← Book details Fatalwar Deborah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 20

Sashe 2

Fatalwar Deborah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Jini! Jini! A bani jini na sha! Ina son shan jini! Mamy ki bani jini!” muryar Abidah ta ratsa dodon kunnena ,a hankali kuma na buɗe idona na ware su a kanta,yanayinta kawai na kalla na tabbatar da eh tana da buƙatar shan jinin,kuma jinin iya nawa ne kawai za ta sha.Na lumshe ido ina mai tuna Madam Lee ba zan manta ba ita ce ta farko da na saba gani cikin irin wannan halin.

“Mama ki jiƙa ganyen magani a yi mata wanka,sannan ki haɗa maganin zazzaɓi kar ki manta ki ɗiga ruwan floris ”na ji muryar Uncle Salem cikin ruɗani,sai na ware idona a kansu ina kallon yadda yake ƙoƙarin lalaɓa Abidah amma sam ta ƙi saurarensa sai ma wani juya idonta da ta fara suna canza kala daga fari zuwa ja kamar garwashin wuta.

Jikin Mama har rawa yake ta yi aikin da Uncle Salem ya bata,sai dai tana kawo robar mai cike da ruwan magani Abidah ta canza murya ta soma magana cikin salon gargaɗi “jini na ce ina so shine kuke wani ƙoƙarin haɗa magani? Ku bani jini ko kuma na kashe ku ɗaya bayan ɗaya”

“Abidana ki yi haƙuri ki bari na yi miki wanka sai a baki jinin”Mama ta faɗa tare da kama rigarta,da ƙafa Abidah ta shure Mama ta yi sama tare da faɗuwa can gefe kanta ya bugu ga table nan take jini ya soma zuba, Abidah ta fara yin dariya cikin wata shaƙaƙar miya ta ƙato majiya ƙarfi kafin ta ce “yaushe aka haife ki da har za ki yi min wayo? Ki yi hankali da ni yau kanki na fasa in kika ci gaba da yi min ƙarya nan gaba wuyanki zan karye na cire shi na baiwa tsuntsayena namanki su cinye”

Cikin zafin rai Uncle Salem ya tsumbula Abidah cikin ruwan ba tare da ya cire mata kaya ba,ai kuwa ta shiga tsala ihu tana kirana “Mamy?Mamy?” ban sani ba ku su ma sun fahimci cewa aljanin da ke jikinta ya bar tunaninta a halin yanzu ita ce ke jin azaba ba shi ba.

Da wani irin sauri na diro daga kan kujerar na zo gaban robar,sai dai ko kafin na taɓa ta Daddy ya wani jawo ni baya.Tun Abidah na iya kiran sunana har ruhinta ya galabaita,idonta suka kafe wuri guda sun koma farare tasss kamar na fatalwa,yayin da fatar bakinta ta soma bushewa tamkar itaciyar da ke neman a yi mata ban ruwa ba ta samu ba.

“Daddy ka sake ni na ceci ƴata kafin ta mutu”na faɗa zuciyata na yi min wani nauyi don tuni na yarda kuma na aminta da cewa eh ni ɗin mayya ce,haka ma ƴata sai dai na lashi takobin zan tarwatsa rayuwar duk wani wanda ke da hannu a kawo wannan ƙwayar maitar a cikin ahalinmu.

“Ki bari Abbanta na bata taimakon ne” Daddy ya faɗa .

Na girgiza kai na ce “duk abin da yake yi mata ga banza ne,domin kuwa iya fatar jikinta kawai zai yi wa aiki amma ruhinta jini yake buƙata”

Uncle Salem ya juyo yana yi min wani irin kallo,sam kuma ban damu ba ni dai burina kawai shine na ceto Abidah.Daddy na sakina sai na lalaba cikin gashina na fito da wani tsinke mai tsini kamar allura,a yatsana manuniyar na caka shi nan take jini ya fara tsirta sai na yi saurin kai shi kusan bakin Abidah a hankali jinin ya soma kwarara cikin maƙoshinta yana shiga hanjinta nan take kuma idonta suka fara dawowa daidai haka ma bushewar da bakinta yayi duk ya dawo normal.

