← Book details Doctor Sageer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 25

Sashe 9

Doctor Sageer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  " Nan da nan kwallar bakin ciki ta cika idonta nan ta goge hawayen ta tace ina tausaya miki ramlat ace ashekarunki kin haihu? Mijinki zai gujeki daga nan yafarayi miki wulakanci daga karshe kuma sai kishiya...

    " Ramlat ce tace anya kuwa kinsan yadda dr yakeson haihuwa kuwa?

     " Tohm shikenan zakiga yanason haihu akan idonki zai wulakanta ki kuma babu yadda zakiyi kuma acikin manyan mata ma kallon raini zasu dinga yimiki kina babbar hajiya araina ki...

   " wallahi hakane yanzu yaza'ayi to??

    " ki tashi muje azubar shine kawai mafita...

     " To wanne asubutin zamuje??

      " Babban asubuti zamuje akwai kawata acikin asubutin ai... "  awanne bangare take?? " tana bangaren emergency...

     " Okay tashi muje sannan suka huce zuwa asubutin ...

   Yasmin dake k'an gado tana tunanin irin kalaman dr sageer tabbas namijin mazaje ne mijin da kowacce mace ke fatan ta samu wani murmushi tayi sannan tace ya Allah karabani da auren da ba soyayya...

     " yasmin zanje asubuti kafin nadawo ki dora abinci...

   " Mama wane babu lafiya?? " Sageeru mana ...

    " Shiru tayi sannan tace tohm Allah yabashi lafiya sannan taje tayi alwala nan tayi sallah tare da addua Allah yabashi lafiya..

    Su ramlat suna sauka tace rabia mijina fa babu lafiya muyi sauri ji nakeyi kamar wani abu zaifaru...

    Ke kinfiya matsala wallahi aikin banza zo muje suna shiga sai kuwa sukayi karo da dady nan yakifa mata mari sau biyu da sauri baffa yace haba alhaji menene haka???

    Dan ubanki mijinki bai baki daman fitaba kike fita ?? Sai yanzu kikaga damar zuwa??

  Gabanta ne yayi mummunan faduwa sannan tace wallahi ...

    " mumy ce tace kada kice komai munafuka...

    Rabia ce ta salallaba tayi sauri tafita bata tsaya ko'ina ba si motarta cike da dariya hahaha har iyayenki sai nasaka sun tsinemiki hahaha taja motarta tatafi....

Ramlat ce ke kuka tana fadin nashiga uku ina mijina yake??

     Mumy ce ta dakatar da ita mijinki din uban wa mara tarbiya??

     " hajiya ce tace haba mumy ai bahaka ake ba har yanzu fa yarinya ce ramlat kiyi mata ahankali kikasani ko wane case din takeyi mai mahimmanci...

    " mumy ce tace wane irin case ne daya huce cutar mijinta eh??

    Haka sukayi jugum jugum mumy tace ramlat bazata zauna dashi ba mama ce zata zauna ....

    " Har karfe tara shiru har ya huce 20hours har yanzu bai farka ba...

     " hajiyar sageeru ce tayi cikin dakin nasa ta zauna akusa dashi inbanda kuka da addua babu abunda takeyi...

   Yasmin dake zaune a palour tarasa menene yake mata dadi, tun dazu sai tunanin dr sageer takeyi cikin yanayin kunci tace why my heart nan hankalinta yakara tashi taga har goma basu dawo ba abinci ta zuba sannan ta nufi hanyar fita tare da rufe kofar su tana kokarin fita bilal yace uwar gantali inakuma za'aje??

     " Gidan uban da ka aikine sannan ta bude kofa tafita nan tasamu mota tahuce asubutin...

     Lokacin data isa gaba dayansu sunyi jugum jugum tana karasawa dakin taga hajiya tanata kuka... cikin tashin hankali tace hajiya lafiya shiru tayi mata sai alamar kuka...

     " a tunanin ta mutuwa yayi cikin tashin hankali ta matsa kusa da gadonsa tana kuka hannunsa ta ruki tace ya sageer please karka mutu danAllah karka barmu tana wani kuka mai cike da tashin hankali...

