← Book details Diyar Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 14

Sashe 8

Diyar Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allura ya hada ya ba Bahijja tare da zama kan kujera ya nuna ma SHEKH inda zai zauna, bayan ya zauna ya zubamai ido.

Kasa da kai Hammad yayi yana jin mamakin yanda yake shakka mutumin.

SHEKH yace" ina jinka.

Hammad yace na fahimci tana da Asma, kuma bayan haka ruwa yamata duka, kana kamar jininta ya hau sakamakon furgita da tayi ,amma Alhamdulillah Allah ya kiyaye gaba, yanzu zata kwana biyu kamin a sallame ta.

SHEKH yace "tabbas tana da ita , sai dai Abinda ya bani mamaki to mene ya fiddo da ita daga Islamiya har ruwa ya mata duka ?.

Cikin fushi nasu na Fulani ya zaro wayar shi ya kira Ya Sayyadi.

Yana É—agawa ya mai sallama bayan ya amsa yace" Taya akabari Zarah ta fito cikin ruwa? gashi ya mata duka har ya kwantar da ita? Gaskiya Ya Sayyadi zan iya hanata wannan TP É—in, Saboda nafi bukatar lafiyar ta akan matsalar ta.

Salati ya Sayyadi ya É—auka yace" Wallahi SHEKH bamayine in ana ruwan safe, kuma ban'fito da waya ba .
Nan ya fad'amai yanda akai.

Ajiyar zuciya ya sauke yace" Shikenan! ya kashe wayar.

Sosai ya burge Hammad yanda yake son yarsa.

Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Hammad dake kallonshi yace" Allah ya kyauta gaba bani takaddun maganin da kuma bill É—in abinda zanbiya.

Bakin Hammad ya É—auki rawa yace" am ka barshi kawaiii,kuma dan Allah kayi hakuri,kamun magana akan in daina amma.

Murmushi Sheikh ya saki ya au kason lefin ka kenan ko?

Hammad ya daga kai yace hakane amma na daina.

SHEKH yace tom bara kaji bana shiri da wanda bayaji,ashe kana da aikin yi amma kuma kake son yiwa rayuwarka illa,kai likitan ne kason mene sigari kejawowa hakane?,to amma miyasa bazaka daina sha ba har sai wani ya faÉ—ama.

Kai a'ƙasa Hammad yace" na:maka Alkawari Abba bazan sake ba insha Allah, na bayama kuskurene Allah ya gafartamun... .....

Cikin jin daÉ—i SHEKH ya dafa kanshi yace "Allah ya amince yama rayuwarka albarka .
ya sunan ka.?

Murmushi ya saki cikin tsannin jindaÉ—i yace" Muhammad,Amma ana cemun Hammad.

Kai SHEKH ya jinjina yace" gaka da suna mai daraja , Allah yabaka ikon koyi da maisunan Muhammad.

Hammad yace" Ameen Abbah, nagode am nace yarkane?

Kai SHEKH ya É—agamai yace "yatace kwalli daya mace, tan@ da yayu maza biyu..

Hammad ya jinjina kai yana murmushi yace kana sonta sosai.

SHEKH ya gyara Zama yace" Muhammad
Dole inso Zarah,saboda tana sona,tanada biyayya sosai,bantaba cewa tayiba tace batayi,bantaɓa ba Zarah fari ba tace baki takeso,ga baiwar ilimi da Allah yamata,shiyasa nike son ta, nike jinta fiye da sauran Yayunta,ga tausayi tana bani, saboda lalurinta,ina alfahari da yarinyata, kuma bana iya ɓoye sonta a duk kan inda nike..

Sosai yake jinjina kai cikin gamsuwa da maganar dattijon yace" Allah yasa Nima Daddy yamun irin wannan son.

Murmushi SHEKH yayi yace" zai ma fiye da haka muddum ka kasance mai biyayya ga umarnin sa. Ko zan iya ganin ta?.

Kai ya jinjina mai yana zuba tagumi.

Mikewa SHEKH yayi yamai godiya sosai kana ya fita office din. Hammad ya bishi da kallo.

Kai tsaye É—akin da Zarah take ya nufa ya isketa kwance tana bacci cikin natsuwa, su Abdallah na zagaye da ita.

Shekh ya daÉ—e tsaye akanta yana mata Addu'a kana suka fita shida Sudais.

