← Book details Fatalwar Deborah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 20

Sashe 14

Fatalwar Deborah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jakar kayana ya buɗe ya je ya ɗauko kayan baccina,irin rigar nan mai buɗewa ya saka min bayan ya zare ta jikina sai rumtse ido nake don ko bra ban saka ba saboda muddin ba fita zan yi ba takura min take.Shi ma irin rigar ya saka sai dai bai ƙulle tashi ba,ina ganin ya kashe hasken ɗaki ya kunna wutar ƴar ƙaramar waya sai ya ɗauko ƙaton blanket ya rufe ni kafin shi ma ya shigo ciki.Hannuna mai sanye da zobe ya kamo ya riƙe kafin yayi min rumfa da ƙirjinsa mai cike da yalwa gashi ta kwanta sai santsi take.

Wannan karon yana ɗora bakinsa kan nawa ji na yi kamar ya jona ni ga lantarki,tuni na ji duk jijiyoyin jikina sun dawo aiki.Na ƙanƙame shi gam ina yin numfashi da sauri-sauri,yayin da shi kuma ya ci gaba da shan yawuna kafin ya soma shayar da ni nasa can kuma ya cire bakinsa ya mayar da shi daidai kunnena yana cewa “faɗa min wa ya baku abinci jiya?”
Dukkan jikina rawa yake saboda sabon yanayin da na tsinki kaina,na tallabo bayansa da kyau na ƙanƙame shi ina jin lokacin da igiyar rigata ta since ƙirjinmu ya mannu da na juna sai na ji kamar raina zai fita tsabar shock.Murya na rawa na ce “ headmaster ne!” ina gama basa amsa ya ƙara lalubo bakina wannan karon har da romance yana yawo da hannunsa a duk sassan jikina.Ni dai duk abin kamar a mafarki nake jinsa ba zahiri ba saboda tunanina ba zaune yake daram ba,ban san lokacin da na yi bacci ba bugun ƙofa ne ya tashe ni.Na ware idona a hankali sai na ga Uncle a tsaye bakin ƙofa yana murza key,yana gama buɗe wa sai Inna A'i a tsaye kamar wacce aka fiddo daga rame.......

My book is only 500 via

2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822

Zuwa page 10 zan gama free page in sha Allah,za ki iya yin payment ɗinki tun yanzu.
[28/02 10:12] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.

*FCWA*☀️

________________________

08

Da wani irin sauri na gyara rigar baccina wacce na tuna sosai Uncle ne ya saka min ita .Na miƙe tsaye ina mai ci gaba da kallon Inna A'i wacce ta shigo ƙafafunta fututu kamar wacce aka fiddo daga kabari.Tana shigowa Uncle ya maida ƙofa ya rufe,sannan ya je ya zauna kan dadduma hannunsa riƙe da ƙaramar casbi.

“ Innarmu daga ina kike?” na samu kaina da tambaya.
Sai ta dubi Uncle Salem,ni ma sai na dubi bangaren da yake ina mai tambayar kaina ‘shi wannan a nan ɗakin ya kwana ko me?’ a nan take kuma kwanyata ta soma kawo min gogagen kilishen abubuwan da suka faruwa sai dai ba su fita sosai ba dishi-dishi ne ban ida tantance taƙamaimai abin da ya faru ba a tsakaninmu.

“ Bari har na yi wanka Nafisa, lokacin sallah ma ya gabato ” Inna A'i ta faɗa tare da nufar toilet.
Yadda na ji idonsa na yawo a jikina yasa na kai dubana gare shi,sai na ga ashe cinyoyina ne yake kallo bai ƙyaftawa.Duk sai na ji babu daɗi don dai bai saba yi min haka ba,na je na ɗauki hijabina na saka na yi tsaye har sai da Inna A'i ta fito daga wankan sannan na shiga saboda fitsarin da nake ji ya matse ni.

Wani irin tsoro ne ya kama ni ganin ina yin fitsari baƙi ƙirin da shi tamkar wani Lipton .Wani kuka ne ya ƙwace min tare da tashi ina yarfa hannu,ban san ta ya aka yi har Uncle ɗin ya ji kukan ba sai gani na yi ya shigo toilet ɗin sam kuma a wannan matakin da nake cikin tsoro ban ga aibun shigowarsa ba .

Wani irin sihirtacen kallo yayi min a tsakiyar idona da suke tsiyayar da hawaye kafin ya ce “ ki yi wankan tsarki ki fito, wannan dattin ciwon cikin da kika yi ne jiya ko kin manta har magani na baki?” yayi maganar yana jan ruwa fitsarin ya wuce,sai a lokacin na ji kunya tare da gyaɗa masa kai alamun na yarda.

Murmushi ya sakar min kafin ya fita,sai a lokacin na cire rigar baccin da hijabi.Wankan tsarkin na yi kamar yadda ya umarce ni kuma sai na ga ya kyautatu ɗin na yi shi.Bayan na fito sai na ga yana bai wa Inna A'i magani da murfin roba,ya fi kala uku maganin kafin kuma ya miƙe ya fita.

