← Book details Doctor Sageer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 25

Sashe 4

Doctor Sageer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    " Cikin sanyin murya tace Allah sarki ...

    Aisha ce tashigo part din su mamee tare da yasmin dr yana bayansu Assalamu alaikum hajiya mamee menene duniya???

    " Tsaki tayi tace kin bayana kenan uwar magana lafiya dai kikazo ince ba auren naki ne ya mutu ba??

    " Aisha ce cikin siyasa tace ina auren mu zai mutu naku bai mutu ba kuna soyewarku...

    " Ai nayi tunanin auren ne ya mutu ai kizo kukarawa baffan ku wani hawan jinin???

    " Ina ai igiyar aure Allah kadai ke rabata mutum komai shidancin sa bai isaba...

    " Tsaki takaraja ciki da tsanar Aisha da yasmin can tace sageeru Maryam babu lafiya fa?

     " Yasmin ce tace yaya ana magana?

    " Allah yabata lafiya anjima tashirya driver sai ya kaita asubuti ai..

     " To shikenan ina surukar tamu??

    " tananan tana gaidaki...

      yasmin ce tace yaya Aisha tashi mu tafi...

    " Sum sum sum dake uwar munafukai daga zuwanta zakice tatashi ku tafi to takiya...

    " yasmin dai batace kalaba, Aisha tace ohh naga ranar da zaku gani wallahi in banda zumunci mai zai shigo damu??

    " Ai kun tsosa agurin uwarku dole kuyi fitsara...

      " tashi sukayi suka fita suna fita sukaga Alhaji haruna nan Aisha ta gaidasa..

     " dangin tsiya kice kin bayyana bakar kadara haihuwar asara...

    " Ko sauraran sa basuyi ba haka suka huce suka huce part dinsu sannan suka fashi da kuka...

    " Mama ce tace ke aisha daga zuwanki sai kuka??

   " Mama wannan wacce irin rayuwace ta kunci haba mama wannan cin mutuncin ace shi iyayena suke ji...

    " Yasmin ce tace ai kadan kikagani yaya wallahi inkinga yadda suka tozarta baffa jiya sai kinyi kuka kuma wai ace bazamuyi magana ba???

   " Mama itama taji haushin abun amma sai ta dake tace ai sai hakuri watarana zai zama labari ...

   " Aisha ce tace ni ko atatsuniya ban taba ganin irin tsanar nan ba?

    Hakuri dai zakuyi Allah yana sane damu...

Mummy ce tace Allah yanunamin ranar auren nan naki barister yau dai ankawo kudi...

    " Murmushi tayi tace mumy kinga gidan dayakeyi kuwa anjima zai turomin dan haka kisanar da dady asakamin hadaddun kayan daki please...

    " Oh wannan wacce irin Amarya ce lallai zamani...

    " mumy kenan Wayar tace tafara ringing cikin sanyin murya ta dauka darling dafatan kana lafiya?

    " ke zan tambaya dafatan kina lafiya? Tun dazu tunanin ki kawai nakeyi acikin office , Ramlat ina tsananin sonki DanAllah ki kula dani?

    " Har cikin ranta taji tace mijina bakada matsala ba, nima ina kaunarka dr zan iya komai akanka kuma zanyi maka hidima,zuciyata bazan bude wani yashigo ba ko kadan bazan so naga kayi fushi ba...

    " Ramlat banason wannan aikin naki please ki rage saboda ina bukatar kulawar ki...

    " DanAllah Mubar maganar aikina darling..

   " Shiru yayi yace to sai anjima.." cikin juyi ta rungume wayar tare da murmushi, cikin mintuna taja motarta sai office tana iss tace kawata kinsan me??

   Sai kinfada ince dai mutumin zai sakar mana kudi??

   " ke ba wannan ba kinsan yace wai na jiye aiki!!!

    " mtseww bashida hankali ke doluwar inace dazaki ajiye aikin ki ke yana zura kafarsa kema ki zura duniya fa sai da wuta bakiga yadda manyan mata ke shakstawarsu ba???