Hammad kau kanshi yaci gaba da hautsinawa yana tinanin wato yaro mai natsuwa an'sonsa fiye da maisa iyayen sa magana, ya yarda da maganar SHEKH.
Saboda tsakanin shi da Ahmad kadai hakan ya isa ya zamemai darasi, saboda Daddy yafison Ahmad fiye da shi,to miyasa Dan uzurinsa ya zaɓi zama taƙadari a idon duniya,anya bazai canza wannan tsarin daya dora kanshi akaiba,lokaci guda yaji ZARAH ta burgeshi kuma ya samu natsuwa da ita da kalaman mahaifinta,ya tabbata jininta da ya hau saboda shine ,ta ganta kwance akan sa.
kanshi ya shafa ya saki murmushi yace akwai irin su kuwa yanzu? Wayar shi tafara ring yana ganin Affan ne yayi tsaki yakashe wayar baki daya tare da kife kanshi akan table din ya fara tinanin abinda ya faru yana sakin murmushi....
Bayan mangariba yana fitowa sallah kai tsaye dakin da take ya nufa. yana da tabbacin ta isa tashi , dan Lokacin da Allura zata gama aiki jikinta ya ƙare.

Yana shiga ya isketa zaune tayi tagumi tana hawaye ita kaÉ—ai É—akin.

Kamar ya juya kuma ya daure yayi sallama .

Da sauri ta sake gyara zaman hijjob inta batare da ta ɗago kai ba ta amsa murya ƙasa -ƙasa.

Nesa da ita kaÉ—an yayi tsaye yana kallonta yanda idonta ke tsiyayar da hawaye...

Ahankali yace" ya jikin,da fatan ba wata damuwa.?

Da sauri ta juyo ta kalleshi karaf idonta ya fada cikin nashi, shima ita yake kallo.
Da sauri ta janye idonta daga gareshi ta saki kuka sosai tace "mikazoyi,zaka karane,wanda kayi bai isheka ba....

Ahankli ya kara so inda take yasa kujera nesa da ita kaÉ—an ya zauna.

Gyaran murya yayi yace" ZARAHHH ya fada cikin wani masifaffan sauti dake furta harafin sunanta dalla -dallah.

Wani irin faduwa gabanta yayi batason sadda ta kalleshi ba akaro na farko takeɓe daga ita sai namiji har take binshi da kallo..

Kallo daya yamata ya mayar da kanshi gefe dan bazai iya jurewa ba.

Yace Zarah ni ba ɗan iska bane kamar yanda kike tinani, wallahi bantaɓa rike hannu mace da sunan iskanci ba,sai dai da niyyar taimako kamar yanda namiki,shima dan ina likita,amma banson mene yasa akaro na farko da haduwar mu ba kikemun wannan mummunan kallon,bazan rantse miki abanza ba saboda ba bashin rantsuwar kike bina ba,amma wallahi billahi bantaɓaki da sunan jin dadi ba,hasalima a idona kika faɗa kwalbati kinga ko isa inda kike banba,saboda nason inda kina da hankali zaki iya fito da kanki,to amma danaga kinfito numfashinki ya dauke kuma zaki iya rasa ranki yasa nakira sst na, ita kuma ta razana da ganin ki ,naga tana neman sakinki kuma kanki zai iya buguwa, Ahalin da kikeciki zaki iya shiga babba matsala a kwalwarki,mafarin na tareki kenan,in kuma baki yardaba Zarah zaki barni da Allah shiyason zuciyana,Kuma shizai miki sakayya kinji yakarasa cikin sanyin da baison na mene ba....

Sosai jikinta yayi sanyi A'hankali ta fara furta Astagfirullah!!!..

Kanshi ya É—ago suka hada ido zarah ta kasa janye nata, lokaci daya hawaye ya sakkomata tace" ka yafeni na munatama zato ko ,dan Allah kamun affuwa rashin sani ne ka yafen?

Kai ya jin'jinamata yana Murmushi yace "nima kinyafemun.

Murmushi tayi tana dagamai kai.

yace nagode da fahimta.

Kai ta jinjinamai tana kyafkyafta ido alamar son magana.

Yace uhm kamar akwai abinda zaki faÉ—a ko,kiyi maganarki kai tsaye,ko baki yafen ba.?

"Kai tadaga alamar eh."

Ido ya zaro cikin mamaki yana binta da kallo yace" kuma?.

Cikin shagwaɓar data saba take dan turomai baki tace "gaskiya Ni.

