Sashe 4
Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Mene ka ce daddy." Zarah ta tambaya cikin jajayen idanunta na kuka
Alaji cikin kwanciyar hankali da nuna kauna ga Zarah ya fara cewa ,"Allah ya halicceki da kyau, sannan ya mahaifinki da mahaifiyar ki suna tare dake , sannan ga 'yan uwan ki masu baki farin ciki ."
Jikin kowa ya yi san yi yayin duk suke sake kasa kunne domin sauran mahaifin nasu .
Haka Alaji ya cigaba da cewa ," Baki ta'ba neman abu kin rasa ba , amma ga shi a yau kina kuka cikin bakin ciki sakamakon Allah ya jarabce ki da rashin Kamal. "
Zarah ta sauke kanta kasa cikin wani yanayi
Alaji sale ya ce ,"Idan Allah ya rubuta Kamal mijinki ne , to dole zaki aure shi , matukar Kamal yana son ki , komai daren dadewa baza ki bar zuciyarshi ba ."
Zarah ta dago ta kalli mahaifinta cikin sabon hawaye
Ba tare da jiran komai ba , ya cigaba da cewa ,"To sai mene idan Kamal zai auri wata !Abin da nake son ki sani , karki yadda duniya ta rudeki , karki yadda kibi rudin zuciyarki , wannan lamarin kar ya shigar dake wani hali kiji kin tsani Kamal ko matar da zai aura , sannan matukar kina son shi ko mata 3 ya yi ya ce zai aure ki cikon 4 karki yadda ki dubi wannan matan a gabanki domin zaki halaka , ni a matsayina na mahaifinki duk san da Kamal ya zo min da zancen auren ki , matukar kina son shi to babu makawa zami farin ciki , kuma mu yi shagali sosai na bajin ta da nuna babban gida ne mu."
Ajiyar zuciya Zarah ta yi tana jin farin cikin kalaman mahaifinta
Hakan ya sa ta fara magana ,"A gaskiya na gode Allah da wannan a hali daddy, matukar tsanar Kamal naji ta rufe ni kafin wannan maganar taka
Na gode daddy, ina fatan na zamo tamkar haka , yayin da damuwa ta samu 'ya'yanmu mu juya musu kaddararsu zuwa nasarori ."
Mahmud ya yi ajiyar zuciya yana cewa, " Gaskiya ne Zarah, babu iyaye kamar namu mu godewa Allah, sannan ina baki shawara ki d'auki maganar Daddy, domin amfaninta yana tare dake duniya da lahira ."
Murmushi Zarah ta yi tana kallon yayan nata tana cewa, " Daddy, mommy na rungumi kaddara , amma ina san ku sani ina san Kamal, ina bukatar addu'oinku idan kamal alheri ne gare ni Allah ya bani , idan aka sin haka ne Allah ya nisanta mu dashi." Ta karasa magana tare da radadin rashin Kamal hadda wasu hawaye a idanunta
A lokacin hajjiya ta ce ,"To alhamdulillah Allah ya muku albarka."
Umar ya ce ,"Amin mommy. "
Zarah ta koma ta kwanta kafar Hajjiya tana ajiyar zuciya, lokaci guda kuma tana yiwa Umar murmushi yayin da suka had'a idanu .
Fatima kuwa tun da gari ya waye babu wani sukuni a tare da ita domin yau Kamal zai zo , haka kawai take jin kamar Kamal zai zo mata wulakanci ne , haka dai ta runga zullumi a karshe ta shirya tunkararshi da dukkan irin fuskar da zai zo mata .
Hajjiya Amina ce zaune a dakin Kamal, yayin da Kamal yana tsaye yana sanya agogo bayan wata hula da ya sanya wacce ta hau kan fatar shi sosai , sannan ya matsa bakin mudubi yana fesa turare.
Yana gamawa ya juyo ya kalli mommy yayin da take masa murmushi
Murmushin ya'ke ya mata yana cewa, "Mommy zan tafi Allah ya sa ina zuwa wannan yarinyar ta ce ban mata ba da naji dad'i wallahi mommy."
Hajjiya Amina dariya ta yi tana kallon yaron nata wanda duk ya rame ya yi wani dogon wuya tana cewa
,"Banda abinka Kamal, ai ba yarinyar da zata ganka ta ce baka mata ba , ni dai kawai abin dana ke so da kai , kar ka yadda wani abu ya faru wanda ran mahaifinka zai 'baci, ka yi hakuri komai mai wucewa ne ."
Kamal ajiyar zuciya ya yi kamar mai shirin kuka yana cewa. "In sha Allah Mom bazan baku kunya ba , ko dan girman darajarku , zan rike wannan kaddarar na tunkareta a duk yadda ta zo min , zan nunawa daddy ya isa dani mommy."
Hajjiya wani dadin gaske taji dajin zancen Kamal
Hakan ya sa ta bud'i baki tana cewa. "Allah ya yi maka albarka, wannan umarnin na mahaifinka shi ne farin cikin mu."
Cikin wani yanayi Kamal da matukar tausayin kanshi ya ce. "Yanzu mommy shi ke nan na rasa Zarah."
Ita ma Hajjiya wani matukar tausayin d'an nata taji ya kamata lokaci guda, amma cikin kwarin gwiwa ta ce dashi
.In ji waye Kamal, Allah ne yasan mene ya tsara maka , rabon kwad'o baya hawa sama Kamal, ko ya hau sai ya sakko .Dan haka karka damu ."
Kamal ko kad'an zancen Hajjiya bai kwantar masa da hankali ba , haka suka fita daga d'akin suka nufi babban falon yayin da mommy take kara ja masa hankali a kan abin da ya dace .
