← Book details Doctor Sageer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 25

Sashe 8

Doctor Sageer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    " Murmushi tayi tace sageeru kenan yaushe kasamu lafiyar ma? Kabar zancen nan sai an kwana biyu..

   " Tohm na amince amma ke nakeso kisamo min yarinya mai tarbiya mai ilimin addini DanAllah kinji??

    " To Ni yaya zanyi sageeru dama hajiya kagayawa tafini hulda da mutane ai...

    " Ai duk maccen dake jure akwai da babu itace mace..

    " sageeru kenan yanzu sai zuwa kwana biyu sai a sallameka kenan??

    " Ai na warke anjima karfe 4 akwai wacce zanyiwa cs...

     " Haba sageeru yaushe ka warke din ka hadata da wani likitan sai ya yimata....

     " Mama banga amfanin aikina ba idan bana taimakon talakawa domin wannan matar danake gayamiki satinta daya a asubuti batasan wake kanta ba sai shekaran ko abincin da zataci batada shi ko kudin ganin likita tana cikin halin taimako sosai...

     " Tohm shikenan sageeru Allah yakara budi da takawa da imani ...

     " Ameen mama....

Yasmin ce ke zaune tanacin abinci sai kuwa hajiya cewa tayi kinga har an sallamesu har ya huce asubutin sa...

     " kai amma anya ya warke kuwa??

     " ina wata warkewa? Kawai dai kinsan mutum ne mai taimako...

     " Allah sarki Allah to yakara lafiya..

    " Ameen ... Nikuwa yasmin har yanzu babu tsayayye??

      " Murmushi tayi zuciyarta cike da kunci tace Allah bai tsayar ba,Amma munata addu'a..

   "Hajiya tace ai dama abun na Allah ...Allah yabada nagari ..ameen tace sannan tatashi tayi cikin dakinta da wayarta ke faman ringing...

    " Hello yasmin ykke yusra ce .....

   " Banza sai yau kikaga damar kulani to kinkyauta.....

    " wayata aka sacemin shiyasa ankawo kudina ansa wata 5 fa..

     Haba danAllah congrat Allah yasa damu za'ayi...

   " Ameen yasmin DanAllah ki amince da dr sageer ba lallai sai mara mata ba kowa fa da zabinsa da Allah yayi masa ke dai kiyita Addua Allah ya tabbatar muku da Alherinsa...

     " bazaki gani ba yusra bafa wani sona yakeyi ba kawai yaudarata yakeyi...

   " kada ki yanke wannan hukuncin kibashi dama yasmin...kuma kisani wayake auren soyayya yanzu? Malama anayin aureni dan kauna in akwai kauna ai babu wulakanci da tozarci kuma dan a rufawa juna asiri ne, dukiya ba itace aure mai wadatar zuci mai tsoron Allah wanda zai kula dake wannan shine mai sonki...

    " Yasmin ce tace tabbas hakane dan bazan manta maganan malamin mu ba da yace idan kuntashi adduar miji kuce in talakane Allah yabaku mai addini mai kuma sanaa in kuma mai kudine Allah yabaku mai addini mai kuma aiki dashi...

Hakane kawata nagode sai kinjini, sannan suka kashe wayar...

   Dr sageer dake zaune akan kujerar sa yana cin abinci wayarsa ce tafara ringing salama yayi sannan yace wake magana...

     " yasmin cikin rashin kulawa tace nice dama mama tace mekakeso adafa maka??

     " cikin murmushi kamar tana kallon sa yace duk abunda kika dafa ai zanci...

    " yajin naka?

" Naji sauki ai.." Allah yakara lafiya..

    " Ameen nagode my queen Allah ya mallaka min ke a matsayin matata yadda nake sonki Allah kadai zai shaida...

    " Batare da tace komai ba ta kashe wayar cike da murmushi tana fadin kai kasani...

    Hajiya suwaiba ce tashiga cikin part din su mamee ko sallama batayi ba tace tabbas kun nunamin ku makiya nane kunsaka hassada da bakin ciki acikin ranku tayaya zakuyi gaba to sageeru dai bai mutu ba, haruna kuma sharrin ka kai da isa akanku sai kare marasa mutunci kawai...