  " A hankali ya bude idonsa kalmar da tazo bakinsa shine yasmin...yasmin..yasmin....zaki aure ne???

   " batasan lokacin data miki sannan tayi waje ba tana kuka nan dukk'an su suka tashi sukayi hanyar ciki ba kowa yana kallonsa yana Alhamdulilhi ramlat ce ta matsa gurinsa tana kuka...

" likitane yashigo sannan yakara yimasa allura..

   " Alokacin hajiya suwaiba ta miki tabi yasmin...

Assalamu alaikum!!!

       *Please and please kuyimin afuwa da yawan shuruna da kukeji,Allah yasaka muku da Alheri ina ganin sakon ninku....Nana diso love u so much....*

   _I can't stop apologized for the  spelling and grammar mistake's_

     *How was the page???*

    _Please do vote comments and like my story really need your comments and vote#TEAM....DS

Wato haqiqar haquri shi ne bãwa ya gudãnar da rãyuwarsa a lõkacin musiba/balã'i kamar yadda yake gudãnar da rãyuwar lõkacin zaman lãfiya !

Dõmin Allah SWT bã ya qar'bar wani abun daga wajen bãwa; fãce sai dan ya bãwan yayi haquri, haqurin kuma ya sanya Allah SWT ya so bãwan kamar yadda Allah SWT ya fad'a cewa:
(( Kuma Allah Yana son mãsu haquri )).

Bisa ga haka idan Allah SWT Yana son bãwa sai ya zã'bar masa abin da yafi alheri gare shi da ma duk abin da zai zama maslaha a gare shi, don haka sai bãwa ya yarda da hakan.

*Urs Nana diso*

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:[email protected]

Gmail:[email protected]

Wattpad:NEIRNAHDISO

[11/6, 8:24 AM] ‪+234 703 475 7034‬: 45-50

*_DOCTOR_*
        _*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Dago k'anta tayi sannan ta k'alli yadda ya rike hannun ta, cikin kuzari ta zare hannun ta sannan tace lok'aci fa yana kurewa?

     " batare da yace mata komai ba ya cigaba da driving sai da yaje daidai kofar jami'ar sannan yatsaya...

     " jiyowa tayi tace nagode... " har tayi gaba sannan yace yasmin?

    " Cikin nutsuwa ta karaso har inda yake sannan tace Naam!

     " cikin daure fuska kada taki gayamasa yace karfe nawa zaki tashi???

     " sai lokacin da malamar tazo nayi mata submitting ai...

     " Okay to kikula da kanki bye bye..." wata harara tayi sannan tace tuntuni bai taba cewa in kula da kaina ba sai yanzu...

  Wallahi mamee dr son yasmin yakeyi Allah bazan yarda ba sau dai ni ya aure ne...

  " ke ki kwantar da hankalin ki indai nice bai isa ya aure yasmin ba tabbijan ki kwantar da hankalin ki nasan me zanyi...

     " Maryam ce tace yauwa mamee ta ai yasmin da mai gadi ta dace wallahi...

     " Alhaji haruna ne yace ai sageeru sai nasa yan fashi sun nakasa shi ina tambayar sa bashin kudi sai cewa yayi kowa zai bashi kudi amma banda ne ai wannan raini ne zaici ubansa....

    " lallai wuyansa yayi kauri Daman ai shi dan Adam butulu ne...

   Barister ramlat dake zaune a office dinta duk cikin yanayin damuwa, irin rashin kulawa da dr yake mata har yafara taba mata zuciya tana cikin tunani sai ga rabia ta shigo....

    " ke dai sai kinsawa kanki hawan jini baki da tunani sai na namiji to sai kiyi tayi su hada miki hawan jini ai ki rabu dashi nahada ki da sugar dady wanda sukafi miji ki komai....

     " me kike Nufi rabia?

Dallah ina nufin maza mana ki rabu da dr nahada ki da wasu ku shakata akwai wani sabon Alhaji da aka hadani dashi sai na barmiki shi...

