← Book details Doctor Sageer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 25

Sashe 2

Doctor Sageer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yasmin yarinya ce fara amma irin siraran nan, ga kuma hanci kina ganinta kinga jik'ar ba fulatani, Babu ruwanta tun tana karama kawayen ke ce mata 'yar aljanna saboda hakurinta, lokacin da take aji biyu a islamiyya kwata kwata bata gane karatu hakan ya kansata kullun cikin kuka har mama ta gane sai tafara tambayar lafiya?? Ta sanar daita halin da take ciku daga nan tace ba kuka zakiyi ba addua zaki dingayi nima zan tayaki inshaa Allahu zaki fara fahimta, "Allah to yasa kamar wasa tana zuwa makaranta tana addua cikin shekaru 2 sai gashi tafara karbar kyauttuka, su abida maryam kuwa da kubra sai ma tsanarta da suka karayi haka ta dinga rayuwa cikin kuncin rayuwa. A kwai lokacin da bata da ikon zaman gate anayi mata karatu sai kiga bilal yazo ya zaneta ita kuma aduniya ta tsani bilal saboda zaluncin sa,Dr sageer kuwa irin hidimar da yakeyi masu takanyi masa Addua sosai duk da karancin shekarunta amma bata sakewa da kowa, tana kallon yaran gidan za'aja su amota amma ita sai dai akafa,tana makatantar gamnati amma su sunayin ta rabin million kullum burin su su zageta dalilin haka mahaifinta yace zai kaita boarding ko tasamu ta huta, Mahaifiyarta taso ya barta ta cigaba Amma ina yaki hakan nasa zuciyarta k'una...

Cigaban labari...

Dr sageer ke faman juyi akan kujerar sa ta office babu abunda ke damunsa irin tafiyar yasmin kai yanzu ba zanga kyakyawar fuskarta ba kullum ga lafazunta mai sanyaya zuciya, har khalifa ya zauna akusa da mashi amma bai kulaba...

" Haba doctor wannan tunani ince dai lafiya???

" Jiyowa yayi yace ina kuwa lafiya? Baffa ya kai yasmin makaranta...

" To a gaskiya dr zangaya maka gaskiya ka ajiye maganar yasmin a agefe kafara zancen bikin ka...

" Hmmm daman ai na lura kafi son ramlat, to bari ingaya maka yasmin tsoka tace babu ta inda zamu rabu ni inaso ka binciko min boarding din da suka tafi...

" ai nasanta ko yabzu sai na rakaka sai dai nisanta...

" yanzu kayi magana mutumi na ina godiya ran sunday maje...

Yasmin dake aji azaune tana karatu kamar daga sama taji anyi mata sallama tana daga kanta taga wata yarinya ce da bata huce suyi shekaru daya ba cikin murmushu ta amsa mata sallamar...

" sunana yusra nima last week nazo skull dinnan kuma naga babu ruwanki ga son karatu ko zamu zama kawaye?

Murmushi tayi tace ni yasmin sunana, ina kuma fata zamuyi kawanci nagari??

" inshaaAllah daga nan suka kullah kawance...

Mumy ce tafito zata tafi office tace dota?

" Tace yes mum har kinshirya?..

" Eh ramlat idan dr yazo kya gaishe shi..

" ohh mum bakyason dr sageer dina wallahi....

" haba my barister ni kuwa nake son sa...

" rungume mumy tayi tace har naji dadi lurv u momma...

Yau sunday kowa acikin makarantar ana kawo musu visiting kowacce tana shigowa da abubuwa amma yasmin tana gefe bata cewa komai, alokacin dr yazo yana zuwa yace yar aljanna kamar daga sama ta ruga ta rungumesa tace yaya??

" Dr sageer ne yaji dadi yadda tayi murna da zuwansa cikin murna yace yakike kanwata?kina dai karatun ko??

" inayi sosai wallhi ga mama da baffa?

" Suna gaida ke! Yasmin yasmin?

'Naam ?? " kinsan ina sonki ko?

" eh tace.." to kada ki kula kowa kinji da niyar soyayya kinga yanzu karatu kikeyi...

