← Book details Doctor Sageer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 25

Sashe 23

Doctor Sageer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Acikin ki mana...? " cikin kunya ta kashe wayar ta kalli ramlat tace lafiya kika tsayamin aka??

" Tsaki tayi ta shiga palour dinta nan da nan yasmin tashiga kitchen tunani tayi menene abu mai sauki dazata sarrafa musu?

   Can tace bari nayi musu CP DRINK'S , abarba ta dakko ta yankata sai ta dakko cocumber ita ta yanka guda biyu sai ta zuba su acikin blender tasa ruwa ta markada ta tace sannan ta juyeshi acikin jug tasa sugar directly fridge ta sakashi..

    Bari to Na hada musu da cake alokacin ramlat tashigo wai me kikeyi ne??

    " Abunda kika sakani atake ta dakko kwai guda huda ta zubo flour cokalin cin abinci goma, ta dakko flavour dinta vanillah essences ta ta ebo sugar cokalin cin abinci 6 sai butter dinta simas ta zuba cokali 4 sai baking powder dinta ta gwangwani...

     " Ramlat dake ta saki saki acikin ranta tabbas yasmin indai gurin girki ne ta'iya yadda na dade inasom koyan cake bari nayi shiru na koya...

    " Atake yasmin ta dauki karamar muciya ta zuba butter da sugar a dan bowl kusan minti 5 tanata juyasu har suka fara canjawa sai tafasa kwai ta jujjuya sannan tasaka flour da flavour 1table spoon da baking powder 1tea spoon ta jujjuyasu har sai da suka hade jikin su sannan ta dakko papers na cupcake ta zuzzuba aciki ta kunna abun gashinta ta kunna wutar sama da kasa ta jajjirasu...

      " yasmin tayi dariya acikin ranta tace ni bazan koreki ba duk tsiya kya koya sannan tafito ta gyara palour din kamshi koina ramlat sai tazama yar kauye cikin ranta tace maccen da bataiya girki ba tabbas da sauran ta, duk girmana dr bai ce nayi ba sai ya kirawo wacce ta'iya ....

     " yasmij tazo tacero cake din yayi bala'in kyau ga kamshi nan ta barshi yasha iska sannan tasaka shi a cikin wani bowl ta rufe da abar rufe abinci Sallama taji alamub su mamee sun karaso...

    Alhaji haruna ne yace iyayen rashin tarbiya ko bakuji anata sallama ba??

    " ramlat ce tace sassanun ku da zuwa...

    " Alhaji isa yace ina ita karuwan??

     " Tana kitchen ...

  Yasmin ce tafito dauke da plate da jug da cups tana aa manya iyayen kirki ne to sassanunku..

    " Mamee ce taja tsaki tace dai kace mutuniyar kirki...

   " yasmin ce tace alhaji ya kasuwa??

   " Alhaji isa ne yace kasuwar uwarki bayan ubanki yacinye gadon..

     " Jikinta ne ya mutu tace ina zuwa tayi sama tashiga wanka don taji karar motar dr tana saka turare dauke da towel ta tsaya maganar da suka gayamata ita ke yawo akanta sai hawaye...

    Dr sageer yana shigowa yace au kun karaso sassanun ku yagida kuna lafiya??

    " Cikin faraa mamee ta amsa tace ga turaren danasa a hada maka inata Allah Allah akawo maka namanta...

     " Toh madallah nagode, ramlat ina yasmin?? " cikin gyatsene fuska tace tana sama...

  " Alhaji haruna ne yace au kaima sun asirce ka lallai..

    Batare da yace musu komai ba ya hau sama yana shiga yaganta tana zaune ko kaya bata saka ba tanata hawaye...

    " zama yayi kusa da ita yace my one? Me sukayi miki??

    " Cikin shagwaba tace mamee ce fa tacemin karu.. " kafin takarasa yasa bakinta acikin nasa kusan minti 3 yana kokarin zame towel din tace yaya baki fa mukayi..

    " Allah yasmin zan iya haukacewa shaawa ta takai label din da bazan iya daukar kaina dangirman Allah kiyi hakuri kibarni...

