← Book details Fatalwar Deborah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 20

Sashe 7

Fatalwar Deborah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.

*FCWA*☀️

________________________

01

Ra'ayi riga in ji ƴan magana, wannan haka yake a lokacin da matasa sa'anina ke sha'awar fita waje domin yin dogon karatu tare da burace-buracen ababen ƙyalƙyalin duniya ni kuma shiga ƙauyuka ne ra'ayina domin koyar da yaran da ke cikin duhun jahilci.Sunana Nafisa,matashiyar budurwa ƴar kimanin shekara ashirin da biyu a duniya.Na fito gidan sarauta,a jinin masu izza da taƙamar dukiya sai dai ni sam ba wannan ne a gabana ba.Duk da na sha wahalar shawo kan mahaifina kan ya bar ni na yi karatun zama malamar makaranta amma kuma fafur ya hana ni fita aiki wanda hakan ba ƙaramar barazana ba ce da cikar burin nawa.

Fuska shaɓe-shaɓe da hawaye na nufi ɗakinsa,shine kaɗai tilo da na san zai iya yin magana mahaifina yayi amanna da ita ba tare da gardama ba.Ko sallama ban yi ba ballantana neman izini kawai na tura ƙofar,kamar kullum yana zaune kan dadduma yana jan casbi.A gabansa na zube kamar raƙumar da ke jin ƙishi,ya ɗago fararen idonsa ya zube su a kaina kafin cikin tattausan furuci ya ce “Naf !”
Baki na turo gaba idona na sake zubo da wasu sabbin hawayen.
“ Yau kuma wa ya taɓa ki?” ya tambaye ni cikin nutsuwarsa wacce ke ƙara masa ƙwarjini.

Cikin kuka na ce “Daddy ne wai ba zan yi aikin gwamnati ba”

Yayi murmushin da ya bayyana fararen haƙoransa waɗanda kullum suke shan gugar asuwaki kafin ya ce “ki je zan yi masa magana” da sauri na girgiza masa kai na ce “ a'a Please uncle ka tashi mu tafi yanzu kafin masu hura wuta su ƙara masa ƙaimi” na faɗi haka ne saboda ahalin gidanmu suna da ɗagawa sosai ta yadda suke ganin kamar ƙasƙanci ne a ce jinin gidan ya je yana aikin gwamnati,aikin ma koyarwa.

Ya buɗe baki zai yi magana na yi saurin kamo tafin hannunsa wanda yake lutuf da tsoka sai taushi kamar na mace,hannun nasa ya duba da sauri na sake shi saboda ba tun yau ba ya yi min hani da hakan ba wai iya gare shi ba kawai a'a hatta ƙannaina maza ya hana ni raɓar su ko kuma taɓawa a tsakaninmu.

Na sunne kai wasu hawayen na sake surnano min suna ɗiga kan farin hijabina.
“Nafisatu?” ya kira ni cikin wani salo,ba tare da na ɗago ba na ce “ na'am uncle”
“Me yasa ra'ayinki ya banbanta da sauran danginki? Me yasa kike son yin aiki alhalin mahaifanki sun tanadar miki komai na rayuwa?”

Na ɗago na dube shi kafin na ce “ uncle kai ma ba ka son na yi wannan aikin jahadin na shiga ƙauyuka ina wayar da kan al'umma? Saboda me uncle? Kawai don iyayena suna masu arziki shi kenan sai na yi kwance na dogara da dukiyarsu? Me yasa ni ba zan yi aiki ba?”

