← Book details Fatalwar Deborah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 20

Sashe 1

Fatalwar Deborah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[26/02 16:05] MRS SADAUKI: *FATALWAR DEBORAH*🐲
MAKARANTAR MATSAFA 2☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Ga malaman makaranta

*FCWA*☀️

________________________

01

A gajiye na dawo gida,ina ta ƙoƙarin haurawa sama amma yarana suka rugo tare da rungume ni suna faman faɗin “Mamy! Mamy!” Mohamed na ɗauka shi da ke ƙarami ina mai cewa “yeee! Ɗan gidan Mama,mene ne ka ci duk bakinka yayi shanana?”

Cikin gwarancinsa ya ce “Mama ta bani fura,Inna wake da shinkafa”

“Ƙarya yake Mamy ɗan wake ne Dijo ta yi mana kuma ke ma ta ajiye miki naki ” cewar Abdallah yana mai kallona tsakiyar ido,da sauri na sauke Mohamed ina mai jawo shi na ce “mene ne ya samu idonka?”

“Da muna makaranta ne aljanu suka taso shi ne...shi ne...” sai kuma yayi shuru yana kallon Abidah,ni ma juyawa na yi na dube ta.
Gabana na ɗan dokawa na ce “me ya faru?”

“Wai tana da jinnu in ji Madam ɗinmu” Abdallah ya faɗa yana wani ɓata rai.“Jinnu kuma? ” na yi tambayar da salon mamaki.

“Eh Mamy inda kin ga yadda Abidah ta dinga yi tana tashi sama kamar tsuntsuwa” Abdallah ya ƙara furzo furucin da ya kusa tsinka raunataciyar zuciyata,duk gajiyar da na kwaso ce na ji ta ɓata na zauna dirshen ƙasa ina tambayar ƙarin bayani amma duk sai suka yi min shuru suna kallona cike da tsoro.Ganin ba za su yi magana ba yasa na ɗauki waya na soma ƙoƙarin kiran Abbansu,bugu biyu ya ɗauka yana mai cewa “babyn Uncle ya...” ban bar shi ya ida ba na ce “Abban Abidah ka tawo gida babu lafiya...” sai kuma na fashe da kuka.

“Subahanallah! Meke faruwa ?” ya tambaye ni ina iya jiyo tashin hankali a cikin maganar tasa.

Cikin kuka na ce masa “wai Abidah ke da aljanu yanzun nan Abdallah ke faɗa min”

“Don Allah ki kwantar da hankalinki,ki jira gani nan zuwa ” sai ya kashe kiran.

Haka na saka su a gaba ina kuka su ma suna taya ni,hakan ya jawo hankalin Mama da Inna A'i da suka fito na koro musu ba'asi su ma suka shiga zullumi.Kamar minti goma sai ga Uncle Salem ya shigo sanyen da kakinsa na soja,direct wurin Abidah ya nufa wacce ta rikice lokaci guda da ya ɗauke ta.Ƙoƙarin kwantar mata da hankali ya fara kafin ya ɗauki ruwa ya karanta suratul fatiha⁷,ayatul ƙursiyu ¹,amanar rasulu² sai ya bata ta sha ko minti biyu ba a ɗauka ba jikinta ya fara fitar da zufa,sai dai fa ba irin wacce muka saba gani ba wannan zufa haɗe take da wani koren gumi sannan iskanta bai da daɗin shaƙa.

Uncle Salem yasa hankici fari ya shafi gefen fuskar Abidah nan take yayi datti,sai ya kalli hankicin ya kuma maido dubansa gare ni.Kallo ne mai cike da zargi da kuma son sanin ƙarin bayani.

“Mene ne ke damunta? Ka yi shuru ba ka ce komai ba” Mama ta tambaya.

Uncle Salem ya ƙara haɗe fuska tamau,murya cike da tuƙuƙin baƙin ciki ya ce “Nafisa za ki tambaya ba ni ba”

Duk sai suka maido hankalinsu a kaina,a ɗan rikice na ce “ni kuma?”

