Sashe 10
Fatalwar Deborah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar wacce suka yi wa allurar zaburar wa kuwa haka na wani kwanto jikin A'i mai aiki wacce nake kira da Inna na ce “ ai tare da Innarmu zan tafi ita za ta dinga kula da ni,kafin na dawo ta yi min girki mai daɗi” A'i ta washe baki don sosai take jin daɗin yadda Nafisa ta ɗauke ta tamkar Kakarta sam ba ta nuna cewa ita ke ƙasa gare ta,haka kuma ita ce ta raine ta tun tana cikin tsumman goyo ko aiki za ta yi haka take goye ta in kuma ka ga sun rabu to Uncle Salem ne ke gidan.
“ Ki ma cire wannan a ranki don Inna A'i ba za ta bi ki ba” cewar Ammy tana mai zuba min kunun gyaɗa a kofi.
Na ce “ wai Innarmu ba za ki je ba?”
A'i ta ce “ ke wasa take yi miki fa,tuni ai na haɗa komatsaina na ƙulle a buhu” cike da jin daɗi na ɗauki kofin kunun gyaɗana na fito falo na zauna,tv na kunna na saka horror film ina kallo ina sha sam ban jin tsoron abubuwan da ake nunawa wani sa'in ma ji nake tamkar ƴan uwana ne.
Ƙamshin turarensa ne ya fara yi min maraba kafin shi ya shigo,na ɗaga kai ina kallonsa .Sanye yake cikin kakin soja sun yi bala'in yi masa kyau sai dai ya aske gemunsa da sajensa,da sauri na ajiye kofin hannuna ina turo baki ina kallonsa tuni kuwa ya fahimci dalili don tun ina yarinya nake faɗa masa ina son saje,sannan Inna A'i ta taɓa faɗa min ranar farko da na fara ganin Uncle Salem ya cire sage da gemu haka na yi ta kuka ina ɓata fuska sannan kuma na ƙi yarda da shi .
Da sauri na miƙe zan bar wurin yayi saurin kamo tsintsiyar hannuna yana mai cewa “ oyaaa Naf ɗin Uncle kar ki yi fushi zo ki shanyen kununki ki zo mu je na yi miki shopping ” jin ya ambaci shopping yasa na juyo don na san duk cikin shirye-shiryen tafiyata ne.
Na sake turo baki a karo na biyu kafin na ce “amma shine ka aske ...” yayi wani murmushi mai sauti yana cewa “ zai fito ai,kin ga kar ki yi fushi da Uncle ɗinki” sai ya zaunar da ni tare da ɗaukar kofin ya ci gaba da bani kunun har na shanye kafin ya ce “ je ki canza kaya ki zo mu wuce”
Da murna na koma ɗakina,sai dai ban canza kayan ba kawai dai na zumbulo dogon hijabi har ƙasa.Ina fitowa Uncle Salem ya matso kusa da ni kafin ya ce “ ki canza kaya Naf ” da mamaki na dube shi,ko ta ya aka yi ya gane ban canza ba.
Na marairaice fuska na ce “ Please mu tafi kar dare yayi” ya ɓata rai yana kallon ƙirjina,sai na turo baki na koma ɗaki na je gaban madubi na yi tsaye ashe rabon a yi ne ya kai ni don kuwa ina tsaka da tantance yadda saka hijabin bai ɓoye ainihin shap ɗin jikina ba sai na hango wata farar mata tana saka min abubuwa a jaka,ta yi zaune daram kan gadona.Na waiga da sauri sai na ga wayam,ina maida dubana kan madubi daidai nan ta bi ta window ta fice.Da mugun sauri na je bakin windown sai na gan ta a buɗe alhalin kullum a rufe take ban barinta a buɗe .
“ Naf wai har yanzu ba ki shirya ba?” na ji muryar Uncle Salem a bayana,na juyo da sauri ina cewa “ yanzu zan shirya“ sai kuma na ga yana buɗe ƙofofin hancinsa ya ce “ wannan wai ƙamshin mene ne kamar na Gawa?”
Da ido na tsure shi ina kallo jin ya ambaci gawa,a zuci na ce ‘ kenan dai da gaske ne abin da idona ya gane min? Ko ɗaya daga cikin fatalen da ake cewa sun shigo duniyarmu ne?’
“ Ki yi sauri ina jiran ki a mota” ya faɗa tare da fita.Kayan atamfa na saka kafin na ɗora hijabi sama,sai da na je na shaidawa Ammy kafin na fita can tsakar gida inda yake jirana.Bayan motar na shiga na zauna kusa da shi,waya na tarar yana yi sai da ya bai wa direba umarni sannan ya soma tuƙa mu.
Sai da muka hau titi sosai kafin ya kashe wayar wacce duk rabinta turanci ne da kuma sunayen makaman yaƙi.Na ɗaga kai na dube shi daidai shi ma ya dubo ni,sai muka haɗa ido hannuna ya kamo yana murmushi ban san dalilin da yasa ni ya hana ni na dinga riƙe hannunsa amma shi in ya yi niyya haka yake kamo ni.
