Sashe 19
Fatalwar Deborah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka muka zauna jungum har muka yi sallah isha'i,tsaf na shirya cikin kayan baccina na kwanta.Matar nan ta zo kusan kaina tana shafar gashina kafin ta ce “Naf?” wani irin tsammm na ji a jikina,ban amsa mata ba kuma ban juya na kalle ta ba kawai ta ci gaba da cewa “ke ba ki sha'awar jin labarin ainihin garin nan na Ƙwargwam?”
Kamar mai tsoron yin magana na ce “ina so” ban rufe baki ba ta cire matashin kaina sai ta maye min gurbinsa da cinyarta.
A nan take na ji wata nutsuwa ta shige ni cike da ƙaguwa na ce “Mama ki fara bani labarin mana”
Inna A'i ta ce “ta bamu dai don ni ma tun ɗazu na ƙagu na ji”
Wacce na kira da Mama ta yi murmushi kafin ta soma cewa “a wasu shekarun baya, lokacin ina da shekara ashirin ba ɗaya an yi wani zamani mai ban tsoro da tarwatsa ruhi.Duk dare na Allah haka za ka dinga jin ihuce-ihuce daga gidaje daban-daban wanda tsautsayi ya ja shi ya fita don kai agaji to ba zai sake dawowa ba ko gangar jikinsa ba za a gani ba.Duk wannan badaƙalar da ake yi babu wanda ya san taƙamaimai mene ne ke faruwa,sai sannu a hankali duk kowa ya fahimci akwai wanzuwar fatalwa a cikin garin namu.Manyan abin harinta su ne maza da ƙananan yara sai kuma ƴan mata,haka ta dinga yi wa garinmu ɗauki ɗaiɗaya har ya kai zawarawa sun fi yawa sannan ƴan mata sun yi ƙaranci.A daidai wannan gaɓar ne iyayena suka yanke shawarar haɗa ni da wani malami na garinmu,duk da ban sonsa haka na yarda na aure shi domin tsira da rayuwata.A ranar da aka kai ni gidana a wannan rana ce kuma wannan fatalwa ta kai hari a gidanmu,cikin ikon Allah na amsa sunan matar aure a wannan daren na zama cikakkiyar mace.Yadda ake buga ƙofar gidanmu haɗi da wani kuka ana cewa “malam taimako ! Taimako aljanu sun taso wa ƴata” shi yasa malam ya zura jallabiya ya fita don dama aikinsa ne yin ruƙiya....” sai ta yi shuru,da sauri na ɗaga kai na dube ta sai na ga idonta sun yi ja jawur ga ƙwalla na haɗuwa a cikinsu.
Gabana ya faɗi ,murya na ɗan rawa na ce “kar dai ace shi ma fatalwar ce ta tafi da shi?”
Ta jinjina min kai kafin ta ce “tun da ya tafi bai dawo ba,a ranar na yi kuka kamar raina zai fita.Tun ina lissafin kwanaki har na koma yin na wata ,a ƙarshe na tattare na koma gida.Sannu a hankali cikina ya soma girma har ya shiga watan haihuwa,to a lokacin ne fa na fara yin mafarki mai maimaici tun ina ɗaukar abin wasa har na fara jin tsoro na sanar da iyayena nan suka shaida min cewa ana son na sadaukar da yarona domin farin cikin al'umma.A lokacin ban gane abin da ake faɗa ba sai ranar da na haihu na ga Ummana na gyara jariri ta saka shi cikin wani ɗan basket,ta dube ni ta ce “Rumana ki sadaukar domin al'umma ta rayu cikin aminci,kar ki yi jayayya da abin da magabatanmu suka zartar kawai abin da nake so ki yi haƙuri ki daure wata rana yaronki zai dawo miki” sam sai na ƙi fahimtar Umma na karɓe yarona na rungume,a cikin wannan daren kuma muka ƙara samun ziyarar fatalwa .Abun sam bai yi min daɗi ba,a gaban idona ta kashe dukkan iyayena ta tsotse jininsu ta bar su nan.A washegari mutane suka cika gidanmu,sai aka fara zagina ana cewa ni na kashe su kan in ce wani abu aka fara jifana da duwatsu.Dole dangin naƙi tasa na bar gidan,hanyar daji mai tsarki na nufa wanda zamanin Kakani da iyaye suke kiransa da wuri mai tsarki da ruhika masu kyau.Ina ratsa tsakiyar dajin na soma jin wani yanayi na daban a jikina,sai na soma waige-waige can na hango lilo na yara wanda ake kwantar da su haka na je na ajiye jaririna da ko suna ba a saka masa ba.Ina gama ɗora shi sai wani haske mai ƙarfi ya rufe shi har ban iya ganinsa, wata murya ta ratsa dodon kunnena tana cewa “barka da zuwa uwar Sadauki,ababen alƙawari da tsarkakun ruhika na alfahari da ke a bisa wannan sadaukarwa.Ki juya ki koma gida cikin aminci,daga yau kina kan kariyarmu ” ana gama faɗa min haka na juya cike da kewar ɗana,ga mamakina ko da na koma can cikin gari sai na ga ana bani wani girma na musamman.Tare da ni aka yi hidimar yi wa gawar iyayena sutura,bayan nan kuma na zauna ni da sauran dangi muna karɓar gaisuwa” sai kuma ta sake yin shuru.
Na dubi ɓangaren da Inna A'i take sai na ga duk ta takure wuri guda tana kyarmar tsoro,na tuntsire da dariya kafin na dubi matar na ce “ to amma Mama ya zancen fatalwa?”
“Tun daga wannan lokaci ba ta sake saukowa doron duniyar bil'adama ba,sai dai ta gurɓata mana gari wanda ya koma na matsafa” ta bani amsa.