" Tohm bazan kulaba, nagode da zuwanka lokaci yayi..

" sawa yayi aka shigo masa da abubuwa da yakawo masu yawa sannan yace duk nakine..

" Nagode Allah yabiyaka sai anjima..

" har tayi nisa yace yasmin??.

"Naam..

Kikula da kanki kinji?

" Tohm tace sannan aka shigar mata da kayan..

Tundaga nan ya huce gidansu barister ramlat cikin fara'arsa yashiga palour tana zaune tayi bala'in kyau, yanayin saĺlama ta miki...

" to bakin munafuki bakin dan iska yaudarata dakakeyi to Allah ya rufamin asiri murabu tu daga yau...

" haba ramlat me yayi zafi haka??

" dan iska mai bin mata fitar min agida...

" kifa mata mari yayi see this stupid kika kara jifana da zafaffan kalaman ki wallhi sai na hukunta ki, kuma daga yau babu ni abu ke sannan yafita rai abaci......

Cikin kuru ruwan kuka ta nunashi daga nan kuma tafara nashiga uku inason ka sagee....

_*Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment...*_

_Let me know what you think about this page...Ku gayan ra'ayoyin ku..._

*i request you to avoid spelling and grammar error....#TEAM DS*

GOD BLESS YOU OLL....

*Urs Nana diso*

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:[email protected]

Gmail:[email protected]
[11/6, 8:22 AM] ‪+234 703 475 7034‬: 10-15

*_DOCTOR_*
        _*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Kuk'an da barister ramlat ke famanyi yasa gidan gaba daya ya dauka, adaidai lokacin da momy take kokarin shigowa gidan sautin kukan 'yarta tace yakara firgeta ta cikin sauri da hanzari taisa cikin gidan nan ta tarar da ramlat a shaime tana wasu irin maganganu, dotar??? What wrong with you? Ya'ilahi.....

    " Rungume mumy tayi sannan tace baya sona mumy yace mun rabu wallhi zaki'iya rasani akan dr sageer,mumy please kibashi hakuri kuskure nane...

  " Ya'ilahi me kikayi masa? Always ina gayamiki kina iya magaba kina barister amma u need to change your words namiji bazai dauka ba....

  " Wallahi Rabia ce tace yaudarata yakeyi if yazo naci masa mutunci zai daina kuma zai tsorata....

    " are u mad ramlat? Sau nawa ina cewa kirabu da rabia ba mutuniyar kirki bace ba, kuma ke ina ilimin ki? Mtseww ke kika jawowa kanki dan haka sai kiyitayi....

   " mumy please karkice haka haba mum please ki bashi hakuri please mum!!

   " Har cikin zuciyarta ta tausaya mata especially tafita hayyacin ta hakan yasa tace ke zaki shawo hankalinsa not me tashiga daki...

   " cikin wani yanayi da fargaba ta dauki wayarta tafara kiransa ta kirasa yafi sau 10 amma bai dauka ba.....

   Yasmin ke faman karatun Al kurani malamin math ya shigo nan yayi musu sannan yabafa class work duk wanda bai iyaba bulala biyar ce, yusra kawar yasmin kwata kwata bata iya ba gashi tarasa yadda zatayi yasmin data lura da hakan sai ta bawa yusra littafinta ta karbe nata tana gama solving a tsoroce ta mika mata nata...

  " Duk class din da yafara marking mutum uku ne kawai sukaci nan ya dinga duk'an kamar an aiko shi...

   Yusra ce tace godiya nakeyi kawata kin taimaki ne sosai...

   " yasmin ce tace bakomai kawata malamin math din nan mugune wallahi taso muje na koyamiki yadda ake solving din..

    " Nan suka tafi suna 'yar hirar su can irs teacher yace yasmin?

   " jiyowa sukayi suka gaishe shi cikin murmushi yace kina dai lafiya ko?

   " cikin rashin fahimta tace eh sai anjima sukayi gaba, yadade yana kallonsu har Allah yasa suka huce wasu senior dinsu wata daga cikin su tace kee yarinyar nan zo?

