← Book details Fatalwar Deborah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 20

Sashe 15

Fatalwar Deborah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shuru yayi bai ce komai ba,ni ma sai na rashin kunyata.Na ɗaga kai da niyyar satar kallonsa sai na ga ashe ni ɗin ce yayi ƙuri kamar mai kallon tv.Zan yi ƙasa da kai yayi saurin tallabo haɓata ya ce “ da gaske kin shirya zaman auren?”
Na lumshe ido ina dariya,ya ce “ faɗa min na ji saboda in na koma gida na yi wa Daddynki magana a soma shirin biki”

Na ɗan cinno baki gaba na ce “ni da ko saurayi banda” kamar daga sama na ji bakinsa kan laɓana, wannan karon dai kam cikin hankalina nake.Cike da razani na buɗe ido kafin da sauri na tashi daga gabansa jikina na ɗan yin rawa,duk da ba yau ne ya saba yi min kiss ba amma a goshi ne ko a kumatu ya saba min sannan an ɗauki lokaci mai tsayi rabon da yayi.

“Nafisa?” na ji muryar Inna A'i,da sauri na nufi kitchen ɗin ina jin daɗin kiran nawa da ta yi.Ina shiga ta yi min wani kallo sai na ji na tsargu na yi tunanin ma ta gani ,a ɗan daburce na ce “ ni ma ban san me yasa Uncle yayi haka ba,shi ba giya yake sha ba ballantana na ce bai cikin hayyacinsa ”

“Ungo ni ki je ki sha ya fi wannan surutun da kike yi min marar kan gado,duk duniyar nan akwai mai sonki sama da shi Salem ɗin da har za ki yi tunanin zai yi abin da zai cutar da ke” Inna A'i ta faɗa .
Na karɓi kofin kunun tare da komawa can gefe na soma sha sam na ƙi yarda na koma can,ita ma ba ta matsa min amma ina shanyewa sai na fito don tuni gari yayi haske sannan lokacin da za mu je bakin aji ƙarfe bakwai ne.

Ina fitowa na gansa a zaune ido rufe yana wani jan numfashi tare da ɗan game fuska haɗi da yamutsa ta.Toilet na shiga na yi wanka,da na fito sai na tarar ba ya nan.A gaggauce na shirya tsaf,na zuba takardun da zan yi amfani da su da abin rubutu.
Inna A'i ta fito tana min wani kallo kafin ta ɗauke kai,“ki je yana mota yana jiranki ku yi sallama”

Jiki a sanyaye na fita ganin irin yadda ita Innarmu ta canza min fuska wacce nake ɗauka uwa ta biyu.Hijabi na saka kafin na fita,gidan gaba na buɗe na zaune na sunne kai tare da yin shuru ina wasa da zoben hannuna.Kujerar da nake zaune a kai ya ɗan buɗe ta ja baya,da sauri na kalle shi yadda na ga idonsa sun kaɗa sun yi ja yayi bala'in bani tsoro.Murya na ɗan rawa don duk a tunanina kuka ne yayi,na ce “Uncl...” sauran maganar ce ta maƙale jin bakinsa kan nawa abin ma bai tsaya nan ba ya soma shafar hijabina ta sama .Hawaye ne suka soma zubo min ,ba yau ne farkon jin cewa uba yayi mu'amala da ƴarsa ba na sha jin ire-iren labarun nan a kafar BBC amma ban taɓa tunanin akwai ranar da abin zai zo kaina ba don ban taɓa banbance Daddy da Uncle ba.Duk abin da yake yi ko motsi ban yi ba da yatsana ballantana na yi yunƙurin hana shi ,hawaye kawai nake yi don babu bakin kuka saboda Uncle ya mayar da shi sweet ɗinsa.Sama da minti goma kafin ya janye daga gare ni amma ina jin hucin saukar numfashinsa kusan fuskata da na rumtse idona.Shashekar kukansa da na ji ta yi kuma bala'in tayar min da hankali fiye da abin da ya gama yi min,na buɗe idona ina kallonsa shi ma hawayen yake fitarwa kafin ya kama hannuna dukkan biyun ya ce “ don me Naf? Me yasa kike horar da ni da yawa? Me yasa ba ki ganin zazzafar ƙaunar da nake yi miki? I love Naf! Ina sonki,ina buƙatar ki a kusa da ni haƙurina ya ƙare”

Tamkar wacce aka bugawa guduma a kai haka na ji ,kalamansa kuwa kusan tarwatsa min kwanya suka yi sam kasa fahimtar abin da yake nusar da ni na yi.“Wuce ki tafi ki kula min da kanki”ko ida rufe bakinsa bai yi ba na ɓalle murfin motar na fito.....

My book is only 500 via

2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822
[28/02 10:12] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.

*FCWA*☀️

________________________

09

Ƙafafuwana har harɗewa suke saboda kalaman da Uncle Salem ya fesar min,ruhina kuwa yayi wani irin sanyi saboda zazzafan romance ɗin da yayi min wanda ya toni duk wani sirrin zuciyarsa da muradinta na shekara da shekaru.Ta ya zan so Uncle soyayya ta aure? Ta ina ma zan fara wannan cakwakiyar da sam ƙanƙanuwar kwanyata ba za ta iya ɗaukar wannan rikicin ba.Ina shiga ɗaki na tarar da Inna A'i tana jera min takardun da ni ce na fidda su a jaka,ta ɗago ta dube ni kafin kuma ta kawar da kai.So nake na shaida mata kalamai da kuma abin da Uncle yayi min ko zan samu sukuni amma sam ba ta bani fuska ba.Wannan yasa kai tsaye na shige toilet,ga mamakina duk jikina ya ɓace saboda abubuwan da yayi min har sai da na canza pant na kuma wanke fuskata.Ina tsaka da maida kwalliyar fuskata na ji ƙarar tashin motarsa,na ja ajiyar zuciya tare da motsa laɓana kaɗan na ce “Allah ya sauke ka lafiya!” sai na ɗauki wani sabon hijabi saboda wancan duk Uncle ya cukuikuye shi sannan hawayena sun jiƙa shi ta gaba.
“Na tafi sai na dawo”na faɗa dakyar,ta ce “a dawo lafiya” jakata na ɗauka tare da fita daga cikin gidan na nufi can ɓangaren makarantar.