“ Saboda ke mace ce!” ya bani amsa yana kallon idona,ji na yi kamar ya watsa min ruwa zafi kawai sai na tashi na fita a guje ina gwanjin kuka.Ina shiga babban falonmu duk sai na tarar da ƴan uwana kuwa suna ta cece-kuce akan maganar,ɗakina na wuce direct na haye gado na kwanta rub da ciki amma abin mamaki sai na ji tamkar kan cinyar mutum ne kaina yake amma sam ban bai wa hakan muhimmancin ba na ci gaba da rera kukana,har na fi jin haushin rashin goyon bayan Uncle Salem kan na Daddyna.A hankali na soma jin ana shafar gashin kaina wanda ke luluɓe da hijabina,ido na soma lumshewa ba tare da na shirya ba yayin da kuma na soma sauke numfashi akai-akai.Ban sani ba ko na shiga duniyar mafarki ne ko kuwa zahiri ne amma sai na tsinci muryar wata dattijuwa na yi min gatana haɗi da bani tarihin ababen tsoro kamar yadda na fi ƙaunar kallon horror film.

★A can ɓangaren Uncle Salem kuwa Nafisa na fita da gudu yayi saurin tattare littafansa kafin ya gyara zaman hiramin kansa ya fito.Direct ƙofar da za ta sada ka da babban falon ya nufa bakinsa ɗauke da sallama,tsit duk falon ya ɗauka kafin duk su yi ƙasa da idanunsu saboda yadda yake da matuƙar muhimmancin da kuma girma a idonsu.Cike da girmamawa suka soma gaishe shi “ Barka da fitowa Daddy ƙarami“ domin haka suke kiransa in ka fidda Nafisa da take ce masa Uncle ita ma ɗin shine da kansa ya koyar mata da hakan.

“Fatan dai ba ƙara ta ba aka kai wurinka,a toh don na san ba kasafai za a gan ka a nan ba” cewar Daddy yana ɗan murmushi yana kallon babban abokinsa,amininsa kuma ɗan uwansa.Uncle Salem ya ce “tun da ma ka sani ai shi kenan sai a fara shirya mata abubuwan da za ta buƙata in ta je can”

Daddy ya ɗan nisa yana kallon yaran wurin duk sai suka tashi suka kama gabansu,sai a lokacin kuma Uncle Salem ya zauna suna fuskantar juna.

Duk shuru suka yi na wani ɗan lokaci kafin Daddy ya ce “ ba wai yadda kake tunani ba ne aboki,ina da dalili na daban da yasa ban so Nafisa ta yi nisa da gida”
Uncle Salem ya murmusa ya ce “tun muna makaranta ake faɗar wannan kalmar akan kana da dalilin ƙin yin wani abu amma har yanzu ba ka taɓa faɗa min mene ne dalilin ba.Abdul Hameed ka sani cewa su yara da kake gani sun fi son bin zaɓinsu kan na iyayensu,kuma kai ma in ba ka manta ba...” sai kuma yayi shuru.
Yanayin fuskar Daddy ta ɗan sauya kafin ya ce “babu damuwa zan bari ta je ɗin, Allah ya bada sa'a ya kuma tsare ta akan abin da nake tsoron faruwar” da “amen“ kawai Uncle Salem ya amsa kafin ya miƙe tsammm ya nufi ɗakin Nafisa,ya tura ƙofa tare da yin sallama sai kuma yayi tsaye cak yana buɗe ƙofofin hancinsa saboda kalar wani ƙamshi da ya dake shi da bai taɓa jin irinsa a wannan duniyar ba....
[28/02 10:12] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.

*FCWA*☀️

________________________

02

Tsaye yayi yana kallon yadda take bacci tana wani taɓe baki kamar mai kuka yayin da goshinta ke fitar da gumi.Ya furzar da wani huci kafin ya ƙarasa ya zauna bakin bed ɗin,a hankali ya cire mata hijabin nata wanda ya ɗan jiƙe saboda zufa.Sumar kanta wacce take baƙar ƙirin ya soma shafawa yana tofe ta da addu'a,a hankali ta soma sauke ajiyar zuciya tana wani motsa idonta kamar mai son buɗe su.