   Tohm gani inji yasmin..

       " ga kayana kije ki wanke min kinji...

    " Tohm shikenan, zata karba tace au ashe kinada hankali barshi nafison yarinyar da zatace bazatayi ba.....

  " Tohm nagode suka karasa hucewa,yusra ce tayi tsaki gaskiya kinada over hakuri yasmin ke komai babu ruwanki ???

Maryam ce ke cikin motar saurayin ta sai rangwada takeyi tana wani narkar da murya abun sai wanda yagani, Adaidai lokacin ne dr sageer ya danno kan motar shirun da yaji anki amatsa daga gurin gate yasa shi sakko wa daga motar cikin bacin rai,maganar da zaiyi yaga maryam zaune saurayin ta yana kokarin taba hannun ta sai dr sageer yayi maza ya bude motar cikin zafin rai ya k'ifa mata mari menene haka dan ubanki...

   " Cikin bacin rai tace haba yaya wannan wani irin abu ne??

    " uban wanene wannan 'yar iska wannan samarin banzan kike bi??? Dan ubanki shige gida sannan ya juya k'an saurayin ta cikin zafin rai yace idan nakara ganin ka kofar gidannan sai na ballaka wallahi dan iskan banza da wofi....

   " simsim ya shige motarsa ya gudu...

    " Wallahi mamee watarana sai na karya maryam kina ganin iskancin da tayi amma bazaki hanata ba???

   Mamee ce tajiyo tace banson takura banson shishigi kai uban matan dakake hulda dasu waya sani??? To kafita harkar yarana ko sokakeyi su zama kamar yusra babu mai shinshinasu??

    " Abida ce tace mtseeww mamee kyale wannan yayan bashida waweyyen kai ahaka dan boko sai kauyen ce???

    " Tashi yayi zai daketa ta ruga daki, lallai mamee nagode da kalaman ki kuma kisani uwa na daukeki duk rintse idan naga k'annina sun shiga sun kauce hanya zan musu nasiya in gaya masu gaskiya sannan yafita daga dak'in....

    " tsaki tayi tace too muzuba nidakai muga wanda bai fasaba mara kunya ke kuma ki shige dak'i saura naji kinkara futa...

    " Tana shiga ta k'ifa k'anta ak'an gado tafara kuka...

   " Abida ce tace lafiya maryam ko dai ya dak'i kine??

    " wallahi sister ina bala'in son ya sageer wallhi inasonsa narasa yaushe soyayyarsa ta shige ni sannan ta goge hawayenta tace please karki sanar da mamee...

   " yusra kenan ke dai mutafi...

Tabbijan lallai kina cikin wahala hahaha wannan k'olon gardin kikeso ga alhajin birni nan!

    " banson iskanci abida banson haka ki iya bakin ki nagaya miki...

   " Allah ya baki hakuri son koko daukar rai...

  Bilal ne ya K'alli  mahaifinsa Alhaji isa yace dad wancan baffa ya biyaka kudin ka kuwa??

  Ina ai zuciyarsa ta mutu dubu 20 ake basa kudin gadi ina yaga kudin biyan dubu hamsin??

   " Yasamu kudi ai tunda yakai 'yarsa boarding yakamata gobe ka kunna mada wuta yabiyaka...

    " Angama my son kai dai kanason kaga sun wulakanta kamar yadda mukeso kenan??

    " Kwarai kuwa ko kadan banaso sufimu...

Baffa ke lazumi ak'an dadduma,mama ce tafito tace sannu da hutu maigida...

    " k'allonta yayi yace yauwa uwargida lafiya dai??

    " wallahi kaga nakasa baccin tunanin kada 'yan uwanka su cimaka mutunci akan kudin nan nasu dubu hamsin...

    " To yazanyi? Wallahi banida hanyar samu albashina ma dubu ashirin ne kuma kinsan duk naci bashi banga ta 'inda zanbiya ba...

    " Ya kamata ka kokarta dan Allah wallahi banason naga suna hayagaga...
Chapter 2 · 0% Book details