Sashe 16
Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nasir yayi murmushi yana cewa.
" wallahi Yaya Kamal ina ciki , na rasa mene yake mini dadi , shi ya sa na fito domin na tafi gidan Alaji. "
Kamal ya ce .
"To shi ke nan muma muna nan zuwa ."
Nasir ya nufi hanyar fita yana fadin .
"To sai kun zo ."
Bayan Fatima ta shirya suka nufi police station suna isa barrister Fatima ta tabbatar musu ita ce lauyan da zata kare Zarah kuma tana da bukatar ganinta .
Nan DPO ya bada umarnin a fito da ita .
Lokacin da aka taho da Zarah, Kamal da Fatima hankalinsu ya matukar tashi ganin wani mugun yanayi da take ciki
Da gudu ta karaso gaban Fatima ta zube a kasa tana kuka
Fatima cikin matukar dauriya ta sunkuya ta d'agota tsaye
Kamal kawai kauda kanshi gefe ya yi yana zubar da hawaye daga bisani ya sharesu ya dawo da hankalin shi gare su
"Ki dena kuka Zarah."
Cewar Fatima
Zarah cikin kukan ta fara cewa .
"Fatima Daddy ya zo ya kuma fadan ke ce zaki kareni a kotu , ina cikin mugun yanayi Fatima mara dadi , mommy fa ake zargin na kashe Fatima, dan Allah karki tsaya mini mahaifiya ba wasa ba ce." Ta sake fashewa da sabon kuka
Kamal ya share hawayen da baisan ma sun zu bo masa ba
A lokacin Fatima ta yi murmushi tana rike hannayen Zarah tana fadin .
"Haba doctor zarah, ko kin manta mommy kike kiran mahaifiyar mu , sannan kika bata kulawa yayin da ciwonta ya tashi .
Ni kuma kawai sai na zama kamar kowa ?
Kawai abin da nake so dake ki samu kwarin gwiwa ina tare dake , ki amsan dukkan tambayoyina Zarah ."
Zarah ta sake damke hannayen Fatima tana fara magana .
"Wallahi bansan komai ba Fatima, ina zaman jiran ki dawo na tafi asubiti, ina cikin daki na gama shiryawa, sai na fito falo , ina fitowa na ga Hajjiya Binta a kan mommy dake kwance a kasa tana kiran ta tashi tana jijjigata , da sauri naje wajen domin ina tunanin ko ciwonta ne ya motsa ."
Zarah ta yi ajiyar zuciya ta cigaba da cewa .
"Ina sa hannuna a jikinta , shi ke nan Hajjiya Binta ta fashe da kuka tana fadin na kasheta , har hakan ya yi sanadin zuwana nan Fatima ki dubi halin da nake ciki ." Ta sunkuyar da kai tana kuka
Fatima ta kalli Kamal , Kamal ya sunkuyar da kai
Fatima ta maida hankali ga Zarah tana cewa .
"Zarah mawuyacin abu ne ki kwantar da hankalin ki , ni na sani , amma ina tabbatar miki wannan shari'ar baza tai tsawo ba komai zai bayyana , domin yadda aka shirya komai cikin sauki ne , kuma Hajjiya Binta dole abar zargice ."
Fatima taja ajiyar zuciya tana kallon idanun Zarah da cewa.
"Bazan ce ki kwantar da hankalin ki ba , idan har wannan kalaman nawa basu sa kin samu sukuni ba ."
Zarah ta yi murmushi tana cewa.
"Har yanzu kina nan da halinki koh ."?
Fatima ta yi dariya ta ce .
" Kwarai kuwa dactor Zarah. "
Murmushi Zarah ta kuma yi tana kallon fuskar Kamal shi ma ya mata murmushi
Bayan Fatima ta gama komai suka dauko hanya suka dawo yayin da suka tsaya gidan Alaji Mansur.
Duk suna zaune a falo ,Alaji ne kawai bayanan, domin ita ma Laila ta zo
Kamal da Fatima suna shiga aga gaggaisa
Fatima ta ce wa mommy.
"Mommy ina Daddy na fa ."
Hajjiya Amina ta yi murmushi tana cewa.
"Baban naki da baya son zama waje guda , ai yanzu haka zaki iya ganinshi ya dawo ."
Nasir ya yi dariya yana cewa .
"Daddy manya ke nan Allah yaja kwana ."
Hajjiya Amina ta ce
"Fatima yaushe ne za a shiga kotun ne ? Allah dai ya bayyana gaskiya."
Fatima ta yi murmushi na ya’ke tana kallon Kamal sannan ta ce .
"Ai mommy komai zai zo da sauki ku ta ya mu da addu'a domin bani da wata hujja a hannu ."
Laila ta ce .
"Kaiii aunty kuma haka za a shiga kotun ."?
Murmushi na ya'ke Fatima ta sake yi sannan ta ce . " In sha Allah Laila ai zamu samu hujjojine daga lokacin da shi lauyan da zai tsaya musu zai gabatar da nashi hujjojin tom zamu samu makama ."
Nasir ya ce .
"Tabb Allah dai ya temaka .Lamarin naku sai ku aunty, a ce zaku shiga kotu amma vabu hujja ."
Kamal dai ya yi ajiyar zuciya tunda dai suka gaisa bai sake cewa komai ba .
Laila ta kalli mommy tana cewa.
"Wallahi mommy karki ga yadda masoyan Zarah suke matukar damuwa a social media , har wani program nake saurara a gidan redio da suke yi a kanta ."
Hajjiya ta ce .
"To ya za ai , haka Allah ya so .kowa da irin tashi jaraftar ."
Ta kalli Kamal tana sake fadin .
"Ka kwantar da hankalinka Kamal karka sa damuwa a rai ta maka illa duk wannan abin masu wucewa ne ."
