nan Hajjiya Binta take tabbatar musu Zarah ce ta bangajeta ta fadi bata motsa ba rai ya yi halinsa

Alaji sale hankalinsu ya matukar tashi da samun wannan mummunan labari .

Karfe biyu Faruk da Murja,Ahmad da Najib suka iso Nigeria cikin matukar bakin ciki

Lokacin da suka zo , suka shigo cikin gidan .

Gida kuka wiwi na mutane ,har da su Barrister Khadija.

Haka waje karku ji yadda Alaji Mustapha yake kuka abin tausayi.

Zarah tana zaune idanunta sun yi jajir , tare da mahaifiyar ta

Faruk yana shigowa Fatima ta fada jikinshi tana kuka

Lokacin da Ahmad ya shigo ta koma jikinshi tana sake rurucewa da kuka .

"Daga kanta ta yi sama tana kallon yadda wata 'yar sanda ta shigo rike da ankwa

" Ina Zarah Sale ."

Cewar police din

Tashin hankali Fatima taji ya sake ziyartarta

Ta kalli Zarah tana ajiyar zuciya mai zafi
Zarah cikin kuka ta bar jikin mahaifiyar ta Hajjiya Sa'adatu tana tashi tsaye da cewa .
"Ni ce ." Tana kuka
'Yarsandar ta karaso gaban ta tare da ware ankwar tana shirin sa mata tana cewa .
"Muna zarginki da kisan kai , don haka zamu tafi dake domin bincike ."

Zarah kawai mika hannu ta yi , tana kallon mahaifiyar ta cikin mummunan yanayi

Hajjiya Sa'adatu ta fashe da kuka tana kiran sunan Allah

Fatima ta kasa cewa komai kawai kallon Zarah take Zarah ma tana kallon ta yayin da suka je gaff da fita
Zarah ta yiwa Fatima murmushi mai matukar ciwo.

Fatima wani abu taji ya daki zuciyarta na bacin rai
Kawai ta sake fashewa da kuka

A lokacin aka fito da gawar Hajjiya Samira.
Gurin ya sake rurucewa da kuka .
Ahmad da Najib ma kukan ne ya ke ce musu suka yi waje , suna fita waje nan ma wani tashin hankali ne , domin Alaji Mustapha suma ya yi

Faruk sam bai yi kuka ba , saida lokacin da ake sallatar gawarta lokacin ya ringa zuba nashi kukan kamar mai shirin ham'budewa

Allah sarki Alaji Mustapha .

Kowa haka ne kawai lokaci muke jira , domin mutuwa guda daya ce , sanadi kawai ta tara, Allah ka sa idan karshenmu ya zo mu cika da hasken imani .

Haka aka kai gawarta zuwa ....

Har dare ya yi wannan gida na Kamal kuka bai ragu ba .

Zarah kam tana nan a kulle cikin mummunan yanayi, domin su ma su Alaji sale da su Umar duk hankulansu a tashe suke .

Bayan kwana biyu

Duk suna dai zaune a falon Fatima suna ta juyayi

Ahmad ya ce .
"Ba a tara sani ga Allah, mommy ashe ajalinki yana Nigeria da bamu barki kin zo ba ."
Cikin matukar tausayi da karayar zuciya ya karasa magana

Faruk ya yi ajiyar zuciya ya kalli Ahmad yana cewa .
"Gobe zaku shirya mu koma Saudiya, domin zaman mu ba shi da amfani , idan aka yi addu'ar 3 gobe tafiya kawai zami , ita kuma data kashe mana mahaifiya doka zatai aiki a kanta ."

Murjanatu ta ce .
"To Allah ya kaimu , ai baza ta ci banza ba, sai an kasheta , Allah ya jikanki yayata ."

Hawaye suka zubo mata

Kamal duk wani yanayi mara dadi yaji ya mamaye shi
Fatima ta kalleshi tana cewa .
"Kamal a kan wanne dalili ne zarah zata kashe mommy."

Kamal da hawaye a idanunshi ya tashi ya nufi daki

Ajiyar zuciya Fatima ta yi sannan ta tashi ta bishi

Washe Gari

Bayan an gabatar da addu'a, su Faruk suka fara shirin tafiya, domin har sun yi wa mahaifin su sallama, nan yaci kuka ya ce su kula da kansu
Allah kuma ya basu hakurin rashi.

Umar da Faruk da Hajjiya Sa'adatu suna zaune a falo

Alaji sale ya fito cikin hanzari daga daki zuwa inda suke .

Duk tashi tsaye sukai ganin haka , kafin wani ya ce komai ya fara magana cikin masifa da takama

"Wannan wulakancin ya ishe ni, an ce musu bana son Zarah ne , haukan banza dan anga na yi shiru , kuma na yi shiru ne domin naga gudun ruwansu , ni na san Zarah baza tai kisa ba , dan haka yanzu gidan kamal din zani a yita ta kare ."

Ya fita harabar motoci , Mahmud da Umar suka bi shi .