Suna karasawa sai ga Nasir da Laila sun fito daga 'bangaren Alaji Mansur
Nasir sanye da wata babbar jaka a bayansa ta 'yan makaranta.
Mommy ce ta ce ,"To har ka fito Nasir ."?
Nasir ya ce ." Yes mommy na fito , dan Allah a cigaba da mana addu'a domin satin biyu zami mu fara jarabawa .Kuma kin san mu manyan yarah idan muka fad'i akwai damuwa mommy. "
Hajjiya ta'be baki ta yi tana cewa. ."Ka ga Nasir , kawai ka dage da abin da ya kai ka , kuma wallahi ina jan hankalinka kan yaran nan marasa tarbiya 'yan shaye-shaye , matukar kana so gobenka ta yi kyau dole ka barsu ."
Kamal ya girgiza kai alamun haka ne , sannan mommy ta cigaba da cewa
."Yanzu dai kamar wannan yaron na gidan Alaji Sani ai ba aboki ba ne ."
Hajjiya Amina mamaki ne ya rufe ta gani dajin yaron da take magana ya shigo kai tsaye cikin falon
"Ina kwana maman Nasir ." Abokin nashi ya fada cikin harshen turanci da muryar shaye-shaye idanunshi jajir dasu
"Haba Abba Alaji ya zaka shigo babu sanarwa." Nasir ya fada cikin takaici da haushi
Tsaki Kamal ya ja yana cewa, "Kai me ya sa baka da hankali ne , to wallahi duk ranar da ka sake zuwa gidan nan iya ka cinka can waje , zan matukar 'bata maka rai wallahi."
Abba Alaji ya sunkuyar da kai yana 'kun'kunai
"Ka fita waje ka jira ." Kamal ya sake fada cikin haushi
Abba Alaji ya bud'e kofa yana kallon Nasir da cewa . "Ka yi sauri fa ka fito ." Sannan ya fita
Tsaki Hajjiya ta yi tana fad'in ."Kun gani ba , Allah ya kyauta."
Nasir ya yi ajiyar zuciya yana cewa. "Ku yi hakuri mommy."
Kamal ya ce ."Ba dai wata matsala ko ." Ya yi maganar yana kallon Nasir
Nasir ya ce. "Babu komai Yaya Kamal na yi sallama da Daddy, zamu tafi ."
Nan su kai sallama baki dayansu , sannan Nasir ya fita ya samu Abba Alaji sannan suka d'auki hanyar Ibadan
Laila ita ma ta shige ciki, yayin da Kamal yake cewa da mommy. "Bari na tafi mommy."
Mommy ta ce ."To Allah ya tsare hanya , a dawo lafiya."
"Amin mommy." Kamal ya fada yana fita waje
Yana fita yaje bakin motarshi ya tsaya cakkk , sannan ya yi ajiyar zuciya yana cewa. "Kai rayuwa karki mini haka mana , amma ba komai ta bakin mommy din wataran sai labari komai zai wuce , duk abin da hakuri bai baka ba tashin hankali ba zai kawo shi ba. "
Ya shige motar tashi yana ajiyar zuciya, yayin da mai gadi ya bud'e masa get .
Bayan Kamal ya isa kofar gidansu Fatima mai gadi ya bud'e masa get , yayin da ya shigo ya yi burki ya fito
Mai gadi da gudu ya taho yana cewa. "Barka da zuwa Alaji, sannu da zuwa bakon barrister fatima."
Cikin mamaki da duhun maganar da mai gadin ya yi Kamal ya nanata cikin ranshi ."Barrister kuma ."
Sannan ya kalli mai gadin yana cewa. "Wato kasan da zuwana ke nan ."?
Mai gadin da shegen surutunshi ya kuma cewa ." Ai yalla6ai bani da aiki sai bacci , sai a zo ai ta hon bana ji .Hakan ya sa barrister fatima ta sanar min da zuwanka domin kar nai bacci , domin tasan hali na ."Ya karasa magana yana yankare baki yana dariya.
Shima Kamal dariyar ce ta kamashi , sai dai ya kasa gane mene ya sa ake kiranta Barrister
Daga can gefe Kamal yaji murya tana cewa. "To sarkin surutu Haruna mai gadi ."
Kamal ya juya da murmushi dan ganin waye
Alkalamin
Autar marubuta ne.
FATIMA DA ZARAH🎀
Na
Autar marubuta
________________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><
Editing❌
Page 10 & 11
Habib ne ya karaso cikin far'a suna gaisawa da Kamal
Yayin da mai gadin yake masa kirari ."Ka ga daya daga cikin sojojin mu , ka ga jarumi Habibu dan Alaji. "
Habib ya ce ."Dan Allah Haruna ka tafi ." Kamal yana dariya
Sannan mai gadin ya koma bakin aiki yana sake musu kirari
"To ya na same ku bro ."?
Kamal ya fad'a yana kallon Habib cikin farin ciki
A lokacin Khalid ya shigo yana tura kofa , yayin da me gadin shima yake masa kirari
Kai tsaye Khalid ya nufo wajensu Kamal yana cewa." Ahhh Habib bako ka yi ne ."
Yayin da yake mikawa Kamal hannu suna gaisawa
"Kaji ka Khalid, tom sirikin mu ne ." Habib ya bawa Khalid amsa
Cikin mamaki Khalid ya ce ."Au haba dai , ai wallahi ban gane shi ba." Ya sake mika hannu suna gaisawa
Wani farin ciki Kamal yaji ya rufe shi da ganin 'yan uwan fatima
Haka sukai masa jagora har cikin babban falo suka zauna
Nan Habib ya kawo musu kayan motsa baki , kafin kace komai kuma hira ta 'barke tsakaninsu