Kamal ya kalli mahaifiyar tashi yana cewa.
"In sha Allah mommy." Yayin da suka hada ido da Laila sukai wa juna murmushi.
Sannan ya kalli Fatima yana fadin .
"Mu koma Fatima."
Kafin Fatima ta ce wani abu ne Hajjiya ta ce
"A'a dama ba wuni za ku yi ba ."?
Kamal ya tashi tsaye yana cewa.
" Eh mommy gida muka yi ga shi har zamu tafi Daddy bai dawo ba , a gaidashi ."
Hakan ya sa Fatima ta mike , nan sukai sallama sannan suka koma gida .
07040805269
WhatsApp only
FATIMA DA ZARAH🎀
Na
Autar Marubuta
________________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><
Editing❌
Page 38 & 39
A nan suma su Faruk sun shirya tsaf domin tunkarar kotun da za a shiga
A yanzu haka suna zaune da Barrister Nuhu suna tattaunawa
Murja ce ta kalli barrister da cewa .
"Wannan shari'ar zata dau lokaci kuwa barrister."?
Barrister Nuhu ya kalli Murja a domin bata amsa .
" Banajin hakan matukar ba wani babban lamari ne ya bayyana ba daga su wanda muke kara ."
Faruk ya ce .
"Gara mu yi mu gama mu bar kasarnan domin Wallahi zamanta ya ishe ni ."
Barrister Nuhu ya yi murmushi
Su dai su Ahmad babu abun da suke cewa rashin mahaifiyar su ma kawai ya ishe su .
........
A yau aka gabatar da zaman kotu na farko , kotu ta cika ma'kil da al'umma sai dai ba wani fafatawa akai ba alkali ya ce za a sake zama a ranar 17 ga watan da ake ciki .
Anan cikin gidan Alaji Mustapha duk iyalan nasa suna zaune ana ta hira domin har su Faruk yau sun kai wa mahaifin nasu ziyara , duk ya yi ya yi dasu kan su dawo gidan su zauna akwai isassun d'akuna amma suka 'ki saida suka je suka kama waje , haka ya hakura da su .
Su Habib da Khalid sun yi farin ciki sosai da ganin 'yan uwansu an sha hira an more , sannan suka koma gida .
Ranar kotu
Daga nan falo Kamal yana zaune yana jiran fitowar Fatima a domin su tafi
Cikin cikakkiyar shigarta ta fito ta yi matukar kyau sosai .
Kamal ya mike tsaye yana murmushi yana fadin.
"Ohhh my life , idan kika sa kayan nan matukar kwarjini ki ke mini wallahi, ina fatan nasara a gare mu ."
Fatima ta yi murmushi ta ce .
"In sha Allah, mu tafi kar mu makara."
Suka shige suka tafi
Mutane har sun fara shiga ciki , wasu kuma suna waje , ga 'yan jarida duk sun hallara ,a lokacin ne aka zo da Zarah , babu jimawa alkali ya karaso babu bata lokaci kotu ta fara gudana.
Nan Barrister Nuhu ya tashi ya mika gaisuwa ga alkali tare da gabatar da kanshi da mataimakansa .
Ita ma Barrister fatima ta mika gaisuwa da gabatarwa tare da abokin aikinta Barrister Muhd
Nan alkali ya yi rubutu cikin takardar dake gabanshi sannan ya d'ago yana fadin.
"Kotu ta shirya sauraran 'bangarori ."
Barrister Fatima da Barrister Nuhu suka hada idanu , sannan barrister Nuhu ya tashi tsaye da wasu takardu a hannunsa ya fara magana lokaci guda ya na mika takardun ga alkali .
"Ya mai girma mai shari'a.Dukkan alamu sun nuna Zarah Sale wacce ake tuhuma ita ce ta kashe Hajjiya Samira, sannan daga bangaren lauyan dake kareta babu wata shaida da suka bayyana mana da zata kore haka ."
Barrister Nuhu ya gyara tsaiwarsa ya cigaba da cewa .
"Ya mai shari'a Hajjiya Samira marigayiya tana dauke da ciwon zuciya, sai dai likitoci sun tabbatar mana wannan ciwon nata bai tashi ba har ta rasu , sannan shaidarmu wacce komai ya faru a gabanta Hajjiya Binta ta tabbatar min yadda komai ya faru kamar yadda za tai wa kotu bayani.
Duba da wannan bayanai ya mai shari'a, muna rokon kotu mai albarka da ta biwa Hajjiya Samira hakkinta a domin hukunta Zarah sale."
Barrister Nuhu ya matsa kusa da Zarah da take tsaye cikin akwatin tuhuma yana fadin.
"Zarah Sale mene ya sa kika kashe Hajjiya Samira."?
" Ina da ja ya mai shari'a. " Barrister fatima ta yunkuro ta fada da babbar murya
Alkali ya ce .
"Kotu ta amsa Barrister Fatima."
Fatima ta ce .
"Barrister Nuhu yana kokarin razana wacce nake karewa tare da shirin sanya mata magana a baki ."
Alkali ya kalli Barrister Nuhu yana fadin.
"Ka gyara barrister Nuhu ."
Barrister Nuhu ya ce .
"To na gode ya mai shari'a."
Barrister Fatima ta koma ta zauna
Barrister Nuhu ya baro gaban Zarah ya fuskanci alkali yana cewa.
"Ina son wannan kotun mai albarka ta bani damar gabatar da shaida ta gaba ."
Alkali ya sunkuya ya gabatar da rubutu sannan ya d'ago ya kalli Barrister Nuhu da cewa .
"Kotu ta baka dama Barrister."
Barrister Nuhu ya bukaci da Hajjiya Binta ta fito zuwa akwatin tuhuma