    " Dukkan su babu wanda yayi magana dan  suna shayenta sosai da sosai...

   Abida dake faman kuka tana kaci amanata garba baka kula dani baka sona har yaushe mukai auren zakaci kishiya hatta kusa dabi baka zuwa ...

    " Garba ne yace ai ko jaki yanason kulawa da hutu ballantana ne mutum, menene bana yimiki acikin gidan nan menene bana baki tundaga kan ruwa har reza?  Bakya tsafta kwata kwata dubi dakinki sai kace na mahaukaciya naga har tsintsiya sai na siyo?? Bakya kitso akan kari bakya dan kunshin nan da mata sukeyi ke harma irin style dinkinnan bakyayi wanda zan kalleki naji sha'awar ki komai ina baki har kudi kaya abinci komai akwai ayimin naji dadi ne baza'ayi ba ba? Dan haka aure babu fashi, karatun Alkur'ani tunda muke agidannan banga kinayi ba to uban me kikeso nayi miki??

    " Kuka tasaka tace inshaa Allahu zangyara har sallah ma zantsayar inshaa Allahu kayi hakuri sannan ta durkasa...

    " bakomai abida ni ina kaunarki shiyasa natsaya ina gayamiki gaskiya...

   " zangyara inshaa Allahu mijina...

    Ramlat ce ta fito daga wanka tana amsa waya nan dr sageer ya shigo jakarsa kawai ya ajiye sannan ya rungumeta my brstr kullum kyau kiketa karati sannan ya sumbaci bakinta...

    " shiru tayi sannan tace wane irin so kakeyimin dr?

   " kara rungumeta yayi sannan yace wanda bazai fadu ba...

    " Nan tafara sakashi fita hayyacin sa tabbas mijinta daya tamkar dubu ne samun mai hakuri irinsa sai an tona...

   " Nan suka shiga wata duniyar cike da soyayya da farantawa juna...

   Da safe baffa ya shirya zai tafi kasuwa sai yasmin tace baffa kudin wayar anjima zanje nasiyo...

    " Auta kenan gwara da kika tunamin sai kisiya biyu ke da maryam ko??

   " Hajiya suwaiba ce tace wannan marasa mutuncin kaima dai narasa irin ka dakake jin tausayin su Alhalin su basuji naka ba...

    " baffa ne yace haba babbar yaya ai komai rubewar hannu baka yanke ka yarba...

    " Sallamar dr sageer ce ta katsesu nan suka gaggaisa sannan ya zauna yasmin dake barandar tsakar gida tana gyara wasu abubuwan ta ...

   " mama ina yasmin ta shiga ne ko tana makaranta?..." aa tana can baranda kaje ku gaisa mana...

    " Ita dai hajiya suwaiba takasa cewa komai sai adduar Allah yasa ta amince...

     Amincin Allah ya tabbata ga sarauniyar sarakai hasken zuciyata...

    " Dagowa tayi ta kalleshi nan idonsa yakara rikita ta ta, can tace katashi lafiya...

    " lafiya kalou ina mamakin kin yarda dakikayi da maganata yasmin kuma ke kanki kinsan bazan yaudareki ba...

    " Shiru tayi sannan tace idan ma ka yaudare ni ai kaikaga zaka iya domin shi alhaki kwuikuyo ne ai...

   " yasmin kalli cikin idona magiya nake ki kauna ce ne danAllah!!! Banda ke bazan yabi kowacce 'ya ba kinsani..  tabbas tun kina karama nasa kaki acikin zuciyata.. kinsan zafin soyayya tunda kinyi kuma kinsan wahalar ta..yasmin dita mai kyan hali ga kuma kyan halitta kwayar idonk'i yana riketar dani har na k'asa dauk'e idanuwa na akanta......

    Shiru tayi sannan tace danAllah doctor ka rufamin Asiri ka hakura da soyayyar mu...please sannan ta goge hawayenta...

     " Tabbas yasmin idan kika yimin haka baki kyauta ba kuma zaki sakani halin da yafi nada...DanAllah ki taimaka min sannan ya zauna ...yau zakiji labari na

   Sunana sageer...