    " Dadina dake kinaso ayi dani wallahi kam daman yaudarar sa zanyi nace zanbari sai nashiga daga ciki nacigaba...

    " Yauwa ko kefa, barister lawal yana kiranki kije yana office...

     " Tohm ina zuwa kawata bari naje nadawo nadan maganar case dinnan ce.

    " Rabia ce tayi dariya mugunta tace ai sai najawo kinsa  yasake ki da kanki banza tazata sonta nakeyi? Duk duniya na tsaneta yadda kika samu miji bansamu ba kema bazan barki kiji dadi ba.

    " Barister ramlat ce tadawo tace kawata me muke cewa ma?

   " Uhm daman zancen kudine million uku yakamata yabaki nagyaran jiki karki yarda ko million daya yabaki mugune fa dr yana samun kudi sosai....

     " kinaso kiga nafito kawata kinaso kiga ina harka ban mutafa sannan suka tafa.

Yasmin ce ta dawo daga gidansu fatima tun akan titi wani saurayi ke binta amota har tayi sauri tashiga gida, A dai dai lokacin Alhaji haruna yaganshi sannan ya karaso yace lafiya kuwa??

    " har kasa matashin ya durkusa yace ina yini baba? Daman wata yarinya nagani tun dazu shine nazo gurinta yanzu tashiga ciki..

    " fara ko baka lukutar ko siririya??

    " yadan rissina yace yanzu dai ta shiga.

   " To ina zuwa, daman kafin yakarasa yasmin tafito nan tace sannu ina yini? Lafiya dai ko?

    " wallahi lafiya kalou daman inason mudan tattauna ne ina yawan ganin ki wallahi kuma naji kinshiga raina inason kitaimaka kibani dama in shiga sahun samarin danAllah?

   " Shiru tayi batace komai sai ji sukayi Alhaji haruna yana kai yaro wannan yarinyar dakake gani cikakkiyar karuwace bin maza da mata agurinta yadda kasan dabba, dama daya daga cikin yarana kace kanaso da yafi dan sunfita tarbiya...

    " kuka tasaka tace Allah shaida ne kifa mata mari yayi yace zaki yaudari yaron mutane shigiya 'yar iska..

     " matashin saurayin ne yace kaji tsoron Allah katuna tsayuwar ka da Allah sannan ya shiga cikin motarsa ya tafi..

    " Ke kuma bakiga komai ba sai mun saka miki bakin jinin kare...

    " Da kuka tashiga cikin gidan tagayawa mama komai Aisha tace kyalesu yar kanwata Allah shaidar ki ne Ai kuma shi zai cigaba da karemu karki damu da maganarsu.

   Baffa ne yayi sallama Aisha tayi masa sannu da zuwa nan suka gaisa yace auta wayatabaki? " Dariyar karya tayi tace babu kowa baba.." To kinji ankafe sunanki amasu zana jarabawa ran monday zaku fara sai ki shirya. " cikin mamaki tace baffa wa yabiyamin? " sageeru ne sai kiyi masa godiya. " inshaa Allahu. " Mama tace aikuwa angode.

   " Aisha ce tace kasan ina koyarwa baffa kuma ina daukar kudi masu yawa gakuma business da nakeyi wallahi baffa bana taba komai acikin kudin sai dai ko idan zanyi taimako Allah yabani miji nagare komai shi yakeyi min bana siyar komai kuma nasan gar da adduar da kukeyi min duk da bana kusa daku domin ku iyaye nagari masu koyar da hakuri da yadda da kaddara.. " yasmin ce tace hakane yaya Aisha. " wannan jakar million 4 ce aciki da dubu dari 3 duk kudin aiki na da sana'a tace nakusan shekara 10 danake tarawa wannan gaba daya nabar maka baffa kaja jari domin tarbiyar da kake bani wallahi banda abunda zangode maka duk da bana kusa dakai komai kanwata tasa sai ka turamin duk da munyi nisa kuma mahaifiyata batasaniba, hatta kudin makarantar da kabiyawa yasmin naga kasiyamin atampa duk dan karka fifita wani acikin mu, kaja jari baffa ina fatan wanna kudin yazama dukiyar da Al'umma zasu amfana da'ita ..