Bayan su Faruk duk sun shirya , sun d'ebo kayansu daga gidan Alaji
Komai ya yi musu daidai domin kawai sallama zasi su tafi

Ana wannan lokacin ne suka ji ana kwankwaso kofa
Nan suka bada izinin shigowa

Kamal yana ganin wanda suka shigo ya tashi ya nufi wajensu .

Alaji Sale ya dakatar dashi da hannunshi da kuma karin magana yana cewa .
"Ba gurin ka na zo ba ."

Kamal yaja da baya ya tsaya cikin matukar mamaki

Alaji Sale ya kalli Faruk yana cewa.
"Wajen ka na zo wato ma tafiya zaku yi tunda kun fa an rufe 'yar iska mara gata koh."

Faruk yaja baya ya jingine akwatin shi yana cewa da Fatima.
"Waye wannan."?

Fatima cikin hawaye ta ce .
" mahaifin Zarah ne ."

"Ohoooo ! Wato kaine wanda yarka ta kashe mana uwa ke nan ." Faruk ya fada

Alaji Sale ya doka masa tsawa da cewa .
"Shiru ! Karka kuma kiran 'yata da ta yi kisa, daman na yi shiru in ga iyakarku , to yanzu komai ya kare ko ni ko koh."

Fatima ta fashe da kukan bacin rai da takaici.
Haka shima Kamal ya rasa inda zaisa kanshi

Faruk yayi murmushi yana cewa.
"Komai ya kare kuwa , dole a kashe Zarah yadda ta kashe mana uwa , domin rai bai fi raiba ."

Alaji Sale ya ce .
"Ni nasan a haife na haife ka , dan haka kawai mu hadu a kotu , zan ga dokar data isa ta kashe mini yarinya."

Najib dai basu ce komai ba .

"Kana ganin zaka kayo lauyan da zai wanke 'yarka , to ai shi ke nan mu hadu a kotun ."

Ya kalli Fatima yana cigaba da cewa .
"Fatima zata tsaya mana a kan wannan shari'ar ka je ka shigar da kara duk inda kake so muna jiran sammaci ."

Fatima ta sake fashewa da wani kuka mai matukar gwanin ban tausayi tana cewa .

"A'a, A'a Yaya faruk bana jin Zarah ta kashe mini mommy, zuciyata ta kasa amsar wannan yanayi, bansan mene ya kashe mommy ba ."

Cikin sabon kuka ta cigaba da cewa .
"Ni na zauna da Zarah nasanta nasan abin da zata iya .
Don haka ku yi hakuri, ni bazan tsaya muku a kotu ba , zan tsaya kare Zarah ne Yaya, zan kare Zarah a kotu shi ne abin da nake nufi ."

Dauuu kowa yaji zuciyarshi ta yi bugun mamaki da rashin gane inda maganar Fatima ta dosa.

Fatima ta cigaba da kuka

A wannan lokacin Ahmad ya dubi Fatima yana cewa.
"Ban gane mene kike nufi ba Fatima zaki kare wa ne ."?

Fatima cikin wannan kukan ta sake fadin .
" Idan har sai an shiga kotu , to ina nufin ku je ku nemi lauyan da zai tsaya muku, amma ni Zarah ..."

Kuka ya kuma cin karfinta

Babu I zuciyar Faruk da yake jin matukar mamaki na abin da Fatima take fada

Shi kuwa Alaji Sale dasu Umar duk jikinsu ya yi sanyi .

Murja cikin kishin Hajjiya Samira ta jefawa Fatima kallo tare da tunanin
"An ya kuwa Fatima jininsu ce ."

07040805269
Autar Marubuta

FATIMA DA ZARAH🎀
Na
Autar Marubuta
________________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><

Editing ❌

Page 34 & 35

Najib ma wani matukar mamaki ne ya rufe shi dajin zancen yayartashi ,

Murja cikin mamaki d takaici ta so fara magana amma bata samu damaba sakamakon Alaji Sale da ya fara cewa .
"Na gode Fatima, amma karki damu. Ni zan nemo lauyan da zai tsaya mini a wannan shari'a karki damu."

Fatima taji ajiyar zuciya tana fadin .
"Ka yi hakuri Daddy, amma bazan bari ka kira wani lauyan ba domin ..."

Fesssss fessss Fatima ta ji an dauke fuskarta da mari har guda biyu lokaci guda

Kamal duk ya rasa me yake masa dadi a wannan rayuwa.

Kowa kallon Faruk ya yi da yake huci , dalilin marin da ya ajewa Fatima

"Tunda haka kika ce , mu zuba mu gani duk inda zaki je ki dawo mu ne jininki , mun gode da butulci ."

Murja a lokacin ta samu damar magana ta fara cewa .
"Rabu da ita Faruk , asararriya mara kishin mahaifiyar ta , rashin zaman da kika yi da ita yasa kike jin tamkar ba mahaifiyar ki ba ."
Chapter 14 · 0% Book details