Sashe 18
Fatalwar Deborah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na ce “kuma jiya da na yi kiran sunan ɗalibai ka ji naka?”
“Eh Madam ” ya bani amsa.
Ban ƙara cewa komai ba sai na fita zuwa ofis ɗin Grand Maa kamar yadda aka ce in wata matsala ta samu can za mu je.Tun daga bakin ƙofa na ji jinin jikina ya daskare yayin da kuma numfashina ya canza salon tafiya,dakyar na danna belt na neman izini ta bani izinin shigowa.
Ina buɗe ƙofa na ci karo da lamba ɗaya ɗan headmaster shi kuma zai fita,yayi min wani mugun kallo kafin ya fice ni kuma na ƙarasa na gaishe da Grand Maa.Ciki-ciki ta amsa kafin ta ce “ me kika zo yi kuma?” tambayarta ta ce ta yi min wani iri amma na watsar da ita kafin na ce “ an manta ba a rubuta sunan ɗaya daga cikin ɗalibaina ba bisa liste ” sai na faɗi cikakken sunansa .
Wani irin kallo Grand Maa ta yi min na kar ki raina min hankali kafin ta ce “ ai ba mantawa aka yi ba,ki duba liste ɗin da kyau” yanzu ma furucinta sai ya yi min wani iri,amma sai na yi kamar yadda ta ce ɗin na nutsu da kyau na duba liste ɗin sai na ga liste ɗin ta fara da lissafin lamba biyu,sannan a can sama ga sawun rubutu nan mai ɗauke da lamba ɗaya sai dai sam ya goge ba ka ma ganin abin da aka rubuta.
“Me haka ke nufi?” na tambaye ta ina mai ɗaga kai ina kallon ta .
“Kin ga Malama fitar min daga ofis ki bar yin kamar ba ki san komai ba,ni ba za a yi comedy da ni ba” ta faɗa cikin ɗaga murya tare da nuna min ƙofar fita,ganin yadda tuwon fuskarta ya kumbura har yana motsi ga idonta da suka rikiɗe suka zama kamar na Zombie yasa da sauri har ina tuntuɓe na baro ofis ɗin.
Ina shiga aji sai na ɗauki biro na rubuta sunan yaron daga sama,sai na soma yi masu darasi har lokacin shan iska yayi.Kamar yadda aka sanar da mu cewa iya ranar Monday kawai a ba za mu fitar da yara aji ba a nan za su ci abincin da makaranta ta dafa musu,to yau suna da damar fita wannan yasa na ce su je su sayi abin da suke so amma da zarar sun ji ƙarar rawa su dawo.
Kowa ya fita daga aji amma banda Firdausi,na dube ta tare da cewa “ke me yasa ba za ki fita ba?”
“Babana ya ce bai da kuɗi” ta bani amsa.Abincina na buɗe muka ci tare bayan mun gama na bata chocolat tare da cewa “kullum zan dinga kawo mana abinci mu ci kin ji ko?” kai ta gyaɗa min alamun to.Haka ta yi ta mini surutu har lokacin dawowar ɗalibai yayi.
Bayan sun shigo waƙa na soma koya musu sai na ga sun fi mayar ma da hankali a kanta,yadda duk suka shiga nishaɗi sai abun yayi min daɗi.
Lokacin tashi ya gabato sai na yi zaune tare da fiddo liste ɗin sunaye,abun mamaki sunan Abdul da ni ce na rubuta shi ya goge babu shi.Shuru na yi ina sauraren bugun zuciyata da yake wani harbawa fiye da ƙa'ida,dakyar na aro jarumtar sake rubuta sunan nasa sai kuma na soma kira ɗaya bayan ɗaya har na gama duk sai aka zo fara ɗaukarsu har kowa ya watse.
Ina fitowa muka yi kiciɓis da Adama na ce “madam Adama Barka da warhaka fatan kina lafiya?”
“Bayan kin kusa kashe ni shine kike tambayar ina lafiya ? To nan sani ba” ta bani amsa tare da yin gaba fuuu.Na yi tsaye cak ina kallon ta kafin dakyar na ɗaga ƙafata na wuce zuwa gida,sai na tarar da Jabeeru direba muka gaisa a mutumce nan Inna A'i ce ke faɗa min Ammy ta aiko shi ya kawo mana abubuwan buƙata har ƙatuwar frigine wacce aka cika da kaji zuƙu-zuƙu.
Bayan ya tafi ne na shiga na yi wanka na fito,ina zaunawa Inna A'i ta miƙo min kofi cike da madara tana cewa “ungo ki shanye ƴar autata ” ganin yadda ta yi min abin cike da soyayya yasa na karɓa na sha ba tare da na tambayi na mene ne ba.
Sosai na yi ƙoƙari wurin watsar da duk abin da ya faru da ni a makaranta muka sha hira da Inna A'i kafin ta kawo min naman kaza wanda ta yi wa wani romo na musamman dama tun da na dawo ban ci komai ba sai na zauna na soma ci sai na ji tamkar ɗanɗanon magani amma ban yi magana ba na ci na ƙoshi.
Inna A'i ta ce “zan fita na je kasuwa akwai abubuwan da zan sayo ”
Na ce “kin san kasuwar ne?”
“Taxi zan shiga,ba zan jima zan dawo”
“To a dawo lafiya” na faɗa nan ta fice ni kuma saboda kaɗaici yasa na jawo wayata sai dai sam babu network a dole na ajiye ta na ɗauki littafin MUTUWARE ,tun a page ɗin farko na soma jin kaina na juyawa yayin da nake ganin kamar abin da ya faru ya taɓa faruwa da ni,da na tsananta tunani ne kawai idona suka hasko min abin da ya faru da ɗalibina Abdul a daren jiya.Na dafe saitin goshina da ya soma tsira min,ba tare da na shirya ba na kwanta baccin dole wanda ban yi niyya ba.