Ina zuwa gaban ajin da zan koya na tarar tuni ɗaiɗaikun ɗalibai sun zo,haka suka gaishe ni irin yadda ake yi.Wani sanyi ya ratsa ni duk sai na ji ƙuncin ya sauka daga zuciyata har da murmushi,ina nan tsaye kamar sauran malamai bakin aji aka soma kawo yaran sai a lokacin na dinga cewa su shiga aji su zauna.Ina nan tsaye wani ya kawo ƴarsa sai kuka take,da sauri na kama hannunta ina mai rage tsayi na ce “yi shuru mana babyna ko ba ki so na baki alawa?”
Cikin murya ƙurciya ta ce “ina so”
Na ce “yawwa to yi shuru sai na baki ,me sunanki?”
“Firdausi”ta bani amsa,na gyara mata zaman ɗan guntun hijabinta kafin in saɓe ta kamar wata ƴata na ce “to yi wa Daddy bye bye sai mu je aji na nuna miki inda za ki zauna” da murmushinta kuwa ta yi masa alama da hannu,ya ce “na gode Madam ”
Na ce “bai komai ai aikinmu ne” sai kuma na shiga aji na zaunar da ita a kujerar gaba ta kusa da kujerar da aka ware domin zamana.

Bayan nan na ƙara komawa can bakin ƙofa,ban shigo ba har sai da ajin ya cika zuwa lokacin tuni ƙarfe takwas ta buga.Ina shiga na yi zaune ina kallonsu ɗaya bayan ɗaya ina jin wani sanyi na ratsa min zuciya,kafin kuma na tashi na bi ɗaya bayan ɗaya ina tambayar kowa sunansa.Dukkansu yara ne da ba za su wuce shekara bakwai ba,wasu ma ba su kai ba,ina cikin zagayen ajin sai ga headmaster ya shigo shi da mataimakinsa.

Takarda mai sunan ɗalibai ya miƙo min da kuma alli wanda zan yi rubutu da allo,liste ɗin na ɗauke da ɗalibi ɗari cicif.Bayan fitarsu ma sai da na sake kiran sunayen yaran kafin na je na soma yin rubuta a jikin baƙin allon wanda yake goge fesss,kwanan wata na rubutu da kuma ABCD sai na soma koya musu suna yi duk bayan na faɗa.Haka muka ta yi har lokacin shan iska yayi,sai dai kamar yadda meeting ɗin jiya ya sanar da mu dokokin makarantar hakan yasa ban fidda su waje ba.

Grand Maa ce ta shigo ita da wata budurwa ɗauke da wani basket,cike da girmamawa na gaishe ta yayin da kuma budurwar nan ta soma raba wa yara abincin da za su ci.Bayan ta gama a gaban idona Grand Maa ta miƙawa wani yaro biscuit kafin su fice.
Bayan an gama cin abinci duk suka je suka jefar da abin take away ɗin a shara nan na ci gaba da yin cours ina aika kowane ɗalibi ya zo ya rubuta harafi ɗaya daga cikin ABCD ɗin da na yi musu.Ƙarfe sha biyu na rana cif aka kaɗa ƙarar rawar tashi ,nan aka zo fara ɗaukar yara ba ni na baro ajin ba sai da kowa ya watse .

A gajiye na shiga gidan,Inna A'i ta yi min Barka da zuwa na amsa ina mai rage kaya na shiga toilet.Bayan na yi wanka ta gabatar min da abinci,na saka plate ɗin gaba tare da ɗaukar waya na kira Ammy bayan mun gaisa cike da alfahari nake bata labarin yadda ranar farko ta kasance ,sai murmushi take kafin mu yi sallama ina gama cin abinci na ɓingire bacci wanda tamkar jirana ake aka ƙara yi min maimaicin duk abin da suka faru a yau ɗin tun daga lokacin da na je na yi tsaye gaban ajina har zuwa lokacin shan iska na yara.Yaron nan da Grand Maa ta baiwa biscuit na ga yana ta kuka yana kallona yana kiran “madam? Madam cikina ciwo! Madam mutuwa zan yi ,wayyo cikina” amma sam wai na kasa tashi daga kujerar da nake zaune,a gaban idona jini ya soma yi masa zuba ta ƙofofin hanci kafin kuma ya faɗi babu rai bayan yayi wata irin ƙara wacce daga nan na tashi daga baccin.

Na yi miƙa tare da duba agogo sai na ga tuni lokacin sallah yayi,kawai na miƙe na je na ɗauro alwala na gabatar da sallar.Sam ban wani bai wa mafarkin da na yi muhimmanci ba sai ma takarda da na ɗauka na soma rubuta abubuwan da zan koyar da su gobe,bayan nan kuma sai muka hau yin hira da Inna A'i lokaci lokaci kuma ina chating abina.
Chapter 15 · 0% Book details