    " Haba yaya munyi baki fa kuma jiranka sukeyi... janta yayi kusa dashi nooo yasmin zan iya mutuwa please please sannan yaja towel dinta...

     " To naji kabari su tafi.." yasmin DanAllah karna zauce please..bakinsa yasa anata kukan da taketayi yasa ya saketa kinyi min alkawari ko?

     " Aa ni banyi maka ba tana kokarin tashi.." Aikuwa takarfi sai na karbi hakkina wannan horon dakikeyi min yayi yawa ..

     " Tashi tayi sannan tacanja kaya shima yayi wanka ya canja kaya sakkowa yayi yaga sunata gulmar yasmin itama sakkowa tayi takaimusu abinci da cake  ..
  Zata zauna dr sageer yace my one dawo kusa dani, murmusho tayi ta zauna kusa dashi duk suka saki baki...

     " Mamee ce tace kutashi mutafi maryam dakkomin cake din ke kuma zakici ubanki sai munfitar dake wallahi...

    " yasmin tayi dariya ta rungume dr tace kaji fa???

    " yama manta suna palour yace please my one kada ki haukatani da sonki ...

    " Alhaji haruna saboda takaici sai yabar gurin cikin zage zage suka bar gurin...

     " ramlat tace Allah yaisa tsakanina dakai ka dauki son duniya ka dorawa karuwa...

   A gigice ya kifa mata mari yakara kifa mata mari are u idiot yasmin ce karuwar how idiot are you   to call her with such name???

    Yasmin ce tace haba mijina kayimata afuwa mana kasan bata danjindadi...

    Wallahi wallahi kikara gayamata sunan nan sai na saba miki ina muhammad  kuma???

   " cikin kuka ta mikamasa shi...

    " YASMIN Takarba tace yarona muje yau agurina zaka kwana...

     " ramlat tace babu inda zaije babu inda zaije..

     " Dr sageer zaiyi magana yasmin tace aa karkace komai yaro ai sai uwarsa muje kace abinci please...

    " cikin kuka tabar palour din tana zagezage...

    " yasmin ce tace miji nagare baya dukan matarsa dan Allah mijina karka kara marinta...

    " ramlat ce tace munafuka tsinanniya wallahi sai nayi maganinki...

   " dr da idonsa yakada yace kinji ko ni bazan samu nutsuwa ba daga wannan sai waccan wannan wani irin bala'i ne??

     "Hannun sa ta kama tace kayi hakuri danAllah..

    " yasmin wallahi akanki kowa sai na bata dashi inasonki yasmin ina kaunarki DanAllah nima kisoni please...

     " Tashi tayi ta hau sama...

   Binta yayi da kallo yana cin abinci...

     Ramlat takasa zama babu shiri ta kirawo rabia kawata yaya akayi??

     " ramlat tagayamata komai rabiaa tace aini jira nakeyi ki kashe aurenki na aure dr...

     Kinada hankali rabia kinasona kuwa?? " Ai duk duniya babu wacce natsana sama da ke kuma ko ta halin yaya sai na kashe miki aure...

     " Ramlat ce takashe wayar tana ambatar innalilahi...tabbas silar kawa zankashe wa kaina aure na shiga uku...

Assalamu alaikum

   *how was the page??*

SOYAYYAR YASMIN DA DOCTOR TANA BURGE KU???

      *ina fata kuna daukar darasi acikin wannan littafin kunga sharrin kawa da makircin kishiya ga kuma kiyayyar kanin uba...

    NA SADAUKAR DA WANNAN PAGE DIN GA DUKKAN MASOYAN LITTAFIN NAN UBANGIJI ALLAH YASA KUNA ANFANA DA ABUNDA YAKE CIKI NA DARASI ABUNDA BANYI DAIDAI BA ALLAH YAYAFEMIN...

INA GODIYA DA SOYAYYAR DAKUKE NUNAWA WANNAN LITTAFIN ALLAH YASAKA DA ALHERI...

    Please do vote comments and like 👏

GO AND SUBSCRIBE TO THAT YOUTUBE  CHANNEL GA SHI CAN NAYI POSTING A FARKON PAGE DIN...FOR THOSE WHO WANT TO LEARN  FOOD,SNACKS AND DRINKS....👆🏼

👆🏼👆🏼please click the link and subscribe  ..