“Ya ake gane matsafi?” na tambaye ta,ba ta bani amsa ba sai ido da ta tsura min har sai da na tsargu na ce “ Mama ya kike kallona haka sai ka ce ni ma dai MATSAFIYA(MRS SADAUKI) ce”
“Wane ne matsafi Naf?” ta jefo min tambayar.
Kai tsaye na ce “mai shan jini”
Sai ta girgiza kai ta ce “a'a ba ita ce amsar ba,a duniyar Ruhaniya sun fassara matsafi cewa duk wanda zai iya juya wani matakin iko ko kuma ya iya karantar tunanin wani to matsafi ne.Sai dai matsafan sun rabu kashi biyu,tsarkaku da kuma masu mugunta.Misali ni da ke ai kin ga aikinmu shi ne ceto al'umma,yayin da kuma tsohuwa mai kifi take muguwa”
“Ni da ke kuma? A'a ni ba matsafiya ba ce,Mama faɗa min ita tsohuwa mai kifi matsafiya ce ko mayya?” na tambaya sai dai ko kafin ta bani amsa Inna A'i ta fasa wani uban ihu tana cewa “wayyo idona”
Da wani mugun sauri duk muka miƙe tsaye,Mama ta ce “dama ai zuwanki nake jira shi yasa ban tafi gida ba.Ki bayyana kanki kafin na binciko ki ”
Na dube ta na ce “Mama ke da wa kike magana?” dariyar da aka ƙyalƙyace da ita ne yasa na samu amsata,na waro ido duk da ina son labarai da kuma horror film amma ai ban taɓa ganinsu a zahiri ba wannan yasa tsoro ya kama ni ashe hakan kuma shine babban kuskurena.Saboda ina firgita duk tsikar jikina ta tashi wannan kuma ya bayyana ɓoyayyar siffata wacce ban san da ita ba sai gani na yi akaifuna na ƙara yin tsayi suna yin tsini daidai nan kuma tsohuwa mai kifi ta bayyana a gare mu.Sai na rasa da wacce matsalar zan ji,dukkan jikina rawa yake.
“Hahaha! Ƙaramar matsafiya har ke ce za ki wani je tare ma wani faɗa?” tsohuwar ta faɗa tana kallona kafin ta mayar da dubanta ga Mama ta ce “ oh! Uwar Sadauki ko kashe ni za ki yi irin wannan hassala?” jin furucinta yasa na juya na dubi ɓangaren Mama,wani uban ihu na fasa tare da rugawa can kusurwar ɗaki ganin Mama ta juyar da idonta sun koma farare tasss kamar madara.
Nan dambe ta kancame a tsakaninsu har suka iso inda nake , tsohuwa mai kifi ta kama ƙafata ta gantsara min cizo ban san lokacin da na fasa wani mahaukacin ihu ba.Cike da jin haushi na caka mata yatsuna gefen wuyanta,zoben hannuna sai ya soma fitar da wani haske kafin can tsohuwa mai kifi ta ɓace ɓat.
Hannuna ya dawo normal sai dai inda ta cije ni ya fasa,da sauri Mama ta nufo ni tare da cire kallabinta ta ɗaure min ƙafar.
Ƴar ƙaramar jaka ta buɗe ta fata ta fiddo wasu abubuwa waɗanda na sha ganinsu wurin Uncle Salem.Hawaye na soma saboda ban son shan maganin nan,ina ji ina gani ta sa wata ƴar ƙaramar wuƙa ta tsaga ƙafata na ƙwalla wani uban ihu ina kiran sunan Uncle haka ta saka min magani kafin ta naɗe min ƙafar,sai ta bani maganin nan da ke kashe min jiki yana jefa ni duniya biyu mabanbanta.Baccin na gama ɗaukata kuma na tsinci ruhina a ɗakin darasi na matsafa,ina shiga sai na ji lamba ɗaya na cewa “ƴar rainin hankali sai yanzu kika damar zuwa?” ban kula shi ba na je na zauna kan kujerata na maida hankali kan darasin da Grand Maa ke yi.Yau kuma zane ta yi a jikin allo na wasu halittu maras kyawun gani kafin ta ce “a yau zan nuna muku yadda ake mayar da abin da ba yiyu ba a zai tabbata,sai dai ku sani hakan a iya ɓoyayyar duniyarmu da kuma masu irin ido uku kawai za su iya ganin abubuwan nan.Ba komai ne wannan abin ba sai fitar da abin da ka zana da hannunki izuwa wannan duniyar,wato ka mayar da zane gaskiya ta hanyar saka masa RUHIN ALJAN(MRS SADAUKI) bari na nuna muku kan wannan zanen” ta faɗa tare da taɓa wani zanen maciji tana faɗar formula na tsafi,sannu a hankali kuwa macijin ya soma yin motsi kafin kuma ƙyaftawar ido ya sauko ƙasa yana buɗe baki .Grand Maa ta ɗauke shi da hannu tana dariya kafin ta ce“kun gani babu wuya ko? Principal raba musu takarda da biro kowane daga cikinku ya zana abin da yake so” haka a raba mana takardu kowa ya shiga zanen abin da yake so,ni sai na rasa ma me zan zana can kuma na soma yin zanen ina murmushi ba tare da ni kaina na san mene ne zan zana ba a haka har na kammala.
Wasu takardun aka sake raba mana masu ɗauke da harafofin tsafi,Grand Maa ta ce su ne za mu karanta domin kawo abin da muka zana izuwa duniya.Bakina na soma motsawa ina kafen zanen da ido kamar yadda ta koya mana,kamar almara kuwa haka na ga ya soma yin motsi sai dai fa ya ƙi yin sauri kamar na kowa tun da tuni suka fara yin shewa suna jin daɗi wasu har sun fara yi min dariya.