← Book details Fatalwar Deborah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 20

Sashe 6

Fatalwar Deborah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayi ɗan murmushi don kwantar mata hankali ya ce “ ba ki san kusan duk kowanne gida NAUSHIN WUTA (Ameera Adam) mazajensu ke yi ba?”

“Kar ka yi ɓarnar bakinka don wallahi ba zan yi BIYAYYA(Mai ƙosai) a gidan auren da ake cutata ba” ta yi furucin tana mai banko ƙofar ɗaki ta fito ba tare da ta yi la'akari da tsawon dare ba,FATALWAR DEBORAH wacce tun ɗazu take tsaye ƙiƙam ta yi wuf ta shige gangar jikin Sakina nan take kuma ta ɗauki controling tunaninta,cike da iya tsafi ta ƙarawa jiki da fuskar Sakina shekaru ta yadda ba kasafai za ka gane eh ita ce ba.

Daga nan direct gidan Uncle Salem ta zo,ba ta wani sha wahalar fiddo Mamar Sadauki tsakar gida ba sai kuma ta fara buga ƙofa.Baiwar Allah Mama ta zo ta buɗe mata ,kawai sai ta fashe da kuka tana cewa ta taimaka mata ba ta da kowa.Abin ka da dama an juye ma kwanya haka Mama ta shigo da ita cikin gidan,a washegari kuma ta gabatar wa da Uncle Salem da ita a matsayin ƴar aiki,shi sam hankalinsa ba kwance ba saboda tashi da yayi ya ga Nafisa ba ta kan shimfiɗa har ɗakinta kuma ya je nan ma ba ta nan.

★Nafisa

A hankali duk kambun maitar da ke jikina ya fice na dawo normal,sai dai kafin ma na kai ga yi mata godiya na ji tana cewa “zan ara miki ƙarfin ikona ta yadda za ki yaƙi abin da ya fito da ke daga duniyarki izuwa nan,ban son gardamar nan taki ki riƙe a barki ” ta faɗa tana mai yi min wani kallo na tsakiyar ido kafin ta ci gaba da cewa “ki faɗa min wacce siffa kika fi so? Ina nufin cikin dabbobi me kika fi so?”

“Ban son ko ɗaya” na bata amsa.

“Me kika fi tsoro to?”

“Ƙadangare” na bata amsa.

Sai ta saki wani murmushi kafin ta yi wa ƴan matan nan magana ta aike su wata maƙabarta tana son su tono mata kabarin wani su kawo mata shi.

Babu jimawa suka je suka dawo ɗauke da wani abu cikin farin ƙyalle,kan teburi suka ajiye shi tare da buɗe shi.Gawar wani ƙadangare ce na gani har ya bushe kana iya ganin ƙasusuwansa.

Wasu harufa ta fara lissafowa yayin da kuma ta saka ƴan matan suka yi wani cercle suka kewaye mu suka sa mu tsakiya,wani furucin su ma suke yi cikin salon ɗaga murya yayin da ita kuma nata take yinsa a sauti ƙasa-ƙasa “Lazaaar! Laaazaaar! Ōÿānīÿēmį ” a hankali na ga ƙadangaren yana dawowa ɗanye haɗi da ɗan kumbura nan take tsoro ya kama ni,daidai wannan gaɓar ne kuma ta kama yatsana ta tsaga shi jini ya soma tsirta yana sauka kan jikin ƙadangaren kai kace dama jinin nawa ne yake so nan take ya soma motsi yana buɗe bakinsa.

Kalmar farko da ya furta ita ce “Gimbiya Sarah” a nan ne kuma na san sunanta,sai ta saki murmushi a lokaci guda kuma ita da ƙadangaren suka kalle ni.

Tsoronsa nake ji sosai,don haka da sauri na je bayan Sarah na ɓuya amma ta wani matsa ta yadda dole dai na fuskanci ƙadangaren wanda ke kallona da ƙattin idonsa.

“Shugabata!” ya furta,na waro ido jin wai ni ce shugabarsa.