   Urs *Nana diso*

Email:kabba43@yahoo. com

Gmail:[email protected]

Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/6, 1:19 PM] ‪+234 703 475 7034‬: 95-97

  *DOCTOR*
           *SAGEER*

_NA NANA DISO_

      https://www.youtube.com/channel/UCvopCYalw1ooSYq-rMhjm5g

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

     " Ramlat ce takashe wayar tana ambatar innalilahi...tabbas silar kawa zankashe wa kaina aure na shiga uku...

    Rabia ke faman dariya tana juya wayarta tabbas lokacin auren dr sageer yayi namiji mai son matansa ga nutsuwa ga ilimi ga arzuki duniya ma yi takeyi dashi zan kokarta shawo hankalin sa naga....

     " Tun da safe dr sageer yafita domin yanada almost 6 hospital da zaiga marasa lafiya ko'ina haka yaje last asubutin da yaje matashi ne bai fisa ba matansa da yaransa suka saka masa hawan jini, tabbas ba karamin girgiza yayi ba especially da ciwon mara lafiyan yayi tsanane har takai sunyi masa aiki yana komawa office tuninsa kawai yakeyi, Tabbas idan bantashi nagyara gidana ba to nima zan samu matsala datafi ta wannan mutumin...

    " nurse ce tashigo tace doctor kayi bakuwa tace kasan da zuwanta...

   " Kinsan dai natashi I can't see anyone yanzu sai dai ce nemata ta shigo...

   " Nurse dince tace mata you can come in dear...

     " Wasu red gown rabia tasaka half kirjinta abude sai wani mayafi data yafa da bai huce iya saman kanta ba ga black jaka tasaka gum abaki ga kuma glass tana shiga tace....

    " Can i seat down??

" Batare da ya kalleta yace yes?? What your problem?

     " Sunan wani babban likita ta fada tace shine ya turoni gurin ka..

       " Har yanzu bai dago ba, yace menene matsalarki lokacin tafiyata yayi...

     " uhm doctor sageer inada matsala acikin vigina ta...

      " bag dinsa ya dauka sannan yace u can work out ni ba likitan wannan bangaren bani ba...

      " Dr sageer husband to yasmin and ramlat, matanka kullum cikin rigima and ba sonka sukeyi ba...

     " jiyowa yayi cikin mamaki yace how dere u...

    " Am sorry karka karasa nasan gidanka sosai yasmin bata sonka kwanaki ma cikinta yabare duk dan dai karta haihu da kai..And ramlat tana zaune dakai dan taci dukiya...

    " ke wacece dazaki zo kina zance akan sirrin gidana how idiot are u getout of my office kafin na baki dirty slap...

    " I will get out basai ka marini ba Amma kuma nasan kanacikin tsananin shaawa ne cuz ramlat na jego and yasmin bataso ta hada jini da kai kawai dai biyayyar iyaye takeyi, and the last thing da zangaya maka sai ka aure ne...

    " Kasa cewa komai yayi sai zuciyar sa datake tafarfasa sauri yayi yaja mota dakyar yake driving din yana isa yaga yasmin na zaune ramlat sai faman zage zage takeyi...

   " Ramlat sai saukar mari taji cikin gigicewa tajiyo tana kuka...

    " from today duk macen da ta kara shigomin gida sai dai kubita kuma wallahi bazaku sakamin cuta ba kullum bala'i babu kwanciyar hankali kun maidani shashasha to nagaya muku baku ba kawa kuma kusani zanyanke babban hukunci aure zan kara...

    " yasmin da abinci ke bakinta tayi saurin fito dashi aure yaya??

    Ramlat kuwa shiru tayi tana kuka tana DanAllah kayi hakuri...

     " bana zance biyu dukanku babu mai kula dani kun maidani...

   Sai kuma yayi sauri ya hau sama dakinsa ya shiga wanka yayi sannan yafara aiki yana cikin aikin yatashi tsaye zantukan rabia ke yawo a kwakwalwar sa " ai yasmin dinma bata sonka biyayyar iyaye takeyi taki hada zuria dakai.."
Chapter 23 · 0% Book details