Baison sadda ya shagala da kallont aba fatanshi kawai taci gaba.

Kallonshi tayi suka hada ido ya ÆŠagamata gira tare da cewa minai miki?.

Manyan idanuwanta ta waro mai tace gaskiya bazan yafeba har sai kadaina shan sigari, sahoda babu kyau, hakama babu kyau ga lafiyanka ,gaka kuma Doctor , Nason kason da haka, ko? ta karasa cikin sigar tausayi.....

Akaro na garko da yaji mace ta burge rayuwar shi bayan mahaifiyar shi. Lallai yarinya ta samu tarbbiyya ,dole mahaifinta ya sota dan ko kalamansu iri dayane kamar sun tsara kafin su faÉ—a...

Tace" bakace komaiba Hamman Yusrah...

Murmushi yayi Yace" ashe kinson ta ,amma bakya sonta,kina bata wahala dan kinga tana maganarki koda yaushe,kinajamata aji dan kinga kinkai ayi tarayya dake saboda kina da kyakyawar Alaƙa ko?
Insha Allah na miki alkawari na daina nida su famfamfam!!! ya faÉ—a yana turo maroom lips É—inshi abun ya masifar mai kyau kamar yanda hakan yayi tasiri ga zuciyar Zarah..

Mikewa yayi tsaye yace fatan lfy agareki Insha Allah.
yana faÉ—in haka ya ficce.

Da kallo tabi bayan shi tana lumshe ido ga wani yanayi na farinciki da taji yana shigar ta.

Baijima da fitaba su SHEKH suka shigo suka ganta ido lumshe.

Da sauri ya karaso wajenta yace" Bintu Abiha ina fatan lafiya.

Tace" Abu Zarah na warke sumul.

Yace Masha Allah ya karamiki lafiya kinji.

Tace Ameen anan umma tamata Sannu tana shirya kayan da qtazo dasu tinda an tabbatar musu da kwanan Asibiti zasuyi.

Bayan kwana biyu sosai shakuwa ta shiga tsakanin zarah da Hammad, wadda su kansu tana basu mamaki, amma basu taba bada fuskar da iyayen su zasu saniba. ZARAH abin har damunta yake, gashi ta kasa faɗama mahaifinta akaro na farko arayuwa datafaramai ɓoyen wani abu daya shafi rayuwarta Saboda tana tsoro tason kullum kashedin sa gareta kartaba namiji damar ganin fuskar ta..

Bayan mangari ba Hammad ya shigo É—akin fuskar shi babu walwala yayi sallama, yana kallon zarah dake zaune cikin ash din hijjob tayi kyau sosai fuskar ta tayi fayau alamar tasha jiki.

Gaisheshi tayi ya amsa yana cewa" ina Ummah?

Tace" ta É—an fita ina son lemun zaki ne..

Kai ya jinjina yace ''zarah kamar kar in sallameki, Amma SHEKH ya matsa yanaso kitafi kibarni ko.

Gabanta ita kanta saida yafadi amma saitayi kasa da kai tace ''to Masha Allah..

Karasowa wajenta yayi ya mikamata farar takarda dake hannu sa.

Ta dago zata karba yakuma mayar da hannuwan sa baya ya ɓoye.

Cikin mamaki take kallonshi.!

Idon shi duk sun kankance yace" Zarah kina farinciki ko,zaki rabu da aljaninin ki ko,bayan na karu da zama dake sosai kuma zaki tafi.

Murmushi tayi batace komi ba.

Yace zarah dan Allah kirike waya sai muna gaisawa kinamun karatu kinji ,Kuma inajin lafiyan ki kinji ƙanwata.?.

Ido ta zaro tace ka shiga makaranta man, SHEKH bazai barni in rike waya ba Har sai nayi Aure...

Jikin shi ya dauki rawa murya na karkarwa Yace" A'a nafi fahimtar naki ne,Kuma Zarah kina nufin aure zakiyi da kananun shekarunki yafada yana zubamata jajayen idanuwan shi?.

Murmushi ta sake saki tace hmmm .

Takarda ya miƙamata ta karba ta kalleshi idonta cike da hawaye tace nagode Allah yasaka da Alkhairi, Abbah yace kyauta kamuna komi Allah yama sakahayya da mafificiyar aljannah.

Kai ya daga tare da fadin Ameen ya juya ya fara tafiya babu lakka ajikin sa...

Har yakai kofa tace" am bakaji ba.
Chapter 8 · 0% Book details