Sashe 8
Fatalwar Deborah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ban san iya lokacin da na ɗauka ina bacci ba,ko da na tashi da ƙamshin turaren Uncle Salem na soma cin karo wanda ya game ko ina na ɗakin.Na turo baki gaba kafin na dubi hijabina wanda na san da shi ne ya cire min shi ko shakka babu.Wanka na shiga,bayan na fito na yi sallar azahar don sallah na ɗaya daga cikin abin da na fi so a kaf cikin abubuwan ibada ita da azumi wannan kuma horarwa Uncle Salem ce tun ina ƴar shekara sha uku yake saka ni yin azumin Litinin da Alhamis,tun ina kukan yunwa har na kai na saba.
Ina zaune kan dadduma Ammy ta shigo,“yawwa kin sha maganin ashe ” shi ne abin da ta fara cewa.
Shiru na yi ina tunanin yaushe na sha magani amma ban tuna ba,amma tabbas da na tashi na ji bakina na zaƙin zuma.Na sake turo baki don kuwa tuni kwanyata ta hasaso min ina baccin ya bani magani.
“ Ammy ni yunwa nake ji” na faɗa kamar zan yi kuka,“ Sai ki je ki ci mana,ki taso ki kaiwa Daddy ƙarami abincinsa” ta faɗa tare da ficewa .Ina kukan sangarta na fita zuwa falo,cikin gunguni nake cewa Ammy “ duk ga ƴan aiki nan amma shine ba za su kai masa ba sai ni ”
Ta dube ni da mamaki kafin ta ce “ au! Dama can ƴan aiki ke kai masa abinci?”
Ba tare da na ce komai ba na nufi dianing na ɗauki ƙaton tray ɗin da aka jera komai nasa,na ɗauka tare da fita ina tafe ina turo baki har na isa sashen nasa dakyar na lalubo sallama can ƙasan maƙoshi na yi.
Bai amsa ba sai ɗagowa da yayi yana kallona kafin kuma ya mayar da dubansa kan system ɗinsa.Hakan yasa na ji haushi na ajiye tray kan table har na juya zan tafi na ji ya ce “ Naf!” na tsaya cak ba tare da na juyo ba ina jiran abin da zai ce sai kawai na ji tsayuwarsa a bayana.Da sauri na juyo muna fuskantar juna,idona tab tsoro nake kallon nasa da nake hango tsantsar ɓacin rai a cikinsu.
“ Ka yi haƙuri!” na faɗa murya na ɗan rawa.Bai ce komai ba ya kamo hannuna ya zauna da ni kan kujera,“ ki zuba abinci ki ci” shi ne abin da ya faɗa sam babu wasa a maganar sai ya je ya zauna ya ci gaba da aikinsa.
Ni kuwa kallo na soma ƙarewa kyakkyawar fuskarsa mai cike da yalwatacen saje da ɗan madaidaicin gemu,kan jajayen laɓansa na tsayar da ƙwayar idona waɗanda ke yin furucin da babu sauti da alamu wani abu yake karantawa.
Tamkar wacce aka yi wa dole haka na ƙanƙance ido ina karanta bakin nasa,na waro ido jin tamkar har da muryarsa ke yi min raɗa a kunne tana sanar da ni abin da yake cewa ɗin.
“ Ba ki ji abin da na ce ba?” ya jefo min tambayar,da sauri na mayar da hankali kan abincin haka na zuba na soma ci lokaci-lokaci ina satar kallonsa har na gama.
“ Kawo min wanda kika rage ɗin” ya faɗa ,sai na dubi plate ɗin yadda duk abincin ke cakule saboda miya da na zuba dayawa don ina son haka.
“ Uncle bari na zuba ma wani” na faɗa tare da ɗaukar wani sabon plate ɗin.
Ya ce “ wanda kika rage nake so”
Na ɗan ɓata fuska cike da kunya na ɗauka na kai masa,ya amsa ya ajiye shi kan system ɗin kafin ya soma ci hankali kwance .
“ Uncle wannan wane ne?” na tambaya ganin wani matashin soja baƙi an naɗe kansa da bandeji.
“ Wani ne” ya bani amsa,da ido na ƙara kafe hoton don kuwa ni dai yayi min kyau sosai har ban san lokacin da na ce “ yana da kyau sos...” yadda Uncle ya ƙware ya shiga yin tari ya hana ni ƙarasa abin da nake son faɗa,da sauri na je na kawo masa ruwa ya karɓa tare da rufe system ɗin ya soma sha kafin kuma ya miƙa min kofin ya je ya kwanta kan kujera mai zaman mutum uku yana wani jan numfashi tuni na tsure wuri guda ina kallonsa....
[28/02 10:12] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️
```LoVe aNd HoRrOr story```👽
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}
*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.
*FCWA*☀️
________________________
03
Jikina na ɗan rawa na isa gare shi ina mai zube wa ƙasa daidai kusan kansa na ce “ Uncle?” shuru yayi min bai ce komai ba haka ya ƙi buɗe idonsa,hakan sam ba ƙaramar barazana ba ce a gare ni don gani nake na yi masa laifi ne har ya sa shi ƙwarewa amma ban san taƙamaimai mene ne ba.
“ Uncle?” na ƙara faɗa wannan karon ina mai kai hannu ina gwale fatar idonsa a dole so nake ya buɗe su ya kalle ni,na kuwa ci nasara ya buɗe su sai dai yadda suka yi ja sosai har sai da na ji tsoro na ɗan ja baya.