Kamar wanda ke wasa da maciji haka ya soma shafa farar fatar fuskarta wacce ta yi ɗan ja saboda kukan da ta yi.Wata irin azababiyar ƙaunarta ce yake jin tana bijiro masa,ji yake tamkar ya ɗauke ta ya haɗiye tsabar so.

Sam bai san abokin nasa ya shigo ba don ya lula sosai a duniyar tunanin muradun ruhinsa,sai jin saukar muryarsa yayi “ sai yaushe ne za ka sanar da ita ɓoyayyen sirrin da ka binne abinka?”

Uncle Salem yayi saurin ɗagowa ya dubi Daddy ya saki ɗan murmushin da ya zame masa jiki kafin ya ce “ har yanzu Naf yarinya ce aboki,zan ƙara mata lokaci ” sai kuma ya mayar da duban nasa ga fuskarta a iya kallon da yake jifar ta da shi ya isa ya fallasa ma sirrin da ƙunshe a zuciyarsa.

“ Shekarunta ashirin har da biyu fa,lokaci na ƙurewa girma na sake zuwar ma amma har yanzu ba ka ajiye iyali ba aboki” Daddy ya faɗa cikin rashin jin daɗi.

“ Shi aure ai ba sauri yake so ba,a'a fahimtar juna aboki.Ka yi tunanin yadda Naf za ta ɗauki lamarin ne in ta ji cewa ni mijinta ne alhalin a uba ta ɗauke ni?”

Daddy yayi murmushi kafin ya ce “ to ai kun fi kusa,ban iya na sani”

Uncle Salem na shirin yin magana aka shigo haɗi da sallama,Ammy ce hannunta riƙe da kofin ruwa.A mutumce ta gaishe da Uncle Salem wanda a girme ya girme mata sannan ta dubi mijinta hasken idaniyarta ta ce “ ga maganinta yau ba ta sha ba sam” ya karɓa ita kuma sai ta fita.

Kan dakalin gado Daddy ya ajiye maganin yana mai kallon Nafisar wacce har zuwa yanzu take baccinta yayin da kuma hannun Uncle ɗinta ke kan sumarta.

“ Aboki me kake ɓoye min dangane da Naf?” yayi tambayar cike da kulawa.
A ɗan rikice Daddy ya ce “ no babu komai zan je na duba wasu takardu in ta tashi ka bata maganin” yana gama faɗa ya fice,shi kuwa Uncle Salem kai ya girgiza tun suna yara suke tare amma har izuwa yanzu bai san dalilin da yasa abokin nasa ke ɓoye masa wani babban sirri da ke ɗawainiya da rayuwarsa.Tun da Nafisa ta soma tasowa yake lura da yadda hankalinsa kocokwam ke kanta hatta makaranta in ta je ya dinga kiran waya kenan yana tambayar labarinta,yana ɗaya daga cikin abin da yasa kuma ya basa aurenta tun ba ta san kanta ba amma har yau ya ƙi sanar da shi mene ne sirrin.

Ganin kamar baccin nata irin wancan ne da ta saba yi ,sai Uncle Salem ya ɗauki kofin maganin ya cika bakinsa da shi kafin ya taɓe bakinta yana ɗura mata shi kamar yadda tantabaru ke ciyar da junansu,a hankali kuma take haɗiye ruwan maganin da shi ne ya haɗa mata shi a haka har ta shanye shi tasss.Da ya kai ƙarshe sai da ya ɗan lashe mata lips kafin ya miƙe ya fita,sashensa ya nufa ya rage kayan jikinsa yayi wanka ya fito ya shafa turare kawai sai ya ɗauki system ɗinsa ya soma aiki yana duba saƙonnin sojawan da shine ya tura su mission a daji.Reppot ne iri-iri wasu na murna wasu na jimame,tuni kansa ya soma yin hayaƙi yana jin cewa da buƙatar ya je can ɗin da bada wata sabuwar atisaye.

★ NAFISA
Chapter 7 · 0% Book details