“Kin ga ki faɗa mana abin da kika yi wa Abidar kafin maganar ta yi nisa” Mama ta faɗa , wannan karon cikin zafi amon muryar nata ya fita.

Wasu hawaye masu ɗumi suka surnano min,ba na komai ne ba sai na baƙin cikin yadda na ga suna jingina ayar zargi a kaina alhalin sun fi kowa sanin cewa a cikin ƴaƴan nawa uku soyayyar Abidah ta daban ce a zuciyata.

“Auta meke faruwa? Ban gane mene ne suke nufi ba” Inna A'i ta faɗa cikin sanyin murya,da sauri na je gare ta don na ga alamu ita ɗaya ce kawai tudun tsirana.Murya na rawa na ce “Innarmu ki tambaye su ni ma ban san me suke zargina a kai ba,wallahi banda laifin komai...” ban ida rufe bakina ba Uncle Salem ya wani fizgo ni tare da miƙar da ni tsaye ya wanke min fuska da wasu lafiyayyun marika guda biyu waɗanda suka tsinkar da igiyar majiyar sautina,yayin da idona suka yi ɗif ban ganin komai sai baƙin duhu da ya turnuƙe ganina.

Ban ida dawowa daga hayyacina ba na ji yana feso min wasu baƙaƙen kalamai waɗanda ko a mafarki ban taɓa tunanin zai faɗa min su ba ballantana a zahiri.

“Ki sakar wa ƴata ruhinta kafin na yi miki illar da har abada ba za ki taɓa moruwa ba.Duk yadda na yi ƙoƙarin nakasa maitarki wato sai da kika fito da ita fili kuma ki rasa wacce za ki kama sai ƴar cikinki”

Idona da suka yi min mugun nauyi na soma buɗe wa a hankali,sai dai ban ganin komai sai buji-buji.Kafin nan Mama ita ma ta feso min nata,“dama tun can ka san mayya ce ka yarda ka aure ta?”

“Mayya???” na maimaita kalmar a bakina.....
[26/02 16:06] MRS SADAUKI: *FATALWAR DEBORAH*🐲
MAKARANTAR MATSAFA 2☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Ga malaman makaranta

*FCWA*☀️

________________________

02

“Mayya? Ni ce mayyar ko wa?” na ƙara yin tambayar wannan karon na yi nasarar buɗe idona na sauke su kan fuskar Uncle Salem wanda yake ta ƙoto kamar wani kumurci.

“Tabbas ke mayya ce kamar yadda ya faɗa” muryar Daddy ta ratso falon namu,duk sai muka mayar da dubanmu a gare shi har ya ƙaraso ya zauna kan kujerun da ke nan falon.

Hawayena ne suka ƙara gudu wurin zuba jin mahaifina ma wanda ya kawo ni duniya ya gaskata maganar da nake jin gwara ace ajalina ne ya riske ni kan a ce gaskiya ce.

Na rairafa wurin Daddy tare da kamo dukkan ƙafafunsa,kaina na shiga girgiza masa murya na ɗan rawa na ce “don Allah Daddy ka bar faɗar haka zuciyata za ta yi bindiga”

Yasa hannu ya kamo kafaɗuna kamar wata ƙaramar yarinya kafin ya ce “ Nafisa ana haifar wasu ne don su zama bala'i da annoba ga al'umma,ke kuma an haife ki ne don kawar da wannan ɓarnar ki kuma kawar da kambun maita.Tabbas na san na yi babban kuskure na nisanta ki daga cikin garin Victoria Falls,domin a can ne kawai za ki iya yin rayuwa ba tare da kin fuskanci ƙalubale ba don akwai ire-irenki da yawa”

“Ire-irena kamar ya? Don Allah Daddy kar ka ce min Mayu domin ni ba mayya ba ce” na faɗa ina mai fashewa da wani matsanancin kuka mai taɓa zuciya.

