← Book details Diyar Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 14

Sashe 14

Diyar Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kai ka fahimci haka.
amma ka kasa sanar mun saida lokaci ya wuce,bayan ko jiya muna da lokaci zan kai maganar ka wa Abbah na,to yanzu bani da abinda zance sai dai ince muyi hakuri .

Afusace yace "bazanyi hakurin ba ZARAHHH, wallahi bazanbarwa kowa keba, saboda danni aka halicceki, zanga É—an yarinya da zai kara danu. wallahi zandawo Hammad dina na asali zarah bazan iya hakuri dake ba ,bazan iya ba, ya fada yana bude motar da karfi yafara tafiya batare da yason inda yake jefa kafar shi ba.

Da sauri ta fito itama tayi tsaye tana kuka tana kallon yanda yake tafiya da masifar sauri.

Da gudu- gudu ta fara bin shi tana kiran shi amma som yaki tsayawa ,tafiya yake har suka doso wata kwana inda wata babbar mota ta doso
inda yake gadan- gadan.

Ihu ZARAHHH ta Kwallah tare da sanya wani masifaffan gudu tacim mashi ta fada kanshi da masifar karfi ta tura shi da karfi.

A'tare suka fada cikin wani rami inda ta haye bisa kirjinshi tana sauke numfashi.

Kallon ta yake sosai ko kyaftawa bayayi.

Ido ta zaro da karfi tare da saurin tureshi ta mike tsaye tace mike damunka ,kanso kamun asara rankane ,yanzu in wannan motar tabi takanka fa zkana tinanin zanrayu cikin aminci? babufa abinda yafi karfin Addu'a Hammad, Dan Allah muyi Addu'a ,ka sani Inma da gan-gan zaka kashe kanka to mizakace da ubangijinka , baidace ba som, bai kamata ba ,kai Musulmine ka son kaddara mai kyau da akasin haka.

Ido ya lumshe yanajin wani yanayi mai wahala fassarawa tare da kudirin komi zaifaru saidai yafaru babu shegen da zai aurar mai ZARAHHH yanaji yana gani ..

Zarah ta ƙaraso wajen shi tace" Dan Allah ka tashi ka tafi gida ka huta.

Yace inaso muyi magana dake kibani number wayar da zan sameki.

Tace bani da ita gobe munhaÉ—u.

Kai kawai ya dagamata yana lumshe ido.

Napep ta tare ta shiga kana ya leko tace dan Allah katashi ka tafi.

Kai ya sake dagamata daga kwancen da yake yana dagamata hannu harta suka tafi kana ya mike yana kallon kanshi yace akanki na farajin haka kuma Insha Allah akanki zan sauke samartaka na my ZARAHHH...

Bayan sati biyu.

Wata sassanyar shakuwa mai cike da so da kauna sukeyi ,kullum ZARAH ta tashi makaranta zasu tsaya susha soyayyar su dan tini sunfara mantawa da wani auran da zatayi

Aranar laraba da tagama T.P aranar kamar yayi hauka saboda baison ya zayyi ba wajen son sake kasancewa da ita ,gashi yayi -yayi ta karbi waya takiya.
Sai dai ta gayyace shi walimar da zasuyi a babbar harabar makaranta ranar Friday.

Haka kam akai ranar Friday gidan su Zarah ya cika da mutane yan makwabtansu suka fara shirya kayayyaki .
Gaskiya Abbah yayi kokari dan rago biyu ya yanka da kaji masu yawa dan duk ayi walima zarah.

Zarah kam na daki tana tinanin rabin ranta, tare da fadin bazan iya rabuwa da kai ba,na saba da kai ,ina sonka sosai my Hammad...

Karfe huÉ—u zarah ta gama shirinta cikin wata maroum din abaya mai masifar kyau sai sheki take inda ta samu Hijjob milk har kasa ta sanya baka ganin komi sai kwayar idonta.

Kanta ta kalla a madubi ta saki murmushi tace" Mrs Hammad Ali bature insha Allah...

Shekh ne ya shigo da fara'a yace "Zarah muje lokaci yayi.