“Nafisa wannan shi ne Lazar,wata ƙawata ce da muka yi rayuwa da ita duniyar bil'adama ta ƙyarƙyare shi ta hanyar tsafi.Yana da matuƙar power na san zai taimaka miki sosai,abin da nake so da ke dai shine kawai kar ki yi gardama har mu kammala aikin nan kin ji ko?”

Kai kawai na gyaɗa mata,sai ta ƙara bani umarnin na zauna.Jikina na ɗan rawa na yi zaune ,yatsana ta kamo wanda ta tsaga ɗazu.A gaban idona ba mafarki ba ta kamo shi Lazar ɗin ta saka min shi ta cikin ƴar tsakar da ko allura sai an yi da gaske ta wuce amma ƙaton Lazar ɗin ne ya shige tsaf,wani iri na ji bayan ta gama shigar da shi.

“Ki lumshe idonki me kika gani?” Sarah ta faɗa .
Na kuwa lumshe su nan na hangi FATALWAR DEBORAH tana shayar da Abidah wata gubar maita,so take a dole dai sai ta cutar da ƴata.Ban san lokacin da hawaye suka zubo min ba,abin da na gani ɗin na sanar da Sarah ita kuma sai ta ce “ƙarfin ikon fatalwa yana ƙaruwa ne ta hanyar shan jini kawai, wannan dalilin yasa ta zaɓi Abidah matsayin wacce za ta dinga yi mata farautar rayukan mutane tana kamo kurwarsu ita kuma sai ta tsotse jinin.Yara da yawa Mayu na amfani da su don yi musu bauta,saboda shi yaro sam ba za a zarge shi ba amma hakan tana faruwa ne ga iyaye masu sakaci wurin yi wa ƴaƴansu addu'ar bayan asubah kamar yadda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yayi mana umarni da mu dinga karanta musu wannan addu'ar *A'UZU BIKALMATILLAHI TAMMA,MIN KULLI SHAITANIN WA HAMMA,WA MIN KULLI AYNIN LAMMA* ”

Idona ba su bar fitar da hawaye ba na ce “in kuma mutum bai iya karanta Larabcin ba?”

Ta bani amsa da “ sai yayi da Hausa don Ubangiji yana jin kowanne Yare sannan yana amsar addu'ar bayinsa ”

“To ki faɗa min da Hausar don halin yanzu ma ji nake kamar ban yi karatu ba”

“Ina neman tsari tare da tawwasali da kyakkyawan zantukan na Ubangijina da ya kiyaye Ni daga sharrin dukkan dodanni,daga sharrin dukkan wasu dabbobi masu dafi da kuma sharrin dukkan wata ido mai cutar maita ”

“Na gode! Yanzu wacce hanya zan bi na koma gida?” na tambaya,shuru ta ɗan yi kafin ta ce “gaskiya ba zan yi miki ƙarya ba,komarwaki ba yanzu ba sai dai kina iya balaguron ruhi ki je kuma ki dawo”

Ban gane abin da take nufi ba,da na tambaye ta kuma sai ta ja ni muka wuce can gidansu.Sosai na yi mamakin yadda duniyar ƙasan ruwa ma take ɗauke da gidaje da kuma iyalai,iyayen Sarah suna da kirki sosai na samu tarba mai kyau na ci na sha sannan muka wuce ɗakinta mai ɗauke da gado da komai na buƙatar mace.

Kasancewarmu cikin ruwa ba shi ke nufin ka yi wanka ba a'a,har da toilet ke da kwai da kuma abubuwan gyaran jiki.Haka na shiga na yi wanka ina ta mamakin duniyar,bayan na fito sosai na ƙara wani mamakin ganin kayan jikina a saman gado.

“Ki yi sauri ki shirya domin ki ziyarci mijinki,in kin je ki sanar da shi duk abin da ya faru zai fahimce ki sannan ki aje hankali ki sama masa nutsuwa”

Ni dai banda kallonta babu abin da nake yi,ban bari ta yi min kwalliya ba sai da na yi sallolina sannan na shirya cikin wata haɗaɗiyar rigar bacci.Turare na fesa sannan na ce “yanzu ya za a yi na je can ɗin?”

