← Book details Fatalwar Deborah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 20

Sashe 20

Fatalwar Deborah Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Grand Maa ta ce “lamba uku ki nutsu da kyau ki aje esprit ɗinki wuri guda don aikin na son nutsuwa” ba tare da na ɗago na dube ta ba na jinjina kai tare da ci gaba da yin fafutukar fiddo shi amma ya ƙi,hakan ya hassala ni na ɗaga murya ina karanto harufan “huhannn!” zanen yayi wani irin kuka da yasa na zabura yayin da ajin yayi tsit.

Kowa ido ya buɗe da baki yana kallon abin da ya fito cikin zanen da na yi,yayin da Grand Maa tsabar tsoro ta ƙanƙame principal.
Da sauri na lumshe ido jin Dragon 🐲 ɗin ya soma lasar fuskata yana yin wani kuka kuma,na buɗe idon tare da kai hannuna na soma shafar saman kansa.

Headmaster na gani da sauri yana goge dukkan zanen da aka yi kan allo.Yadda na kafe shi da ido ƙila shi yasa Dragon ɗina kallon wurin,yana ganin sauran zanen da ba a goge ba ya fara yin wani kuka da yasa duk halittun da ƴan uwana suka zana suka soma ɓuya yayin da kuma Ajin ya soma girgiza takardu na tashi sama.

Headmaster jiki na ɓari ya bar jikin allon ganin my dragon ya soma feshin wuta yana ƙona dodannin da ke jiki.Kafin daga ƙarshe ya soma feshin wuta ta ko ina babu shiri duk suka shiga guduwa yayin ni kuma na yi tsalle na haye bayansa kawai sai ya tashi da ni sama yana shawagi.

“Nafisa? Nafisa?” na ji muryar Inna A'i na tashe ni,na buɗe ido dakyar ina kallon ta kafin na ce “lokacin sallah yayi?”

Ta ce “ina fa ! Gobara ce aka yi can cikin makaranta shine headmaster ya ce a tado ki”

Na miƙe ina kallon bakin ƙofa sai na gansa a tsaye sai gumi yake,na ce “to ni da ba namiji ba mene ne kuma abin tada ni kai agajin kashe gobara?”

Wani kallo ya watso min irin yana cike da takaicina ɗin nan,kafin ya haɗiye wasu yawu har sai da na ji ƙarar muƙut .Ya ce “ki zo mana Malama Nafisa duk kowa fa ya fito ke ake jira”

Ina shirin yin magana aka buɗe ƙofar toilet sai na ga Mama ta fito hannunta riƙe da bokitin ruwa,ta miƙa min shi tana cewa “ki dai je ai taimako babu ruwansa da mace” na karɓi bokitin na zura takalmina ko hijabi ban saka ba haka na fita zuwa can inda wutar ke ci ,abun mamaki a wuri guda take sannan duk ƙoƙarin kashe ta da suke ta ƙi raguwa amma ina watsa ruwa ɗaya da bokiti ta soma mutuwa ko minti biyu ba a yi ba kuwa duk komai ya tsaya cak sai biɗiɗin hayaƙi da yake tashi.Da yake ni har yanzu doluwa ce sam ban ga abun almara ne ba koma wanda hankali bai ɗauka,sai ma murna da na yi wutar ta mutu.Na juya zan tafi na ji muryar Grand Maa na cewa “ina za ki je? Kin ɗauka haka za mu bar ki ne ki tafi bayan duk uwar asarar da kika yi mana”
Da mamaki na ɗago ina dubanta,sai kuma na ga dukkan sauran malaman sun zagaye ni kowane yana murmushin mugunta....
Chapter 20 · 0% Book details