Fita tayi inda ta iske yan'gidansu gabaki É—aya sunsihha mota .
Da hanzari ta bude ta shiga suka dauki hanya.

Suna zuwa bakin harabar makaranta gabanta ya buga, taita waige- waige amma bataga sanyin idaniyar nata ba kuma tana da tabbacin yana kusa.

Parking sukayi inda sukaga manya- manyan motoci daga farkon layin har kusan karshe.

Shiga sukayi inda zarah keta lafewa bayan SHEKH tana kalle- kalle.

Hannuta ya kama suka shiga harabar babba makaranta dake cike da mutane manyan- manyan alhazawa.

A'hankali Zarah tace anya zan iya Abbah.

Yace insha Allah .

Agulguje suka shiga tare da samun wuri suka zauna .
akai-akai take juyawa amma bataga Hammad, ba bayan ya shedamata zaizo.

Ya sayyadi ne ya fito yace" masha Allah Alhamdulillah wada muke jira tazo wata FATIMA BINTU ZARAH ÆŠIYAR SHEKH DEEDAT.

Dan haka zamu fara dake Zarah kifito...

Magana Abbah ya mata akunne cikin natsuwa ta mike tana matse hannayenta....

Ahnakli ta karasa wajen da aka tanafa dan masu gabatar wa.

Cikin natsuwa ya Sayyadi ya buÉ—e taro da Addu'a kana ya mata magana ta É—agamai kai kawai batare da taga Dubban mutanan dake wajen ba.

Rawa jikinta ya dauka lokaci daya ta limshe ido tare da murza speaker hannu ta ta fara Bissimillah.

Wow masha Allah zanso kuga yanda Atenshion din manya-manya alhazawa ya dawo kan ZARAH.

Shi kanshi ya Sayyadi saida ya lumshe ido tare da cewa masha Allah.

Baki ta bude ta fara karatu cikin suratul Nisa'i tanayin nida ta fara share hawayen dake zubomata da tafin hannuta.

Lokaci daya kuma ta cire glass din idonta ta ajiye gefe ido lumshe taci gaba hawaye sunmata jagab.

A'hankali ta farajin sanyi na ratsa illahirin sassan jikinta gaba da baya.

Ido ta bude tare da dan É—agowa ta zubama mutanan dake zaune ido wasun suma kuka suke ganin tana kuka .
karaf idonta ya sauka ga Hammad daketamata Vidio da wayar shi.

Suna hada ido yadagamata kai da hannushi alamun taci gaba.

Ido ta lumshe taci gaba da kwararo karatu har saida tazo inda take so kana ta dasa aya.

Tafi wajen ya É—auka da kabbara.

Ahaka akaita fiddo wayanda za'a yaye bayan an kammala aka duba marking su nan akaga zarah tafisu nesa ba kusaba.

Anan fa manyan alhazawa suka fara fiddo manya manyan kyaututuka na kudi mota kayan sawa ana bata...

Ya sayyafi yace to masha Allah kowa zai iya komawa wajenshi mungode da wannan dumbin Alkhairi...

Kat kat kat !!! suka farajin takun takalma da wani masifaffan turare mai tsananin kamshi.
Gabaki dayansu suka juya Zarah kam ido ta lumshe.

Hammad ne yasha fararan kaya na wani dakeken boyel fari tas sai bakaken takalma da hula sai wani shegen glass dayasa ya toshe idon shi hannushi rike da furanni masu masifar kyau.

Ya sayyadi ya bashi hannu suka gaisa.

Ahankali ya karɓi speaker hannushi yayi sallama tare da faɗin alhamdulillah naji dadi matuka, ina cikin tsananin farin ciki da wannan rana mai albarka.

Cikin tako na kasaita ya karasa gaban zarah tare da fiddo wani farin hankacif ya mikamata.....

Kutt yazata kaya ga zarah ga shekh ga hammad cikin taro.

SHEKH ya hanata mu'amullah da kowa yaushe ta fara baisani ba.

Baba yaba SHEKH wata daya anci sati biyu saura nawa?

Ya alkawarin hamnad na mallakar zarah shin zai hakura koko yola zai bita.
Chapter 14 · 0% Book details