Cikin wata kasuwa na tsinci kaina,sai tafiya nake ina waige-waige kamar mai neman wani abu.Yayin da hankulan ƴan cikin kasuwan duk ya dawo kaina kamar sun ga sabuwar halitta,har tambayar kaina nake mene ne suke kallo a jikina.Ban ɗauki dogon lokaci ba kuma na samo amsar,wato dogayen fuka-fuka ne a bayana sai motsa kansu suke.Ban kuma ɗauki lokaci ba na tashi sama ina baza idona ta ko ina ,can na hango Inna A'i tana ta sauri yayin da wata matsafiya ke take mata baya tana naɗe inuwar Inna A'i tamkar wata tabarma.Shuuu na dira a tsakiya cak matsafiyar ta tsaya tana kallona,“bani abin da ke hannunki ” na faɗa saboda kusan rabin kurwar Inna A'i na hannunta.
Da sauri ta saka abin cikin kwagiri (wata jaka ce da tsofi ke ɗaurawa a ƙugu don zuba kuɗi)
Ihun Inna A'i yasa da sauri na juya ta ɓangarenta,sai na ga ta faɗi na je da guduna ina kiran sunanta na tallabo ta.Ko da na waiga sai na ga babu matsafiyar babu alamunta,daidai nan na tashi daga baccin saboda kakarin mutuwa da na ji ana yi kusa da ni.
Na buɗe idona a hankali da suka yi min nauyi,sai na ga Inna A'i ce kwance tana kakarin mutuwa jini na fita ta hancinta.Hankali tashe na ce “me ke damunki Innarmu?”
Numfashinta kamar zai fita take min jawabi “a kasuwa ne wata mata ta bani ƙananun kifi na ci shine kawai na soma jin jiri,jikina kuma kamar ana cire min wani abu”
Fatarta na kalla na ga ta yi wani mugun ja ga wasu sawun halittu tamkar dai kifin.Tsam na miƙe tare da saka takalmi,idona har wani rufe wa suke saboda ɓacin rai,ni kaina ban san wa nuna min kasuwar ba haka dai na samu kaina da tunkarar wata hanya har na isa.Allon sanarwar na duba inda aka rubuta ƘWARGWAM MARKET wato kasuwar matsafa,ƙafata na ɗora da niyyar shiga sai dai tamkar akwai wani abu da ke jana a baya wanda ya hana ni shiga ciki.Na gwada hakan ya fi shuren masaki amma na kasa,a ƙarshe ma dai sai zube wa na yi ƙasa a gajiye numfashina na shirin tsinkewa.
Nan na kawo ƙarshen free page duk mai son ci gaba zai biya 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank
Sai ya turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
NB: Yanzu nake rubuta shi ,so don Allah kar ki zo kina ce min ke complet kike so Ni kaina banda shi.
In kuma ya kammala 1k ne kuɗinsa.
30 Janairu 2025
[28/02 10:12] MRS SADAUKI: My book is only 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank
DM +22795045822.
__________________________________________________
*PAID PAGE*
11
Daga inda nake yashe a ƙasa fitilun idona ke dallo min abubuwan ban mamaki,komai da ke wakana cikin kasuwar Matsafa .Dariya suke yi min suna zagina da sunan kasashiya,ban san ta ya aka yi ba har nake jin sautikan muryoyinsu alhalin akwai tazara sosai mai mugun yawa tsakanin inda nake kwancen da kuma ƙofar kasuwar.
Fatun idona na soma lumshewa don dole,ina jin kaina na mugun sara min daga nan ban sake sanin abin da ya faru ba sai tashi na yi na tsinci kaina a gida.
Da ɗan mamaki nake kallon ɗakinmu,har zan yi magana sai na ji dariyar Inna A'i ita da wata mata.Da sauri na miƙe na je na yi tsaye bakin ƙofar kitchen ɗin na tsura mata ido,ta saki murmushi kafin ta ce “kin tashi?”
“Innarmu wannan ɗin wace ce?” na tambayi Inna A'i,ta bani amsa da “wata ƙawata ce ,kin ga je ki yi sallah kafin nake gama girkinki ”
Ban ce komai ɗin ba na je na yi alwala na yi sallah,ina tsaka da yin lazumi su suka fito suka yi zaune kan tabarma.
Ido na tsura mata ina don karantar wani abu sai ga shi kuwa na lalubo amsa ita ce matar da ta cece ni ta ɗauko ni daga kasuwa ta kawo ni nan,a cikin idonta na ga lokacin da ta buɗe gorar ruwa ta ɗura min su na sha sannan na ga hatta Inna A'i ita ce ta ceto ta daga mawuyacin halin da na bar ta.
Yadda ta lumshe idonta ya katse min hanzari daga kutsen da na yi cikin tunaninta ba tare da ni kaina na san abin da na yi ɗin ba.
“Mamar Sadauki na ce sai yaushe za ki bani labarinki?” Inna A'i ta faɗa .
“Ki bari har zuwa dare in za mu kwanta” ta bada amsa tana mai buɗe ido,suka sauka cikin nawa da suke ɗauke da mamakin jin wai a nan za ta kwana.
Na yi tunanin Inna A'i za ta yi ƙorafi akan haka amma sai na saɓani ,murna ma take da hakan.