    " Allah yakiyaye wallahi ai ni bana zina ingayamiki ko shekara nawa dr zaiyi baya kulani bazan bi maza ba...

   " kinga kar kigayamin babu dadi kikasan irin shi matan dayake kula? Ya dirka miki cikk yabarki da sha'awar sa kuma yayi ficewar sa dan love dinnan bai nunamiki shine zaki dinga fiffiga akansa??

     " aa rabia komai fa lefe nane abubuwa nawa nakeyi baya kulanani yayi hakuri dani sai yanzu zanje haushi, ciki kuma kinsan babu maganin da ban shaba yake barewa ke duk ba wannan ke damuna ba aure da zai kara...

   " ke kikasani malama ainaga nakya daukar shawarata sai kiyi abund kikaga shine daidai...

    Mtsww ke fa rabia matsalata dake fushi dallah kigayamin zan dauka...

    " kinsan namiji ba'ayi masa sanyi in kin koma ki yimasa rashin mutunci kikuma yimasa kashidi ke in san samune ki gudu gida zakiga ya janyi ko kefa yanzu kikayi magana me kyau ni bari natafi sai gobe...

   Okay bye bye...tana fita rabia tasa dariya tare da fadin ai sai na kashe miki aure bake kawa ba...

Karfe 5 yasmin ta dawo daga skull abinci tace sannan tazauna bakomai take ba sai tunanin dr sageer tabas tabbas tana tsoron shiga tarkon soyayya Amma kuma gwara tayi aurenta itama ta huta cikin wannan tunanin hajiya tashigo tace yasmin?..

   " Naam hajiya  .... " wai meke tsakanin ki da dr ne? Naga duk ya mutu akanki ko soyayya kukeyi...

    " Murmushi tayi tace lahhh hajiya bakomai fa kawai jinin mu yazo daya ne... " Da bakyason sa bazakiyi wannan murmushin ba bazakuma kiyi magana a hankali ba abunda nakeso kigani shi miji nagare shine wanda zai soka koda mutane na zagin ka kuma kigane cewa ita soyayya masu hankali akan saba kuma a daidai ta, kuma ki daina tunanin sai wanda ranki yakeso aa kiyi adduar nagari mai addini wanda zai tararrayi ki, tabbas nasan sageeru yana sonki Amma kuma ya kamata ki amince bawai ina goyan bayansa bani aa kinsan yana da matsalar zuciya kuma zanso ki kasance akusa dashi...

    " Ita dai yasmin batace komai ba har hajiya tafita palour...

    " wayar ta ta kunna hotonan sa ta shiga dannawa kallonsa takeyi cike da kauna..

    Mama ce tace daman hajiya inaso muyi magana kafin ki tafi?

    " Akan me fa?

" A kan sageeru ne dayace a nemar masa mata ni kinga ba harka nake da mutane ba kamar ki ko ke zaki duba masa dannaga yana bukatar karin aure...

    " To ke banda abunki ga yasmin nan me zai hana ahadasu...

    " Nasan halin yasmin hajiya ba lallai ta soshi ba kuma kinga shima dr sageer din ba lallai yasota taba kina ganin yadda ake sokarta cewa taki auruwa nafeson daidai da'ita ya aure ta....

    " Mama kenan ne zanyiwa baffan magana inyaso sai abasu lokaci zakiga in suna son junan su...

    " Mama ce tatashi tashiga daki nan takira aisha tagayamata...Aisha ce tace ai mama kece baki saniba yasmin ta dade azuciyar dr ai ke dai kawai kiyimata addua Allah yasa alkhairi ne ...." inshaa Allah sannan ta goge hawayen ta dama zanga auren yasmin Allah nagode maka...

    Alhaji haruna ne yafito yaga baffa ya chanja mota tsayawa yayi yana kallon ta can yace kace kafara sayar da kawonan mutane kazama dan fashi ko dan mafiya in ba mafiya ba uban wa zai baka kudinnan dakake samu...

    " Baffa babu abunda yace sannan ya huce bangarensa....
Chapter 9 · 0% Book details