“ Faɗa min me da me kike son saya?” ya tambaye ni yana ɗan matsa hannuna,ko kaɗan ban jin wani abu na daban saboda a matsayin uba na ɗauke shi.Na langwaɓar da kai na ce “ Chocolat da kuma teddy babba,sai turare da kuma ƙumbar kanti,da lipstick,da uhmm yawwa da sabuwar waya Uncle Please ” na ƙarashe tare da ciro ƙafafuna na yo sama da su tare da ɗora su kan nasa,ina jin lokacin da ya ja wani numfashi kafin ya ce “zobe fa?” ya tambaye ni saboda yadda ya san ina son zobe sai dai duk in ya siya min ban san ya ake yana ɓata ba.Na saki ɗan murmushi kafin na ce “ na hannunka nake so” sai na soma ƙoƙarin zare wani zobensa mai shegen kyawu da sauri ya dakatar da ni yana mai cewa “ zan saya miki wani dai”
Na turo baki na ce “ Uncle wannan zoben dai kamar a tare aka haife ku ko kuma wani ɗanka sam ba ka son rabuwa da shi,ina ga ma ka fi sonsa fiye da Niii!” na ɗan ja ƙarshen ban shirya ba saboda yadda ya kafe ne da rikatatun idonsa masu matuƙar kaifi .
“ Shi zoben?” ya tambaye ni cikin wata irin murya,ban iya cewa komai ba sai kai da na ɗaga masa alamar eh.A gabana ya cire zoben daga babban yatsansa na tsakiya sai ya kamo hannuna na hagu ya zura min shi a yatsana na biyu,a hankali yayi ta shafar zoben yana kallon tsakiyar idona har ya gama daidaita shi,sam tunanin ta ya aka yi zoben da shi kansa a babban yatsa kawai ya tsaya masa amma ni kuma a yatsa na biyu? Wannan tunanin sam bai shigo kwanyata ba sai na shiga yin murna har da wani rungume shi, Uncle Salem ya ƙara jan ajiyar zuciya a karo na biyu.
Muna isa Mall ɗin ya ja ni izuwa ciki,ana ganinsa da kakin soja duk a soma basa girmansa,ɗaya daga cikin ma'aikatan wurin aka haɗa ni da ita muka je tana nuna min kaya masu kyau sam ban san Uncle yayi tafiyarsa ba sai da muka sauko ƙasa ina ta baza ido amma ban gansa ba.Idona ya ciko da hawaye har zan tambayar mai kula da shiga da fita sai ga shi ya shigo ,ya sakar min murmushi kafin ya ce “ zo ki zaɓi wayar kafin a kira sallah” ya wani kama hannuna zuwa inda aka jera wayoyin manyan masu tsada Iphone na ɗauka sai muka zo nan ya biya kuɗi muka wuce mota yayin da kuma aka kawo min kayana har mota.
Tun a hanya aka soma kiran sallah ga shi wurin da ɗan nisa, Uncle ya ce “ Jabeeru ɗan tsaya mu yi sallah kar jam'i ya wuce mu,dama da alwala ta” wuri direba ya samu ya parker suka fita suka bar ni nan,ina duba sabuwar wayata na ji an ƙwanƙwasa gilashin mota.Da sauri na dubi wurin sai na ga wata tsohuwa mai ƙusumbi a tsaye tana kallona da manyan idonta da suka shige can ciki tsabar tsufa.
Banda ko dala a hannuna tun da ban fito da jaka ba,duk a tunanina almajira ce wannan yasa na buɗe ƙatuwar ledar chocolat da sauran kayan maƙulashe na ɗauko mata cake guda biyu da kuma jus,ina buɗe murfin motar sai ta ɗan matsa gefe na fito .Fuskata ɗauke da murmushi na ce “ ga wannan Kaka banda kuɗi hannuna”
Cike da murna ta karɓa kafin ta ce min “ ki san yadda za ki yi ki hana mijinki tafiya dajin nan rayuwarsa na cikin haɗari tarko ne aka yi masa”
Na yi dariya na ce “Kaka ai ni budurwa ce banda aure”
“Naf shiga mu tafi kin wani fito waje duk ana kallon ki“Uncle ya faɗa tare da buɗe min ƙofa na shiga ina kallon tsohuwar wacce ke tsaye tana yi min murmushi amma abin da ya bani mamaki yadda aka yi sam Uncle bai gaishe ta ba alhalin na san shi da girmama tsofi don shine ya koya min yin sadaka musamman masu rauni irinsu.
Sai bayan na shiga motar ne na lura da ashe tun tuni shi Jabeeru ya zauna kan mazauninsa.Har muka iso gida da tunanin tsohuwar nan danƙare a zuciyata amma sam ban faɗa wa kowa ba sallah kawai na yi na fito na soma buɗe kayan ina nunawa Ammy da kuma ƙannaina biyu Abdul da Mubarak,sai kuma sauran ƴan uwana waɗanda suke cousin ɗina ne.Wayar iphone ɗin dai ce duk suka yi ta taya ni murnar mallakarta don su duk sun jima da yinta in aka cire ƙannaina.Bayan an yi sallar isha'i Daddy da Uncle suka shigo a tare nan ne na ji yana faɗar cewa gobe in Allah ya kai mu Jabeeru direba zai kai mu can ƙauyen Ƙwargwam ni da Inna A'i saboda shi zai wuce can mission.Sam kwata-kwata ban kawo zancen cewa akan Uncle Salem wannan tsohuwar ke magana ba shi yasa kawai ban wani damu ba sai ma rigima da na ɗora masa na cewa to dole da zarar ya sauko ya fara zuwa can inda nake kafin ya zo gida.
A cikin daren ma sai da na yi mafarkin tsohuwar nan ta sake ce min kar na bar mijina ya tafi,amma na share batunta na soma shirin tafiya don tuni tun jiya ka saka komai namu a cikin mota.