“Kin fiya sauri kamar zawo,ki jira mana ina haɗa jirgin balaguron ne”Sarah ta faɗa tana mai zana gidan gizo-gizo,bayan ta gama ne ta umarce ni da na lumshe idona sannan na ratsa ta cikinsa haka kuwa aka yi.

Ina yin yadda ta ce sai na tsinci kaina a gidan Uncle Salem,a cikin ɗakinsa ban bayyana ko ina ba sai a cikin madubi.Ya fito daga wanka ƙugunsa ɗaure da towel yana goge gashinsa da ɗan ƙarami,sai na ga ya fara buɗe ƙofofin hancinsa alamun ya ji ƙamshi jikina kenan .Na saki murmushi na ce “kawo na taimaka maka na tsane ma jikin” da sauri ya juyo muna kallon juna,kafin ya ce “Naf?” na yi murmushi na ce “ka taimaka min na fito”

Hannunsa ya miƙo ni kuma na ɗora nawa ya jawo ni,na yi tsalle na ƙanƙame shi.Ya ce “ina jin ki a jikina amma na bar ganin ki”

“Dama ba za ka iya ganina ba saboda ni ruhi ce” na basa amsa ina mai kai wa lips ɗinsa sumba,kan bed muka zube da dukkan alamu shi ma yayi kewata na san halin Uncle sosai muddin yana gida to kowanne dare sai mun kyautata shimfiɗar aurenmu.Cikin shauƙi da bege muka raya daren,ina dab da yi masa bayanin abin da ke faruwa na ji Sarah ta fizgo ruhina na koma can ƙasan ruwa.Na buɗe ido ina kallonta cike da takaici na ce “ya kuma za ki yi min haka?”

Ita ma rai ɓace ta ce “kafin ki je sai da na faɗa miki da kin je za ki yi masa bayani amma kika fara da wata sumbatarsa,sannan tuni hasken alfijir ya keto inda na ƙara ko minti guda ne za a samu matsala don duniyar ruwa ba irin taku duniyar ba ce nan muna da ƙa'ida” tana gama faɗa ta fice ta bar ni nan.

★Gidan Uncle Salem

Shi ɗin ya yarda da akwai ɓoyayyar duniya wannan yasa bai yi mamakin ziyarar da Nafisa ta kawo masa ba.Sosai ya ji daɗin kasancewa da ita don babu wani banbanci tsakanin mu'amalar ruhi da kuma ta gangar jiki, washegari cike da walwala ya fito kusan kowa ya ga canjin amma ba wanda ya san dalili hatta kuwa Deborah wacce take jin kwaɗayinta a kansa ya ƙaru.

Yau girki na musamman ta yi wa ƴan gidan wanda ko kaɗan ba ta wani shan wahalar kunna gas,cikin iya tsafinta take yin komai.Da dare bayan ta faki idon mutane haka ta haura sama,ɗakin Nafisa ta je ta buɗe drowerta ta ɗauko kayanta sai ta shiga toilet ta tsoma kayan cikin ruwa.Da wannan ruwan ta yi amfani ta yi wanka,nan take jikinta ya fara rikiɗa ya koma irin na Nafisa.Cike da makirci ta shirya cikin wasu fitinanun kayan bacci ta fesa turare sannan ta nufi ɗakin Uncle Salem ta je haye bed ɗinsa,shi kuwa bawan Allah yana toilet yana wanka sai tunanin moments ɗinsu na jiya yake.

Yana fitowa yau ma da ƙamshinta ya fara cin karo irin na jiya,ya washe baki yana kallonta jikinsa har rawa yake ya haura gadon yana mai cewa “Naf?”

Ita kuwa FATALWAR DEBORAH wacce ke ɗauke da siffar Nafisa cike da zaƙuwa ta rungumo Uncle Salem.Daidai nan free page ya ida mai son ci gaba 500 ne via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822

*NB:* lokacin posting sai bayan shan ruwa in sha Allah.
[28/02 10:12] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}
Chapter 6 · 0% Book details