Daddy ya ce “sai haƙuri Nafisa amma ba za a taɓa canza wa tuwo suna ba,alƙalamin ƙaddararki ya riga da ya bushe. Yanzu kuma lokaci yayi da za ki fara fuskantar kanki ”

A hankali na zame daga jikin Daddy na miƙe tsaye na soma ja da baya ina girgiza kai,ko kaɗan ba zan taɓa yarda da wannan tashin hankalin ba .Kamar wata mahaukaci haka na ruga zuwa kitchen na ɗauki wuƙa,ba tare da wani tunani ba na yanka hannuna daidai babbar jijiya ta magudanar jini.

“Gwara na mutu da na dinga amsa sunan mayya wallahi ba zan yarda ba” na faɗa ina ƙoƙarin jan ƙofar kitchen na rufe,sai dai tuni Uncle ya rige ni.Wani irin mugun riƙo yayi min ya fitar da ni daga kitchen ɗin,duk yadda na so kashe kaina hakan ɗin bai faru ba don tuni ya tsayar min da jinin tare da ɗura min maganin da ya saba bani.

Tun ina kuka tare da suratai har na soma gajiya ,a hankali kuma idona suka fara lumshe wa alamun bacci na son ɗaukata.

UNCLE SALEM ya ja wata irin ajiyar zuciya yana kallon fuskar Nafisa wacce lokaci guda har ta faɗa,sai yanzu kuma yake ganin bai kyauta ba sam da ya ɗauki mataki kai tsaye ba tare da wani tunani ba.
A kunyace ya dubi abokin nasa kuma surukinsa ya ce “mu je daga ciki”sai duk suka haura sama ,a falon Uncle ɗin suka zauna kafin kuma su yi shuru.

Daddy ne ya fara yin magana,“aboki kana tune da cewa fatalwa ba za ta taɓa yi wa mutum wata hidima ko taimako ba dole da sai da wani sharaɗin? To Deborat ta ƙara bayyana a ɗakina yau a karo na biyu,sannan ta sanar da ni cewa kai ma ka san da dole za ta zo tun da ta shigar ma faɗa ”

Uncle Salem ya ja wata ajiyar zuciya kafin ya ce “to amma mene ne na sako Abidah a ciki? ”

“Saboda Nafisa ta fi sonta a cikin ƴaƴanta” Daddy ya basa amsa.

“Mene ne mafita yanzu?” Uncle ya tambaya .

Daddy ya ce “da dukkan alamu akwai wani kuskure da ka yi ,ko kuma aikin kawar da matsafan nan bai kammalu ba” Daddy ya faɗa.

Uncle Salem yayi shuru yana nazari kafin ya ce “ yanzu dai abu na farko da za mu yi shine ganin mun disashe kambun maitar da ke jikin Abidah kamar yadda na dinga yi wa Nafisa tun tana ƙarama zuwa yanzu.Amma abin da ya fi ban mamaki bai wuce yadda cutar ta yi saurin bayyana a jikin Abidah ba alhalin duk wani ƙarfin iko na power yana bayyana ne a shekaru sha uku zuwa sama”

“Mu saka ido kawai sosai”Daddy ya faɗa tare da miƙewa tsaye , Uncle yayi masa rakiya suka sauko ƙasa har zuwa yanzu Nafisa na ta yin bacci ita da Abidah.

A nutse yake kallon su duka biyun,wani abu yake gani suna masayen ta bacci mai kama da kambun maitar ido sai dai bai san ta yaya zai yi ya dakatar da su ba.

Ragowar ruwan addu'ar ya ɗauka ya zuba wa Abidah,da wani irin bala'itacen ihu ta tashi daga baccin tana kiran “ina son sha jini! ”
[26/02 16:07] MRS SADAUKI: *FATALWAR DEBORAH*🐲
MAKARANTAR MATSAFA 2 ☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Ga malaman makaranta

*FCWA*☀️

________________________

03
Chapter 1 · 0% Book details