    " yasmin ce tasaka kuka ta rungume aisha tare da fadin tabbas nayi wani sabon karatun Anan idan kanason d'anka yatashi cikin tafarkin gaskiya to kasanar dashi ilimin addini kakuma zama babban misali nagurin koyar tarbiya,kar kuma kanuna masu bambanci , abunda zamuci miki shine Allah yayimiki Albarka yaya inasonki wallahi...

    " Mama ce tasaka kuka tace tabbas mai hakuri shikeda riba, ako da yaushe baffa kana fadan Allah yana sani damu kuma zai dubimu yau gashi ranar tazo ranar da mai hakuri zai ci riba, Allah yayi muku albarka aisha Allah yasaka muku da Alheri halinki nagari yasa 'yar uwarki tagado halinki...

    " Baffa ma yayi musu addua tare da godiya sannan yace yadda kikace naja jari zan koma sana'ar mahaifina wato atampofi tunda tun ina karami na iya sana'ar daman ba lallai kayi ilimi kakuma samu sanaar da kake tunani ba wane sain sai kaga alkhairin ka yana inda baka tunani especially idan kana addua ...

   " Tabbas hakane..

Yau Aka kai lefen dr sageeru akwati goma sha biyu kaya masu kyau, wani satin za'a fara biki yasmin kuwa ta hada kayanta zata koma boarding tun karfe 8 baffa yasa aka kaita gida ya cika da hidimomi kalakala..

    " Da daddare dr sageer yaje gurin ramlat taci kwalliya bakace ita bace ba daman irin siraran matannan ne ga ido amma batada hanci sosai kuma ita chocolate colour ce sai dai iyayi acikin ta kamar me tana zuwa tace ya muradin zuciyata..  " Cikin kayataccen murmushin sa wanda ya bayyana hushiryar sa da hakorin makka yace Amincin Allah ya tabbata agareki ya ruhin zuciyata amaryata kuma muradi
na...

    " yauwa mummy tace in gayamaka kayafa sunyi sai sai Allah yabiyaka kuma gobe zasuje jiran kayan dak'i ..

    " Dariys yayi yace tohm shikenan na riga nacika saman ku kwacika kasan kitchen dinki katoto kinsanni da son abinci...

    " Haha lallai kam..

   To ni inada aiki yanzu sai zuw gobe in Allah yakaimu..

   " kagaida gida sannan tashiga cikin gida..

Baffa ya bar aikinsa yasamu babban shago ya zuba kaya aciki, da magriba yana dawowa yayi sallah, Dr sageer yana shigowa yace baffa naga yanzu kana yin yamma??

    " Eh da yake yanzu nakoma shago nazuba kaya.. " shago baffa? Ina kasamu kudi?? " Wanda ya yarda da Allah ai shi zaisha kallo, ga dubu dari tukwuicin bikin ka Allah yasaka albarka a auren ku kuma kaji tsoron Allah kariketa dakyau..

    " To baffa nagode Allah yakara budi sannan yatafi, " mama tace gaskiya nayi dacen miji wallhi mai boye sirrin gidan sa akwai da babu..

   " Murmushi yayi baice mata komai ba...

    Yau jumma'a yau aka fara biki sunyi kamu da dinner sai dauren aure abun ba a magana sai wanda yaje biki dai yayi kyau sosai kuma manyan mutane sun halacci bikin su abida da maryam da bilal basu haukace ba sai da sukaga gida kowa baisan yana ginin ba kallon kolo sukeyiwa dr sageer nan suka dawo gida suma zagin. " mumy da dady sunyiwa ramlat fada abisa gaskiya da amana sannan aka tafi da ita hajiya suwaiba itama tayi mata sannan akayi gidanta..
Chapter 4 · 0% Book details