Murya a disashe kamar wanda ransa zai fita yana kokowa da numfashinsa ya ce “ Nafisa me na faɗa miki? Ban ce kar na saki ko da wasa kin ce wani namiji yana da kyau ko kuma ki kalle shi ba?”
Na ɗan ja ajiyar zuciya tare da matsowa na ce “ ka yi haƙuri Uncle ba zan sake ba,amma saboda me Uncle? Ka ga fa duk ƙawayena suna da samari ni amma ka hana ni kuma...kuma kamar mai baƙin jini maza sun tsane ni ” shaaa hawaye suka zubo min tuna yadda ko a makaranta ƴan ajinmu ba su shiga duk abin da ya shafe ni,kusan kuma malamanmu maza ma haka ba kasafai suke saka ni yin wani abu ba,in an zo nan ta wurin ƙannaina da kuma mazan da suka zo karatu a gidanmu su ma duk hakan ce ke faruwa.
Ba tare da ya ce min komai ba ya tashi zaune haɗi da ɗan duƙewa ya dafe saitin zuciyarsa,ina ganin haka sai na miƙe da sauri har ina tuntuɓe na nufi bedroom ɗinsa na ɗauko masa maganinsa.Na cika kofi da ruwa tare da ɓallo ƙwaya biyu na miƙa masa ya karɓa tare da sha,cikin ƙanƙanin lokaci ya soma yin wata ajiyar zuciya kafin ya ce “ ki je ki haɗa kayanki,zuwa jibi sai na kai ki can ƙauyen da za ki koya”
Duk ƙuncin da ya cunkushe min zuciya ne ya tafi ban san lokacin da ƙawa zuci ya ja ni ba kawai na rungume shi ina cewa “ na gode sosai my Uncle,kenan har ka yi magana da Daddy ya amince wayyy!” na yi ihun murna ina jijiga bayan Uncle da na rungume tsam a ƙirjina kafin kuma na sake shi da gudu na bar falon.
Ina shiga ɗaki na tarar da family na cin abinci,ɗakina na nufa na shiga sauko da akwatina ko taimakon masu aiki ban nema ba na soma shirya kayana ina yi ina murmushi ina jin daɗi na luluɓe min ruhi.Sai hoton kaina nake gani a cikin aji ina koyar da darasi wa ɗalibaina,ban zauna ba sai na haɗa duk kayana na jiki da kuma jaka da takalma.
Takardu da littafaina ma trolly daban na ware musu kafin na miƙe ina yawo cikin ɗaki ina magana ni ɗaya kamar irin yadda malamai ke yi.A hankali na soma jin ciwon kan da ya zame min aboki tun na ƙurciya na ziyartata,tun ina daurewa har na kai na kasa jurewa na haye bed na kwanta.Mafarkin da na jima ban yi ba tun shekaru kusan uku shine na soma yi kamar ana jirana.
Tsaye nake kan ƙafafuna na mage ina juya idona masu matuƙar haske da hange nesa tamkar na Alhuduhudu. Manyan-manyan dabbobin daji ne a tsaye a gabana suna buɗe min bakunansu masu manyan haƙora yayin da ni kuma ke ankare da kowanne daga cikinsu kafin mu soma yin dambe ina jibgarsu duk na yi musu jina-jina da jini kafin wata halitta mai siffar babban sauro ta caka min bakinta daidai cikina .Azabar da ta ratsa ni ce yasa na saki wani razananen ihu,daidai nan na farka sai dai abin mamaki daidai wurin da aka cake ni ɗin har a zahiri ciwo yake yi min.
“ Lafiya Nafi?” Ammy ta faɗa wacce ta shigo yanzu hankali tashe,ido na soma juyawa amma na kasa faɗa mata don ko na ce zan faɗi abin da na gani a mafarki kamar abin tsayi sam bakina ba zai iya furtawa ba.
Hawaye kawai nake yi,sai shi ma Daddy ya shigo yana tambayar lafiya.Kai kawai na girgiza masa ,ya zo ya kamo hannuna ya ce “ kina ji na Nafisa faɗa min mafarkin me kika yi?” da sauri na janye hannuna daga cikin nasa,na diro daga kan bed na nufi ƙofa.
Sai kuma na yi tsaye ganin Uncle shi kuma zai shigowa gemunsa na ɗigar da ruwa da alamu alwala ce yayi.
Haɓata ya tallabo ta yadda zai iya kallon fuskata da kyau ,tsakiyar idona ya dinga duba yana wani motsa baki kafin ya ce “kin kuwa yi Azkhar yau?”
Idona na soma juyawa ina son kauce kallon nasa da ba ƙaramin takura min suke ba,sam babu daɗi ji nake kamar yana zuƙo raina ne.
“ Kin yi Azkhar na ce?” ya sake tambayata.
Kai na girgiza alamun a'a,don kuwa ban yi saboda tun asubah na samu saƙon cewa sunana ya fito a jerin waɗanda za su je bautar ƙasa wannan zumuɗin ya shagaltar da ni yin Azkhar kamar yadda na saba.
Ya sake ni kafin ya ce “ biyo ni” sai ya juya,haka na take masa baya ina waiwayen su Daddy muka fita zuwa can sashensa da yake waje.
Ɗakin Uncle Salem ciki biyu ne da falo,ɗakinsa guda na bacci guda kuma wanda yake zuba kayan maganin aljanu na ruƙiya.Direct ɗayan ɗakin muka shiga,kaina ne ya juya da na shaƙi warin magani iri-iri yayin da gefen cikina daidai inda aka soke ni ya soma motsi har sai da na danne wurin.