★Uncle Salem

Jiya a lokacin da Inna A'i ta ɗauki wayar Nafisa ,a cikin muryarta kawai ya ji hucin wani ruhi da ke jikinta.Bai kuma yi wani dogon tunani ba ya fahimci tabbas da matsala,can gida ya koma ya tattaro duk maganin da ya san zai buƙata kafin ya ɗauki hanyar garin Ƙwargwam.Abu guda ya sani shine ba zai iya rabo su daga ƙauyen can ba tun da har Innarsa Delu ta yarda ta bar su suka wuce alhalin kuma ta fitowa Nafisa a siffar ruhi.
Ko da ya zo kuma bai ga Inna A'i bai yi mamaki ba,ita kanta Naf ɗin ƙwayar idonta kawai ya kalla ya hango yadda guba ke son game dukkan jikinta.Abu biyu ne yasa ya bata maganin,na farko don ya ji wane ne ya ciyar da Inna A'i don samo mafita,na biyu kuma don karye abin da aka baiwa Nafisar a cikin shayi ta sha.
A jiya ba don yana son ceto Inna A'i ba babu abin da zai hana shi ya mayar da Nafisa cikakkiyar mace,sosai moment ɗin ya ja shi zuwa ƙarshen shauƙi.Ba tare kuma da ya fita ba daga nan inda yake kwance da taimakon zoben hannunta ya lalabo Inna A'i a can wani ƙasurgumin daji tana yi ta tafiya ita ɗaya kamar mahaukaciya saboda tun bayan fitarta zuwa mayar da kwanukan gidan headmaster a nan bakin ƙofar ɗakinsu ta ji kamar ta zurma cikin rame kafin kuma ta tsinci kanta wani wuri.Dukkan detail ɗin nan Uncle Salem ya gansa daki-daki,wanda kuma ko ita Inna A'i aka tambaye ta ba za ta kawo shi ba.

Yadda ta ji muryarsa kamar daga sama shi ya sa ta juyo baya ta fara dawowa gida kuma,ko lokacin da ta buga ƙofa daga cikin ramen ta fito sai dai Uncle ya toshe duk wata ƙofa da zai sa A'in ta fahimci wani abu.

Yanzu kuma da ya fito, tsugunawa yayi ya ɗiga wasu ruwa cikin ramen kafin ya rufe kwalbarsa ya saka a aljihu.
Masjid ɗin makarantar ya nufa wanda ake ta kiran sallah,yana isa ya shiga sawun gaba bayan yayi nafiloli sai ya zauna har lokacin sallar yayi .Tuni kuma masallacin ya cika aka tayar bayan an gama ne Uncle Salem ya juyo yana kallon headmaster wanda ya zauna kafaɗa da kafaɗa da shi.Ya saki wani murmushi kafin ya ci gaba da yin Azkhar ɗinsa,har sai da ya gama kafin ya basa hannu ya ce “ Assalamu alaikum ”

Headmaster cikin mazgewa ya miƙawa Uncle hannu suka yi musabaha wacce yayi da na sanin yin ta,don kuwa akwai kumfan magani a hannunsa na karye sihiri.
“Wa'aleykum Salam ! Fatan an sauka lafiya?” ya amsa tare da saurin janye hannunsa.

Uncle Salem ya ce “ lafiya lau alhamdullah ! Na zo duba wurin da matata ne za ta yi aiki ita da Kakarta sai kuma na ga wuri yayi kyau”

Cike da takaici headmaster ke kallon Uncle ,don kuwa tun zuwansa jiya akan idonsa na ɓoye ya sauka.Sannan sarai ya san da shi ne ya warware zare da abawar da ya ƙullawa Inna A'i,amma saboda ya iya munafurci shine zai ce masa wuri yayi kyau.
Cike da iya tako shi ma headmaster ya ce “ ai kuwa dai school Ƙwargwam na kula da malamanta har ma da ɗalibai”

Uncle wani murmushin ya sake yi kafin ya ce “ ni ne shaida,amma me yasa kuka bata ɗaki mai lamba uku bayan ita sabuwar zuwa ce?”
“ Ɗakin nada matsala ne?”
“A'a kawai na tambaya ne”
“In ba ta sonsa ai sai a canza mata”
“ A'a na faɗa ma wuri ne mai kyau,kuma lamba ukun ai ita ce daidai da ita surukar Inna Delu guda” Uncle ya faɗi haka ne ya na saka idonsa cikin na headmaster don yi masa gargaɗi kan cewa kar ya sake cutar masa mata in kuma ya ƙara yin kuskuren haka shi da shi shege ka fasa.Da sauri kuma ya miƙe ya barsa nan.


Bayan na gama sallah haka na tsure Inna A'i da tambayoyi sai ta faɗa min inda ta je amma sai kwana-kwana take yi min daga ƙarshe ma ta shige kitchen tana cewa “bari na haɗa mana breakfast ”
Na ce “ yau fa Litinin ko kin manta azumi muke ni da Uncle ”

“ A'a yau ba za ki yi ba,ki bari har Alhamis ” Uncle ya faɗa wanda ke shigowa.Na dube shi da mamaki jin yau shine ke cewa na ajiye azumi,“ Uncle ina yi fa” na faɗa kamar zan yi kuka ina kallonsa.Ya ɗauke kafin ya ce “a'a akwai maganin da za ki sha yanzu kafin ki ci komai” sai yayi gaba ya ƙarasa gaban jakarsa ya fiddo wata kwalbar zuma.

Ido tab hawaye nake dubansa,ya ɗago ya kalle ni kafin ya ce “za ki zo ki sha ko sai na zo nan na ɗauko ki na matse miki baki tare da ɗura miki shi?”

Jin ya fito a Uncle Salem ɗinsa mai tsanani yasa na ƙarasa gabansa na yi zaune tare da tanƙwashe ƙafafuna.Da wata ƴar ƙaramar cokali ya soma bani zumar har sai da na sha bakwai da ita kafin kuma ya soma bani wasu sauran maganin,ɗaya kuma ya ce “ wannan kuma sai in kin ci abinci za ki sha” sai ya miƙo min na karɓa ina gunguni.

Yayi murmushi mai ɗan sauti kafin ya ce “ Naf sai yaushe za ki girma?”
Kamar suɓutar baki na ce “ ranar da ka yi min aure”
Chapter 14 · 0% Book details