Assalamu alaikum

    Naga Sak'onin ku nagode Allah yasakada alheri...kuyi hakuri da shiru na da kukeji..lurv u oll

   _I can't stop apologized for the  spelling and grammar mistake's_

     *How was the page???*

    _Please do vote comments and like my story really need your comments and vote#TEAM....DS

*Urs Nana diso*

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:[email protected]

Gmail:[email protected] 

Wattpad:NEIRNAHDISO

[11/6, 8:24 AM] ‪+234 703 475 7034‬: 30-35

*_DOCTOR_*
        _*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  Yanayin da momy ta tarar dashi ko motsi bayayi nan takira mai gadi ya taimaka mata suka nufi asubuti directly emergency sukayi nan akayi dak'in dashi sannan babban amininsa wato dr khalifa yashiga domin ya dubasa...

    Mumy dake faman sintiri da salati abunda yafi tsaya mata ina ramlat tashiga?? Aikin tatafi mijinta na wannan halin?? Cikin kankanin lokaci takira dady nan yakaraso yanata salati da fadin sai ya sabawa ramlat...

     " mumy ce ta kalli Dady idonta cike da hawaye tace to yanzu yaya zamu sanar da mahaifansa??

     " Tun ahanya nakirawo baffa dan shine mai sauki kuma sai yafi fahimtar abun cikin sauki....

    Baffa dake faman sauri mama tace ina zakaji ne??

    Au namanta bangaya miki ba sageeru ne babu lafiya rai ahannun Allah suna can asubuti...

     " Innalilahi kuma yasmin tacemin jikin da dan sauki kaga yanzu yayi tsanani to innakarasa aiki matawo ko??

     " tohm bari nasanar da alhaji haruna da isa ko??

      " Toh a sanar dasu kuwa kasan dai halinsu dama dai ka kyalesu ko??

    " Ai shi zama da mutum sai kayi hakuri ballantana hakkin maqotak'a...

    Yana fitowa daga part dinsa yatarar dasu harda su maryam bilal da mamee zasu fita babu wanda ya k'alli shi sannan ya dubesu yace sageeru babu lafiya ankwantar dashi asubuti...

     " Alhaji haruna ne yace wannan matsalarka ce, Alhaji isa kuma yace ai da mutuwa yayi kaga sai muci gado ko??

    " mamee data tamutse fuska tace ku dayake wahaltawa ai sai kuje kuyi jinyarsa sannan suka fita...

    " Dai dai lokacin da zai shiga mota hajiya suwaiba tashigo nan yace mata tatawo suje asubuti, Akan hanyarsu tatafiya tace kaddai ciwon sageeru ne ya tashi???

    " Eh hajiya shine abundai sai addua... " D'ana bai samu macen kwarai ba ina tabbatar ita zata karasa shi...

     " Baffa ne yace hajiya kamar yaya?? " Nan ta kwashi labarin duk abunda ramlat take masa ayadda aka bata labari...

      " kidaina kuka Allah yana sani dashi kuma za'a daidaita su inshaa Allahu...

      " kallon baffa datayi tace babu yarinyar dakake ganin za'a hadasu??

     " Shiru yayi yace kina nufin yakara aure wai?? Haba hajiya abu abun asannu tukunna...

     Suna karasawa asubutin sukayi gurinsu nam suka gaisa dasu mumy sannan likita yafito yace ina mahaifansa??

   " Gamu cewar baffa daga nan suka bisa office shi da hajiya kallonsu yayi yace kunsan yanada ciwon zuciya ko??

     " Kwarai kuwa cewar hajiya... " To yanzu dai jikin nasa Alhamdulilahi zai farka nan da 10hours inshaa Allah amma inasu ku lura kukuma kula sosai akwai matsala atare dashi...

      " Kamar ta tunani saka abu arai da damuwa gakuma yunwa har ulcer takamashi yana da kyau alura da lafiyarsa..

      " Inshaa Allahu za'ayi...

Brstr ramlat da ita da rabi suke hira nan ramlat tace kawata cikine fa dani???

    " Wani bakin ciki ne ya tokari mata wuya wato har ramlat tasamu jindadi da mijinta tabbas tasan abunda zatayi...

     " Dake fa nake magana brstr rabia??
Chapter 8 · 0% Book details