Sai da na tabbatar ta sha jinin yadda ya kamata kafin na janye yatsana,a nan take kuma kamar na kashe pampo jinin ya bar zuba.Daga cikin ruwan na tsamo ta na rungume ta gam a ƙirjina,ina jin ƙaunarta na sake huda ɓargon zuciyata tana ƙara samun matsuguni.

Miƙewa na yi da ita a jikina na haura sama,ina jin Mohamed na kuka amma ko waiga wa ban yi ba.Ina shiga ɗakina na cire mata kayan jikinta na yi mata wanka da kaina,sannan na shafa mata mai .Kayanta suna can ɓangaren Mama don a can suke kwana su duka ukun wurin kakarsu,wani kallabina na atamfa na ɗaura mata na kwantar da ita kan bed sannan na shiga toilet na sakar wa kaina shower.Duk abubuwan da suka faru suka soma dawo min ,wani irin ciwo zuciyata ta soma tuna marin da Uncle yayi min na soma yi wa kaina tambayar ‘ya bar sona ne ko me? Duk tsawon shekarun da aka ɗauka kenan ya san ina da wannan cutar amma bai taɓa faɗa min ba,don me sai yau? Saboda kin fara tsufa!’ wani ɓangaren zuciyata ya bani amsa.

Ina nan tsaye na ji an turo ƙofar toilet ɗin an shigo,na san in ba shi ba to babu wanda zai iya yin haka.Amma duk da haka ban juyo ba,sai ji na yi ya rungume ni ta baya tare da yi wa cikina zobe da hannuwansa yana mai ɗora kansa kan kafaɗata,cikin wani sauti marar hayaniya ya furta “ki yi haƙuri babyn Uncle ” ji na yi kamar ya watsa min ruwan zafi,wato ya san abin da yayi min bai kyauta ba?

Da wani irin ƙarfi na ture shi ina mai juyowa muna facing juna,cikin masifa na ce “na ƙi na yi haƙurin! Ba zan yi ba! Ka fita ka bani wuri zan yi wanka”

Ya matso yana shirin kamo hannuna amma na buge shi ina mai cewa “kar ka taɓa ni ! Ka fita ko kuma ni na bar ma toilet ɗin”

A cikin idonsa ina iya hango damuwa,a haka ya fita ni kuma na ɗauki soso da sabulu na soma wanka ina yi ina kuka har na gama.Ko da na fito ban ga Abidah ba,na san kuma shi zai ɗaukar ta ya sauka da ita ƙasa.A gaggauce na shirya tsaf kamar wacce ba ta da damuwar komai na sauko,ina isa falon Abdallah ya zo ya rungume ni yana mai cewa “Mamy ?”
Na ɗan ƙaƙalo murmushi na ce “ka ci abinci ne?” kai ya girgiza,na kama hannunsa ina mai kallon inda Mohamed ke bacci fuskarsa duk ta yi sawun busassun hawaye.Tausayinsa na ji,don na san saboda ni ce duk gidan ya hargitse.Can inda aka ware domin cin abinci na ja Abdallah na zaunar da shi kan kujera na soma basa da hannuna shi kuma yana yi min surutunsa wanda babu laifi na ji nauyin zuciyata ya ɗan rage.A hankali na ɗaga idona saboda yadda nake jin kamar ana ankare da duk wani motsina,Uncle na gani ya harɗe hannuwansa kamar ya samu tv yana kallona...
[26/02 17:28] MRS SADAUKI: *FATALWAR DEBORAH*🐲
MAKARANTAR MATSAFA 2 ☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Ga malaman makaranta

*FCWA*☀️

________________________

Masu jiran book ɗin *MAKARANTAR MATSAFA* to ya kammala za ku iya tura kuɗinku kai tsaye ta wannan account 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank sai ku turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822

04

Da sauri na fidda hannuna daga cikin plate ɗin abincin na miƙe, kitchen na shiga na fara wanke hannuna kenan na ji ƙamshin turarensa ya cika wurin.Na haɗe fuskata tamau kafin na juyo na banka masa wata muguwar harara,shi kuwa murmushi ya sakar min ya buɗe baki da niyya yin magana na bangaje shi na wuce ina jin sawun takunsa alamun ya biyo bayana amma ban juya ba har na soma taka step,muryar Mama na ji tana kiransa “Sadauki zo nan ” a yadda na ji amon muryarta na tabbata ranta a ɓace yake.

Shi kuwa ce mata yayi “ina zuwa Mama ɗan jira ni don Allah ”

Ina shiga ɗakina na fara ƙoƙarin rufe ƙofar da key amma ya wani bangazo ƙofar har sai da na kusa faɗuwa na yi tangal-tangal amma yayi saurin cabko hannuna,bayan na tsayu daram kan ƙafafuna na yi ƙoƙarin fizge hannuna amma ya ƙi sakina sannan na kasa ƙwatar kaina don ba ƙaramin riƙo yayi min ba.

“Naf don Allah wannan duk na mene ne?” yayi tambayar cikin sanyin murya.
Idona ya kawo ruwa,shi kuwa sai ƙoƙarin ɗago haɓata yake sama don na kalle shi amma na ƙiya.“Na ce ki yi haƙuri ko?” ya ƙara faɗa.

Sai a lokacin na ɗaga kaina sama na sauke masa idona masu cike da masifa na ce “na ƙi na haƙura ɗin,ba zan yi ba.Ni za ka tozarta gaban ƴaƴana? Ni ka kira mayya? Na ji gaske ita ce ɗin,amma kai yanzu ba abin kunya ne a gare ka ba ka kira matarka da wannan sunan? Kuma gaban ƴaƴana...” kukan da ya kubce min ne yasa ni yin shuru ban shirya ba.

Ya ce “kar fa ki manta su Abdallah yara ne ba su san abin da kalmar ma take nufi ba,sannan Mama da Inna A'i sam ba za su taɓa tada zancen ba”

Ƙirjinsa na soma duka da dukkan ƙarfina kafin na soma magana cikin ɗaga murya har jijiyoyin wuyana na tashi,“kasancewar tasu yara yasa na fi damuwa,don za su iya fitar da maganar su ce sun ji Abbansu ya cewa Mamynsu Mayya.Kenan me za ka ce in ƴan unguwa suka fara guduna? ”

Ƙara riƙe ni yayi gam na soma zillewa ina son raba jikina da nasa,ya ce “don Allah Naf ki yi haƙuri wallahi na san Abdallah ba zai taɓa faɗar haka ba ballantana Mohamed da ko magana bai iya ba”

“Shi kuma zargina da ka yi ka ce ni na kama ruhin Abidah?”

“Naf ki fahimce ni na faɗi haka ne saboda ke ma farkon ciwon jinnunki haka suka fara nunawa,tun gwajin farko na gane kina ɗauke da kambun maitar aljanu amma na yi ta fafutukar ganin na toshe duk wata ƙofa da za ta iya yin galaba a kanki har ki fara aiki da ita.Ina son ki Naf, wannan dalilin yasa duk wani lokacina na ƙarar da shi wurin kula da ke.Na san na yi kuskure a ɗazu amma ki yi haƙuri ki yafewa Uncle ɗinki”

Kalamansa sosai suka daki zuciyata,amma ba zan sauko da wuri ba na fi son na nuna masa zunubinsa mai girma ne don ko kowa ya kira ni da sunan mayya shi bai kamata furucin ya fito bakinsa ba.
Chapter 2 · 0% Book details